Bayan Adamawa, NiMet Ta ce Jihohin Arewa 2 Za Su Fuskanci Ambaliya Ranar Talata
- NiMet ta yi gargadi cewa mamakon ruwan sama a ranar Talata zai iya jawo ambaliya a Adamawa, da wasu jihohi na Arewa
- Hukumar ta yi hasashen ruwan sama mai karfi zai sauka a jihohi da dama ciki har da Borno, Bauchi, Kano, Kaduna da Benue
- NiMet ta shawarci mazauna garuruwan da ke cikin hadarin ambaliya da su dauki matakai na kare rayuka da dukiyoyinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jihohin Arewa uku suna cikin tsananin hatsarin ambaliyar ruwa yayin da NiMet ta saki hasashen yanayi na ranar Talata, 12 ga Agusta, 2025.
Hasashen yanayin, ya nuna cewa mamakon ruwan sama da zai ci gaba da sauka ba tsagaitawa ne zai jawo ambaliya a Adamawa da sauran jihohin biyu.

Asali: Original
Hukumar hasashen yanayin ta kasa, ta saki wannan rahoto ne a cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na X a daren ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen yanayi a wasu jihohin Arewa
Sanarwar NiMet ta ce za a samu hadari mai hade da tsawa da kuma ruwan sama a sassan jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma a safiyar Talata.
Jihohin da ake sa ran ruwan zai sauka sun hada da Borno, Bauchi, Jigawa, Kano, Zamfara, Kaduna, Sokoto, Kebbi, Katsina, Yobe, Adamawa, da Taraba.
Daga yammaci har zuwa dare, NiMet ta ce ruwan sama zai ci gaba da sauka a wasu sassa na jihohin Katsina, Zamfara, Kebbi, Yobe, Gombe, Bauchi, Borno, Kaduna, Kano, Jigawa, Taraba, da Adamawa States.
Hadarin ambaliya a jihohi biyu
Sakamakon wannan ruwan sama da za a dauki dogon lokaci ana yi, hukumar NiMet ta ce jihohin Adamawa da Taraba za su gamu da ambaliya.
Hukumar ta gargadi mazauna wadannan jihohi biyu da su dauki matakan gagawa yayin da ta jaddada cewa:
"Ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai zuba ba tare da kakkauta wa ba zai jawo ambaliya a Adamawa da Tabara. Lallai suna cikin hadarin ambaliya."

Kara karanta wannan
Ranar Lahadi: Mamakon ruwan sama zai haddasa ambaliya a Katsina, Neja da jihohi 12
Hasashen yanayi a Arewa ta Tsakiya
A shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa, hukumar hasashen yanayin ta ce za a samu ruwa mai matsakaicin karfi a Abuja da jihohin Plateau, Nasarawa, Benue, Kogi, da Niger States a safiyar Talata.
A yammacin ranar kuwa, za a samu gangamin hadari da tsawa, tare da saukar ruwan sama a Abuja da wasu sassan jihohin Plateau, Niger, Nasarawa, Benue, Kwara, da Kogi.
Sanarwar NiMet ta ce:
"Ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai zuba ba tare da kakkauta wa ba zai jawo ambaliya a jihar Benue."

Asali: Original
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
A safiyar Talata, za a samu ruwan sama a wasu sassan Imo, Ebonyi, Abia, Anambra, Ogun, Ondo, Oyo, Delta, Cross River, da Akwa Ibom States da ke Kudancin kasar nan.
Zuwa yammaci kuwa, ana sa ran ruwan masa mai matsakaicin karfi zai sauka a dukkanin jihohin shiyyar.
Hukumar NiMet ta shawarci wadanda ke zaune a garuruwan da ke da hadarin ambaliya su dauki mataki, yayin da ta bukaci hukumomi su shirya kai dauki idan an samu ambaliyar.
Ambaliya za ta shafi jihohi 30 a 2025
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta bayyana yiwuwar ambaliya a garuruwa 1,249 da ke cikin kananan hukumomi 176 na jihohi 30 da Abuja.
Ministan harkokin ruwa, Farfesa Joseph Utsev, ya ce sauyin yanayi na kara haddasa ambaliya, wanda zai shafi sana'o'i, muhalli da zirga-zirgar ruwa.
Rahoton hukumar NIHSA na 2025 ya lissafa jihohi 30 da ambaliyar ruwan za ta shafa da suka hada da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra da Bauchi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng