Abubuwa 8 da Suka Bambanta Shugaba Tinubu da su Buhari, Jonathan da 'Yar Adua

Abubuwa 8 da Suka Bambanta Shugaba Tinubu da su Buhari, Jonathan da 'Yar Adua

  • Fadar shugaban kasa ta bayyana siffofi takwas da suka bambanta Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin da aka yi a kasar
  • Daniel Bwala ya ce Shugaba Tinubu na da siffori irin su yafiya, yakini a kan mutane, rashin son kai da hadin kai don cimma nasara
  • Bwala ya kara da cewa wadannan siffofi ba za a samu rabinsu a wajen abokan hamayya ba, don haka Tinubu bai damu da 2027 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fadar shugaban kasa ta lissafa muhimman abubuwa da suka bambanta Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin da aka yi a kasar nan.

Fadar shugaban kasar ta kawo wannan batun ne matsayin martani ga wadanda da ke tunanin hadakar 'yan adawa za ta iya razana Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na fama da rashin lafiya? Fadar shugaban kasa ta yi bayani

An bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya bambanta da sauran shugabanni ta siffofi 8
Bola Ahmed Tinubu tare da Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zaben 2023. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Siffofi 8 na Shugaba Bola Tinubu

Mai ba shugaban kasa shawara kan yada manufofin gwamnati, Daniel Bwala ya wallafa a shafinsa na X cewa abubuwa takwas suka bambanta Tinubu da sauran shugabanni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Jarumtaka:

A cewar Bwala, Tinubu na da tarihin ɗaukar matakai masu tsauri da ake buƙata wajen tafiyar da kasa, ko da kuwa hakan zai haifar da suka.

2. Ladabi da kiyaye tsari:

Mai ba da shawarar ya ce shugaban ƙasa na bukatar kyakkyawan aiki daga waɗanda ke yiwa kasa aiki, kuma yana jagoranci ta hanyar da zai zama abin koyi.

3. Karfin gwiwa:

Da zarar Tinubu ya ɗauki shawarar yin abu da yake ganin daidai ne, Bwala ya ce “babu abin da zai iya hana shi ko karkatar da shi daga wannan abu.”

4. Yana fadada tunani:

Bwala ya bayyana Tinubu a matsayin wanda koyaushe ke son koyon sababbin abubuwa kuma a shirye yake ya saurari sababbin shawarwari don inganta gwamnati.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Yadda dan sanda ya tsere da gudu bayan kama kwamishinansu

"Tinubu ba ya da son kai" - Bwala

Mai ba shugaban kasa shawarar ya ci gaba da jero siffofin shugaban kasa Bola Tinubu da cewa:

5. Yawan afuwa:

Ya ce shugaban ƙasa na ba mutane damar wanke kansu idan sun yi ba daidai ba, dabi’ar da ya koya daga mahaifiyarsa wadda ta jagoranci ƙungiyar ‘yan kasuwar mata.

Daniel Bwala ya ce Shugaba Bola Tinubu ya kasance mutum wanda ba ya da son kai
Shugaba Bola Tinubu a tsaye a zauren majalisar zartarwa yayin da ake shirin fara taron FEC. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

6. Yakini a kan mutane:

A cewar Bwala, Tinubu na ba wa abokan aikinsa kwarin gwiwa da duk wata amincewa da suke buƙata domin cimma nasara a ayyukan da aka dora musu.

7. Rashin son kai:

Mai ba da shawarar ya ce Tinubu ya kasance a koyaushe yana son ɗaga darajar mutane da tabbatar da sun cimma burinsu a bangaren da suka zaɓa.

8. Haɗin kai:

Bwala ya kwatanta shi da tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln, yana mai cewa Tinubu na ganin haɗin kai a tsakanin bangarori daban-daban ne mabuɗin cimma nasara.

A karshe, hadimin shugaban kasar ya ce "waɗannan siffofi, ba za ka samu rabinsu a cikin abokan hamayyarsa ba,” yana mai cewa wannan ne ma dalilin da ya sa Tinubu bai damu da duk wani shiri na kifar da shi a 2027 ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi martani mai zafi, ta ce ana zuzuta batun yunwa a Najeriya

'Lafiyar Tinubu kalau' - Bayo Onanuga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta karyata rahotannin da ake yadawa cewa Shugaba Bola Tinubu yana kwance rigi-rigi ba shi da lafiya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar da sanarwa cewa Tinubu yana nan cikin koshin lafiya, don haka karairayi ne kawai ake yadawa.

Bayo Onanuga ya roki 'yan Najeriya da su toshe kunnuwansu daga sauraron masu yada jita-jitar rashin lafiyar shugaban kasar, wanda ya ce farfaganda ta ce kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com