Sokoto: Ƴan Bindiga Sun Shammaci Masallata a Sallar Isha, Sun Kashe Wasu da Dama
- An shiga tashin hankali a Sokoto bayan ’yan bindiga sun kai hari yayin sallar Isha a kauyen Marnona, karamar hukumar Wurno
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun hallaka wasu masallata sannan suka yi garkuwa da mutane da dama, suka tafi da su cikin daji
- Har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga jami’an tsaro ko hukumomin jihar kan lamarin ko matakan da ake dauka don kare al’umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - An shiga tashin hankali bayan kai wani mummunan harin yan bindiga a jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun hallaka wasu da dama kuma suka yi garkuwa da mutane zuwa daji.

Source: Facebook
Shafin Bakatsine da ke kawo rahotanni da suka shafin matsalar tsaro shi ya tabbatar da haka a manhajar X a yau Lahadi.
Harin yan bindiga ya yi sanadin masallata
Ko a kwanakin baya ma, yan bindiga sun kai hari a masallaci kuma a jihar Sokoto inda aka tabbatar sun sace mutane da dama.
Maharan sun afka wa wani masallaci a garin Bushe na ƙaramar hukumar Sabon Birni, inda suka sace akalla mutum 10, ciki har da liman.
Rundunar ’yan sandan Sokoto ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa ana kokarin ceto mutanen da 'yan bindigar suka sace a wancan lokaci.
Wani dan majalisar dokokin jihar ya yabawa sojoji bisa hana ’yan bindigar yin garkuwa da karin mutane bayan sun kai mummunan harin.

Source: Original
An sake kai hari masallaci a sallar isha
Majiyoyi sun ce maharan sun kai harin ne ana tsaka da sallar Isha a kauyen Marnona da ke jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne a daren jiya Asabar 9 ga watan Agustan 2025 a kauyen da ke karamar hukumar Wurno.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa
An tabbatar da cewa maharan sun hallaka masallata sannan suka kwashe wasu daga cikinsu zuwa cikin daji domin neman kuɗin fansa.
Sanarwar Bakatsine ta ce:
Jiya da daddare, ’yan bindiga sun kai wa masu ibada hari yayin sallar Isha’i a kauyen Marnona, karamar hukumar Wurno, jihar Sokoto.
"An harbe wasu daga cikin masu ibadar, sannan kuma an yi garkuwa da wasu da dama aka tafi da su cikin daji."
Babu wani martani daga jami'an tsaro, hukumomi
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wani bayani daga jami'an tsaro kan abin da ya faru.
Har ila yau, daga ɓangaren hukumomi a jihar babu sanarwa ta musamman kan lamarin ko kuma kokarin dakile hakan.
Mazaunin Sokoto ta tattauna da Legit Hausa
Ahmad Muhammad Wababe ya yi magana kan matsalolin da suke ciki na hare-haren yan bindiga.
Wababe ya ce a karamar hukumar Dange Shuni da Tureta suna cikin tashin hankali fiye da tunanin mutum.
Ya ce:
"Yanzu gaskiya ƙananan hukumomin Dange Shuni da kuma Tureta suna cikin tashin hankali sosai saboda suna kusa da Zamfara ne shiyasa."
Ya ce daren ranar Laraba da misalin karfe 9:30 to 10:30 kan hanyar Gusau kusa da dai titin Tureta aka samu wasu yan bindiga suka yi garkuwa da wasu mutanen Dange Shuni.
Sannan sun sace wasu yan kauyukan da ke da kusanci da ita daidai da Mashayar Maikine abin ya faru.
Yan bindiga sun kashe masallata a Zamfara
A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a masallacin Dole Moriki da ke Zurmi a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yayin harin, an harbe mutum daya da kuma jikkata wasu biyu yayin sallar Isha.
Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare lokacin da mutanen ke tsaka da ibada lamarin da ya tayar da hankalin al'umma.
Asali: Legit.ng

