An Kashe Kusan N50trn: Manyan Ayyuka 16 da Tinubu Ya Yi bayan Cire Tallafin Mai
- Bayan cire tallafin mai, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kashe sama da Naira tiriliyan 49 domin aiwatar da manyan ayyuka a kasa
- Fannonin noma, wutar lantarki, ilimi, kiwon lafiya da dai sauransu ne suka lakume kudin, da nufin farfaɗo da tattalin arzikin kasar
- Sai dai wasu ‘yan Najeriya sun soki gwamnatin, suna tambayar dalilin tsadar kayayyaki duk da an kashe wadannan makudan kudi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Bayan cire tallafin man fetur, Shugaba Bola Tinubu ya kashe tiriliyoyin Naira domin aiwatar da manyan ayyuka da zuba jari a fannoni da dama.
Fannonin da suka lashe kimanin Naira tiriliyan 50 sun hada da noma, wutar lantarki, ilimi har aka gangara zuwa kiwon lafiya, da nufin gyara tattalin arziki a ƙarƙashin Renewed Hope.

Source: Twitter
Manyan ayyukan gwamnatin Tinubu
Mai tallafawa shugaban kasa ta fuskar kafofin sada zumunta, Olusegun Dada ya wallafa kididdigar yadda Tinubu ya kashe wadannan kudi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusegun Dada ya bukaci mutane su je su tantance wadannan ayyuka da aka yi, domin gaskata irin kokarin da Shugaba Tinubu ya ke yi wajen ci gaban kasar nan.
Legit Hausa ta jero bayanai game da yadda Shugaba Tinubu ya kashe tiriliyoyin Naira da inda aka kashe su a kasa:
1. Bankin noma (N1.5trn)
Rahoton ya nuna cewa an fitar da N1.5trn don sake farfado da bankin Noma (BoA), domin tallafawa manoma musamman matasa da mata ta hanyar bayar da rance mai sauƙin biya da shirye-shiryen ci gaban gona.
Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Mohammad Babangida, dan tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin shugaban bankin BoA.

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5
2. Layin dogo na Gabas ($3bn)
Tinubu ya kuma amince da kashe $3bn don farfaɗo da layin dogo na Gabashin Najeriya wanda ya taso daga Port Harcourt zuwa Maiduguri.
Idan aka kammala aikin, layin dogon zai haɗa yankuna da dama tare da farfaɗo da kasuwanci a Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas.
3. Biyan bashin kamfanonin wuta (N4trn)
An ware N4trn domin biyan tsofaffin bashin da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki (GENCOs), don dawo da kwanciyar hankali a bangaren samar da haske a kasar nan.
4. Tallafin wutar lantarki (N213.7bn + N1.2trn)
Gwamnatin Tinubu ta ware N213.7bn don ayyukan wutar lantarki, da kuma N1.2trn (na yarjejeniyar gwamnati da Bankin Duniya) don ƙara ƙarfin samar da wuta a ƙasa baki ɗaya.
Sauran manyan ayyukan Tinubu
- N150bn – Tallafin farko ga hukumar zuba jari ta Kudu maso Gabas (SEIC)
- N4.2bn – TETFund da shirye-shiryen binciken ilimi.
- N24bn – Tsarin samar da wuta a kwalejojin kimiyya.
- N45.9bn – Tallafi ga cibiyoyin kiwon lafiya 8,800.
- N825bn – Sabunta gine-gine a ƙarƙashin UBEC da kuma gina sababbin makarantu tara.
- N200bn – Rance mai rahusa ga kanana da matsakaitan 'yan kasuwa ta hannun bankin masana'antu.
- N45,000 – Tallafin wata-wata ga ɗaliban kwalejojin fasahohi.
- N500m – Shirye-shiryen ƙarfafa mata.
- $7bn – Biyan bashin ajiyar kuɗin waje.
- N18bn – Biya bashin inshora ga jami’an tsaro.
- N683.43bn – Kudaden da aka ware wa jami’o’in gwamnati a 2024.
- N22trn – Bashin babban banki don tallafawa kasafin kuɗi.

Source: Twitter
Makasudin wadannan ayyuka
Rahoton ya nuna cewa kashe waɗannan kudi da nufin farfaɗo da ɓangarorin noma, sufuri, wutar lantarki, ilimi da lafiya, tare da samar da ayyukan yi da ƙara ƙarfin tattalin arzikin ƙasa.
Amma masu amfani da kafofin sada zumunta sun caccaki gwamnati kan wadannan ayyuka:
@kadmaye:
"Zuki ta malle. Ai idan kayayyaki suka yi sauki a kasuwa, 'yan Najeriya ba sa bukatar wani dan amshin shatan 'yan siyasa ya zo na fada masu cewa gwamnati na aiki."
@phreshconcept:
Bayan duk wadannan kudaden da kuka kashe, nawa ake sayar da bokitin garin kwaki, nawa kofin shinkafa, nawa ake sayar da taliya? Mu wadannan ne matsalolinmu ba wai a zo ana yi magana bayani kan kudin iska ba."
@KnawtieGbedu:
"Sai dai in ce sannunku da kokari. Don ni babu daya daga cikin abubuwan da ka lissafa da ya shafe ni a matsayina na dan Najeriya.
"Ina ci gaba da fama da tsadar rayuwa, yayin da kasar ke ci gaba da yi mun daurin huhun goro, duk da kun ce an kashe tiriliyoyin Naira a saukaka rayuwata."

Kara karanta wannan
Tinubu: Gwamnati ta kashe N26.38bn a kan jiragen shugaban ƙasa a cikin watanni 18
Tinubu zai gina layin dogo a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya za ta gina titin jirgin kasa a Kano wanda zai rage cunkoson abubuwan hawa a birnin.
Hon. Abubakar Kabir Bichi ya bayyana cewa idan aka kammala aikin, to layin dogon zai ƙara daraja ga tattalin arzikin jihar Kano da Arewa baki daya.
Bichi ya ce shirin na N1.5tr yana cikin muhimman ayyukan da Shugaba Bola Tinubu zai aiwatar a Arewacin Najeriya kamar yadda ya yi alkawari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

