Rayuwa bata taba wuya irin haka ba – Audu Ogbeh ya bukaci FG ta dakatar da kashe-kashe

Rayuwa bata taba wuya irin haka ba – Audu Ogbeh ya bukaci FG ta dakatar da kashe-kashe

- Tsohon ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Audu Ogbeh, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da kashe-kashe a fadin kasar

- Audu Ogbe ya bayyana cewa rayuwa bata taba wahala irin na wannan lokaci ba

- Ya ce zamanin yakin basasa ne lokaci na karshe da kasar Najeriya ta fuskanci yawan kashe kashe na al'ummanta

- Jigon kungiyar dattawan arewan ya ce idan ba a tashi tsaye wajen kare yankin arewa ba toh za a wayi gari a ga babu yankin

Tsohon ministan noma, Audu Ogbeh, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da kashe-kashe a fadin kasar, cewa rayuwa bata taba wahala irin na wannan lokaci ba.

Da yake magana a taron farko na sabbin zababbun shugabannin kungiyar dattawan arewa (ACF) a Kaduna a ranar Laraba, tsohon ministan ya ce lokacin yakin basasa ne lokaci na karshe da kasar ta fuskanci yawan kashe-kashe irin wannan.

Yakin basasar Najeriya wacce ta barke a 1967, ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da miliyan biyu.

An yi yakin ne bayan yankin gabashin Najeriya ta kaddamar da jumhuriyar Biyafara.

Rayuwa bata taba wuya irin haka ba – Audu Ogbeh ya bukaci FG ta dakatar da kashe-kashe
Rayuwa bata taba wuya irin haka ba – Audu Ogbeh ya bukaci FG ta dakatar da kashe-kashe Hoto: Guardian
Asali: UGC

A ‘yan baya-bayan nan, ‘yan fashi, da kungiyoyin ‘yan ta’adda irin su Boko Haram da ISWAP sun tsananta kashe-kashen mutane a yankin arewacin kasar, wanda hakan ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi.

Ogbeh ya yi kira ga sabonta kokarin da ake wajen magance matsalar rashin tsaro, jaridar The Cable ta ruwaito.

“Muna da kabilu sama da 300 a yankin arewa, kuma ba za mu iya bari mu zama wata kungiyar kabilanci ba,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Ba a ga watan sabuwar shekarar Musulunci ba, gobe Juma’a ne 1 ga watan Muharram

“Nauyin da ya rataya a wuyanmu a yanzu ya fi na baya. Bamu fuskanci wannan kalubale ba a baya – kashe-kashe a dare da rana. Rayuwa bata taba yin wahala irin wannan ba illa a lokacin yakin basasa. Idan bamu tsare arewa ba a yanzu, za mu rasa arewa,” ya kara da cewa.

A wani labari na daban, kungiyar SOKAPU ta mutanen kudancin jihar Kaduna, ta na ikirarin an kashe mata mutum 11, daga ciki har da wani Mai unguwa da mahaifiyarsa mai shekaru 97.

A cewar wannan kungiya mai kare al’ummar yankin jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga ne su ka yi wannan danyen aiki a kananan hukumomin Zango-Kataf, Kajuru da Kachia.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin sakataren yada labarai na SOKAPU, Luka Binniyat. Ya ce a yanzu garuruwa 109 da ke yankin kudancin Kaduna su na hannun ‘yan bindiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel