Sheikh Murtala Asada Ya Yi Zazzafan Martani ga Malami kan Sulhu da Turji, Ya Bugi Ƙirji
- Malam Murtala Asada ya mayar da martani mai zafi ga Sheikh Adam Muhammad Albaniy kan sukar sulhu da Bello Turji
- Asada ya ce ya sha ba jami’an tsaro bayanai har aka kai wa Bello Turji hari, lamarin da ya fusata rikakken dan bindigan matuka
- Ya bayyana cewa Bello Turji ya taba yin bidiyo yana masa barazana saboda bayanan da suka kai ga kisan mutanensa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Wasu malaman Musulunci suna ci gaba da mayar da martani kan tattaunawa da Bello Turji da wasu yan ta'adda.
Malam Murtala Asada ya yi martani ga Sheikh Adam Muhammad Albaniy game da sukar sulhu da Bello Turji.

Source: Facebook
Turji: Murtala Asada ya yi martani ga Albaniy
Malam Murtala Asada ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Malam Asada ya yi martani mai zafi game da kalaman Sheikh Albaniy wanda ya yi masa raddi.
Shehin malamin ya yi alfahari cewa babu wanda ya addabi Bello Turji a rayuwarsa kamar Murtala Asada.
Ya ce:
"Amma cikinsu an samu wasu sun yi tambaya, wai Murtala Asada maganganun da ka ta yi shekaru meye fa'idar da suka yi.
"Idan da kana da wayo da kafi kowa sani, idan ba girma ya ragi wayo ba akwai wanda ya dami Bello Turji kaman Asada.
"To sai ka tambayi Bello Turji me yasa ya damu da Murtala Asada, in gaskiya ne ya damu da kai."

Source: Facebook
Yadda Murtala Asada ke addabar Bello Turji
Murtala Asada ya ce Bello Turji da kansa ya san barnar da yake yi masa har ya kawo misalai irin abubuwan da yake aikawa jami'an tsaro.
Ya ce akwai lokacin da fitar da bayanai har aka yi nasarar kai harin bam gidan Bello Turji wanda ya fusata shi sosai.

Kara karanta wannan
Ta fara tsami: Shehi ya gorantawa Murtala Asada game da tattaunawa da Bello Turji
Ya kara da cewa:
"Amma shi Bello Turji ya san barnar da Murtala ke yi masa, zan ba ku misali na sha fadawa jami'an tsaro inda Turji yake.
"Na sha fadin abubuwa kan Turji ga kaza ga kaza, har gidan Bello Turji na nunawa jami'an tsaro suka kai masa hari .
"A lokacin suna shirin wani biki sojoji suka kai hari har suka hallaka masa mutane, dalilin haka Turji ya yi bidiyo a kaina.
Malamin ya ce ko mutum bai sani ba ya san yana daga cikin mutanen da suka bayar da gudummawa a wannan harka."
"A bidiyonsa yana cewa a fadawa masu malamai, a fadawa Murtala Asada idan yana da wani hukunci da ya fi na Allah ya yi.
"To wannan bidiyon da ya fitar yana magana ne kan sakon da Murtala Asada ya ba jami'an tsaro suka kawo masa hari idan kai ba ka sani."
- Cewar malamin
Sheikh Assadus Sunnah ya tattauna da Turji
Kun ji cewa Bello Turji ya amince da dakatar da kai hare-hare kan manoma tare da sakin mutane 32 da ya yi garkuwa da su a dajin Zamfara.
Malamin Musulunci, Sheikh Asadus-Sunnah, ya ce sun gana da Turji har sau uku a cikin watan Yuli domin samun zaman lafiya.
Biyo bayan lamarin, an samu sassaucin zaman lafiya a yankin Shinkafi, inda jama’a ke komawa gona cikin kwanciyar hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

