Dandalin Kannywood: Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawaki Ali Jita rasuwa

Dandalin Kannywood: Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawaki Ali Jita rasuwa

- Mahaifin fitaccen mawakin Kannywood, Ali Jita, Alhaji Isa ya rasu

- Ali ita ya yi rashi na mahaifin nasa a daren ranar Juma'a, 5 ga watan Fabrairu

- Abokan sana'arsa sun fito don taya shi alhini da jimamin wannan babban rashi da yayi

Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawakin nan na Kannywood Ali Jita, Alhaji Isa rasuwa.

Marigayin ya rasu a daren ranar Juma’a, 5 ga watan Fabrairu a asibitin Ali Jitan da ke unguwar Shagari Kwatas a garin Kano.

Za kuma ayi jana’izarsa a safiyar yau Asabar da misalin karfe 9:00 na safe.

Dandalin Kannywood: Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawaki Ali Jita rasuwa
Dandalin Kannywood: Allah ya yi wa mahaifin shahararren mawaki Ali Jita rasuwa Hoto: alijita1
Source: Instagram

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Amurka ta goyi bayan Okonjo-Iweala ta jagoranci WTO

Tuni dai abokan sana’arsa suka wallafa labarin mutuwar mahaifin Ali tare da sakon ta’aziyyarsu zuwa ga ahlin.

yakubmohammed_ ya wallafa a shafinsa na Instagram:

“INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJI'UN. Allah Yayiwa Alhaji Isa Mahaifin Abokinmu Ali Isa @alijita1 Jita Rasuwa A Daren Jiya. Za'ayi Jana'izarsa Yau Da Safe Da Misalin Karfe Tara (9).

“Muna Addu'ar Allah Ya Jikansa Ya Gafarta Masa Yasa Aljanna ce Makomarsa. Mu kuma Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Kyau Da Imani.”

fatymuhd ta wallafa:

“Inalillahi wa’inailaihi raju’un Allah Ya Jikan ka Baba Allah Yasa Kaffara ce Allah Yasa mutuwa ta zamo Hutu agareka Nayi matukar rashin Suriki Allah Yasa halinka Nagari yabika Allah yakai Haske kabarin ka Allah Yasa aljanna ce makomar Baba

falalu_a_dorayi ya rubuta:

“Allahu Akbar, Allah ya jikan sa, yai masa rahma, su kuma Allah ya basu hakurin rashinsa. @alijita1”

KU KARANTA KUMA: Ba za mu bari mutum 1 ya jawo mana rikici ba, Ganduje ya bayyana dalilin haramta wa Sheikh Kabara yin wa’azi

nazifiasnanic ya wallafa:

“Inna lilahi WA inna ilaihirrajiun Allah yayi WA Baban Abokin mu Rasuwa @alijita1 zaayi janaizar sa gobe da safe Allah ya yafe masa.”

A wani labarin, mutanen karamar hukumar Dawakin Tofa da ke jihar Kano sun shiga halin juyayi sakamakon mutuwar tsohon dan majalisa, Dr Abdullahi Maikano Rabiu.

A cewar jaridar The Punch, tsohon dan majalisan wakilan ya rasu sakamakon cutar COVID-19 a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu.

Rabiu ya rasu a cibiyar killace masu cutar da ke Kwanar Dawakin Tofa, a Kano, inda yan uwansa suka tabbatar da mutuwarsa ga manema labarai a ranar Alhamis.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel