'Yan Ta'addan ISWAP Sun Yi Ta'asa yayin wani Hari a Borno
- 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kara aikata ta'addancin da suka saba yi a jihar Borno duk da kokarin ganin bayan miyagun
- Miyagun 'yan ta'addan sun je har gida sun yi awon gaba da wani shugaban kungiyar mafarauta, kafin daga bisani suka kashe shi har lahira
- Harin ya kara fito da matsalar rashin tsaron da aka dade ana fama da ita a wadda ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar Borno
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Ana zargin cewa mayakan kungiyar ta’addancin ISWAP sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a jihar Borno.
'Yan ta'addan na ISWAP sun kashe shugaban mafarautan ne na kauyen Garjang, a karamar hukumar Damboa, jihar Borno.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan ISWAP sun yi ta'asa a Borno
Majiyoyin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe, a ranar Lahadi, 10 ga watan Agustan 2025.
An bayyana cewa wanda aka kashe, mai suna Habu Dala, mai shekaru 53, 'yan ta'adda ne suka sace daga gidansa.
Bayan 'yan ta'addan sun sace shi, sun bi da shi ta hanyar kauyen Mulharam zuwa kauyen Forfot, duk a cikin karamar hukumar Damboa.
Bayan samun labarin sace shi, mutanen kauyen sun taru inda suka shiga neman Habu Dala domin cetonsa.
Bayan wani lokaci suna bincike, sun gano gawarsa a wani wuri, kuma jikinsa na dauke da raunukan harbin bindiga.
Daga bisani dakarun sojoji na rundunar Operation HADIN Kai tare da mambobin kungiyoyin 'yan sa-kai na CJTF da mafarauta, sum isa wajen da aka gano gawar domin gudanar da bincike.
An dauki gawar zuwa babban asibitin Damboa, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. Bayan haka kuma, aka mika gawar ga iyalinsa domin yi masa jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
'Yan ta'adda na firgita jama'a
Wannan lamari ya sake tayar da hankulan al’ummar yankin, musamman ganin yadda hare-haren ‘yan ta’adda ke ci gaba da faruwa duk da kokarin jami’an tsaro na kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Asali: Original
Rasuwar shugaban mafarautan dai babbar rashi ce ga yankin, musamman ma ga ‘yan kungiyar mafarauta da suka dade suna aiki kafada da kafada da shi wajen yaki da mayakan ISWAP da Boko Haram.
Rahotanni sun nuna cewa, bayan faruwar lamarin, an kara tsaurara matakan tsaro a yankin don hana sake faruwar irin wannan hari a nan gaba.
Sojojin Borno sun hallaka 'yan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram bayan sun yi artabu da su a jihar Borno.
Sojojin sun samu nasarar ne yayin wani artabu da suka yi a kan hanyar Mayanki da ke yankin Dar El-Jamal bayan sun shiryawa 'yan ta'addan kwanton bauna.
A yayon artabun da aka gudanar, sojoji sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda bakwai tare da kwato makamai a hannunsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng