Fitaccen Mawaki a Arewacin Najeriya, Ali Jita Ya Zama Mai Unguwa a Kano

Fitaccen Mawaki a Arewacin Najeriya, Ali Jita Ya Zama Mai Unguwa a Kano

  • Fitaccen mawaki Ali Jita ya samu sarautar mai unguwa a 'Ado Bayero Royal City' a Darmanawa, Kano a bikin nadin da aka gudanar
  • Hakimin Darmanawa, Sarkin Yakin Kano, ya ja hankalin sabbin masu sarauta da su rike gaskiya da amana wajen sauke nauyin al’umma
  • Ali Jita ya gayyaci jama’a tun ranar Juma’a domin taya shi murna da addu’o’i, bikin ya gudana yau da safe a fadar Hakimin Unguwa Uku

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Fitaccen mawaki a Arewacin Najeriya, Ali Jita ya samu sarautar gargajiya mai muhimmanci a Kano.

An tabbatar da cewa Ali Jita ya samu sarautar mai unguawar 'Ado Bayero Royal City' da ke Darmanawa a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ali Jita ya samu sarautar gargajiya a Kano
An nada Ali Jita a matsayin mai unguwa a Kano. Hoto: Ali Jita.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani faifan bidiyon nadin sarautar da Sarauta TV ta wallafa a shafin Facebook a yammacin yau Asabar 9 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

An gudanar da nadin sarautar a Darmanawa a fadar Hakimin Unguwa Uku da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.

Ali Jita ya gayyaci al'umma nadin sarauta

Tun farko mawakin ya gayyaci al'umma zuwa bikin a jiya Juma'a 8 ga watan Agustan 2025 domin taya shi murna da addu'o'i.

A cikin sanarwar da ya wallafa a Facebook, Ali Jita ya ce za a gudanar da bikin nadin sarautar a ranar Asabar 9 ga watan Agustan 2025.

Ya ce za a gudanar da bikin da misalin karfe 10:00 na safe a fadar Hakimin da ke Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni da ke jihar Kano.

Ali Jita ya zama basaraken gargajiya a Kano
Fitaccen mawaki, Ali Jita ya zama mai unguwa a Kano: Hoto: Ali Jita, Sarauta TV.
Source: Facebook

An nadawa Ali Jita sarautar gargajiya a Kano

A cikin bidiyon nadin sarautar, an gano yadda aka nadawa Ali Jita rawani tare da yi masa fatan alheri da addu'o'i.

An rubuta a saman bidiyon kamar haka:

"Mai girma Hakimin Darmanawa, Sarkin Yakin Kano, Alhaji Mujtaba Abubakar Abba ya nada fitaccen Mawaki Ali jita sarautar mai Unguwa, tare da sauran mutane 15 da kuma Mukaddashinsa a safiyar yau Asabar.

Kara karanta wannan

Daliban Yobe sun samu tagomashi, gidauniyar Atiku ta dauki nauyin karatunsu

"Bayan kammala nadin Sarautar, Sarkin Yakin Kano ya ja hankalinsu da su dage wajen riko da gaskiya da amana tare da sauke nauyin da ke kansu don tsira har a wajen Ubangiji.
"An ja hanakalinsu ne domin mahimmancin da aikin nasu yake dashi a cikin al’umma da kuma Masarautar Kano baki daya."

Ali Jita na daga cikin mawaka da suka shahara a Arewacin Najeriya kuma ba shi ne mawaki na farko da ya samu sarautar gargajiya ba.

An karawa sarautar Alan Waka girma

Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya daga darajar mawaki Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa) daga Ɗan Amanan Bichi.

Baffa Babba Dan'agundi ne ya bayyana hakan cikin wani bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a kafar sadarwa a ranar Lahadi, 8 ga Yunin 2025.

Dan'agundi ya ce bayan shawarwari daga manyan mutane a Najeriya, Sarki ya yanke shawarar kara darajar Alan Waƙa zuwa Ɗan Amanan Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.