Kafin Ya Mutu, Tsohon Minista Audu Ogbeh Ya Hango Masifar da Ke Tunkaro Najeriya

Kafin Ya Mutu, Tsohon Minista Audu Ogbeh Ya Hango Masifar da Ke Tunkaro Najeriya

  • Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon ministan noma (2015 zuwa 2019) kuma tsohon ministan sadarwa (1982 zuwa 1983) Audu Ogbeh ya rasu
  • Kafin rasuwar fitaccen dan siyasar, Cif Audu Ogbeh ya bayyana cewa ya hango wata babbar masifa da ke tunkaro kasar Najeriya
  • Audu Ogbeh ya kuma gargadi 'yan Najeriya game da tabarbarewar tattalin arziki, watsi da noma, da rushewar kananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Audu Ogbeh, tsohon ministan noma, ya yi magana a fili kan batutuwan da suka shafi kasa kafin rasuwarsa a ranar Asabar.

Ogbeh, wanda ya taba rike mukamin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya rasu yana da shekaru 78, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Tsohon ministan noma, Audu Ogbeh ya yi magana kan matsalolin Najeriya kafin ya rasu
Cif Audu Ogbeh, tsohon ministan noma, sadarwa, kuma tsohon shugaban PDP na kasa da ya rasu. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Audu Ogbeh ya hango masifar da ke tafe

A wata hira da Daily Trust ta wallafa jim kadan kafin iyalansa su sanar da rasuwarsa, Ogbeh ya bayyana damuwarsa kan makomar Najeriya.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ku yarda da ni, na kasance mutum ne wanda yake cikin bakin ciki, kuma ya gaza samun farin ciki, lallai kullum ina cike da tsoron makomar mu.
"Wataƙila ba zan jima raye ba, yanzu ina kusantar shekaru 80 ne, amma sam bana jin daɗin abin da idanuwana suke gani. Abin yana sanya ni cikin bakin ciki mai tsanani."

- Audu Ogbeh.

Cif Ogbeh ya yi gargadi cewa tabarbarewar tattalin arziki, watsi da harkar noma, da rushewar tsarin gudanar da kananan hukumomi alamomi ne da ke nuna kasa tana cikin hadari.

Ogbeh ya fadi matsalar da matasa ke ciki

A cewar tsohon ministan noman:

“To, ina da mata ɗaya, yara biyar, da jikoki takwas. Amma na kasance mutumin da ke rayuwa cikin bakin ciki domin ina hango wata masifa da ke tunkaro mu.
“Ban ga dalilin da zai sa mu yi tsammanin matasa za su farka wata rana su fara tsalle da murna ba.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, tsohon ministan Buhari, Audu Ogbeh ya rasu

“Kowane matashi na kokarin tura kudi gida ga mahaifiyarsa da 'yan uwansa, wadanda suke tsammanin yana da tarin kudi tunda yana rayuwa a Abuja.
“Amma ba su san cewa ba su da kudin ba. Kuma yawansu na ƙaruwa a birnin, suna ta barin ƙauyukansu suna shigowa birane neman kudi.
“Sai sun isa birnin ne za su gane ashe kallon kitse suke yi wa rogo, rayuwar birnin ba sauki ne da ita ba. Amma ba za su iya komawa ƙauyensu ba, haka za su ci gaba da zama, ana masu kallon kudi, alhalin ba su tara komai ba."
Audu Ogbeh tsohon ministan noma ya gargadi najeriya game da matsin tattali, watsi da noma
Cif Audu Ogbeh, tsohon ministan noma, sadarwa, kuma tsohon shugaban PDP na kasa da ya rasu. Hoto: @FMINONigeria
Source: Facebook

Audu Ogbeh ya tsallake rijiya ta baya

'Dan siyasar ya ba da labarin yadda ya tsira daga yunkurin kashe shi a 1998, inda ya bayyana cewa ubangiji ne kawai ya tseratar da shi.

“Eh, sun karya ƙofa suka shigo. Sun harba alburusai ta ko ina. Sun harbi masu tsarona. Sun harbe ni, suka bar ni cikin jini suka tafi. Wannan idon nawa sai da ya kusa fitowa waje.
“Wasu ma'aikatan gidana sun ji maharan suna shewa, suna cewa ‘Mun kashe shi’. Da suka tafi, ma'aikatan suka zo da ƙarfe 6:00 na safiya suka kaini asibiti. Kaina ya kumbura sosai har na suma."

Kara karanta wannan

'Samu na ya ƙaru': G Fresh ya faɗi miliyoyin da yake samu a TikTok bayan aure

- Audu Ogbeh.

Takaitaccen bayani kan ayyukan Ogbeh

Audu Ogbeh ya yi mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Benue bayan ya shiga siyasa a 1979, a cewar rahoton The Cable.

Ogbeh ya rike mukamin ministan sadarwa na tarayya daga 1982 zuwa 1983 a gwamnatin Shehu Shagari.

Ya zama shugaban jam’iyyar PDP daga 2001 zuwa 2005, sannan ya yi ministan noma daga 2015 zuwa 2019.

Tashin tashina kan rasuwar Sanata Ibrahim

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito ana zargin cewa Sanata Ibrahim Musa Kontagora ya rasu ne saboda rashin cika $15,000 da za a yi masa aiki a wani asibitin Abuja.

Rahotannin sun yi ikirarin cewa asibitin sun nemi a biya su $30,000 don yi masa aiki amma rabi kaɗai iyalansa suka biya wanda ya jawo jinkiri har ya rasu.

Hukumar gudanarwar asibitin ta bayyana cewa wannan rahotanni ba gaskiya ba ne domin har ragowar canji aka mayar wa iyalan sanatan bayan ya rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com