Duk da Sabuwar Doka, Katsina da Jihohin Arewa 14 Sun Ki Biyan Ƴan Fansho akalla N32,000

Duk da Sabuwar Doka, Katsina da Jihohin Arewa 14 Sun Ki Biyan Ƴan Fansho akalla N32,000

  • Kungiyar NUP ta bayyana cewa jihohin Arewa huɗu ne kacal suka bi dokar biyan mafi ƙarancin kudin fansho na N32,000
  • Shugaban kungiyar, Kwamared Mohammed Sali, ya ce akwai jihohin da har yanzu suke biya tsofaffin ma’aikata ₦3,000 ko ₦5,000
  • NUP ta bukaci gwamnatocin jihohi 15 ciki har da Katsina da su fara aiwatar da sabon fanshon N32,000 ga tsofaffin ma'aikatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Kungiyar tsofaffin ma’aikata ta Najeriya (NUP) reshen Arewa ta nuna damuwarta kan yadda har yanzu wasu jihohin shiyyar ba su karawa mambobinta kudin fansho ba.

Kungiyar NUP ta ce jihohi huɗu ne kacal daga cikin jihohi 19 na Arewa suka bi umarnin gwamnatin tarayya na biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000 a wata.

NUP ta zargi gwamnatocin Katsina, Taraba da wasu jihohi 13 da kin fara biyan 'yan fansho N30,000
NUP ta ce gwamnatin Katsina na biyan 'yan fansho N5,000 yayin da ake biyansu N3,000 a Taraba. Hoto: @GovAgbuKefas, @dikko_radda
Source: Twitter

NUP ta yi magana kan kudin 'yan fansho

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta yi wa APC illa a mazabar Ganduje a Kano

Shugaban NUP, Kwamared Mohammed Sali, ya bayyana hakan a jihar Kaduna yayin da yake jawabi a taron kungiyar na Arewa, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamared Mohammed Sali ya bayyana cewa jinkirin jihohi na kara kudin fansho “babban rashin adalci ne” ga tsofaffin ma'aikata da suka sadaukar da shekaru masu yawa wajen yi wa kasa hidima.

“Jihohi huɗu ne kacal daga cikin 19 a yanzu suke biyan mafi ƙarancin kudin fansho na ₦32,000. Akwai wasu jihohi da har yanzu suke biyan tsofaffin ma'aikata N3,000, N4,000 ko N5,000, wanda hakan babban rashin adalci ne," inji Sali.

NUP ta yi magana kan fita zanga-zanga

Ya jaddada cewa kungiyar za ta ci gaba da daukar matakan tattaunawa da gwamnatocin jihohi maimakon tashin hankali don matsa wa jihohi su bi dokar sabon mafi karancin albashi.

Kwamared Sali ya ce:

“Ba za mu ce za mu ja daga da kowace jiha ba, shekarunmu sun wuce na yin fada da kowa. Mu dai iyayenku ne; Ko kuna so ku ga iyayenku suna gudu a titi saboda an jefa masu hayaki mai sa hawaye? Mu dai za mu bi kadi ne ta hanyar tattaunawa da jihohin da abin ya shafa."

Kara karanta wannan

Bayan bidiyon Dan Bello, Gwamna Abba Yusuf ya kwace kwangilar aikin titi a Kano

Mohammed Sali ya bayyana cewa jihar Adamawa na dab da fara biyan mafi ƙarancin fanshon ₦32,000 ga tsofaffin ma'aikata.

“Gwamnan Adamawa ya kafa kwamiti na musamman, har ya kammala aikinsa, yanzu muna jiran amincewarsa kawai a fara biya,” inji Sali.
Kungiyar NUP ta yabawa Uba Sani kan biyan yan fansho N30,000 duk wata
NUP ta roki gwamnan Kaduna, Uba Sani ya kara kudin 'yan fansho zuwa N32,000 daga N30,000. Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Kudin da jihohin Arewa ke ba 'yan fansho

Sakataren kungiyar, Alhassan Balarabe Musa, shi ma ya yi Allah-wadai da banbancin da ke tsakanin albashin tsofaffin ma'aikata da irin makudan kudaden da ake ba 'yan siyasa duk wata.

“Idan ɗan siyasa, bayan shekaru huɗu ko takwas, yana karɓar kudi masu yawa, to yaya matsayin dan fansho da ya shafe shekaru 35 ko fiye da haka yana yi wa kasa hidima?
"Akwai jihohi, irin su Taraba da har yanzu suke biyan 'yan fansho N3,000, irin su Katsina kuma suna biyan N5,000, Zamfara ma haka. Wannan abin takaici ne."

- Alhassan Balarabe Musa.

Ya ce jihar Kaduna ita ce kadai a Arewa maso Yamma da ke biyan N30,000, amma ya roƙi Gwamna Uba Sani da ya ƙara kudin zuwa N32,000 kamar yadda gwamnatin tarayya ta yanke.

Kara karanta wannan

Shirin Hajjin 2026 ya kankama, NAHCON ta fadi miliyoyin da alhazai za su tanada

Gwamnati za ta karbe gidajen tsofaffin ma'aikata

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fara tattara sunayen ma'aikatan da suka yi ritaya amma suka kasa biya cikakken lamunin gidajen da suka karba.

Hukumar lamunin gidajen ma'aikatan gwamnati ta tarayya (FGSHLB) ce ke da alhakin tattara sunayen kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Ngozi Obiechina, ta bayyana.

Sanarwar Ngozi ta bayyana ta cewa hukumar za ta dauki matakan shari'a da doka don dawo da kadarorin da aka ba ma'aikatan da basu biya bashin nasu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com