Za a Rusawa Tsohon Gwamna Kadarorin Miliyoyi, an Umarci Ya Kwashe Kayansa a Gida

Za a Rusawa Tsohon Gwamna Kadarorin Miliyoyi, an Umarci Ya Kwashe Kayansa a Gida

  • Tsohon gwamnan jihar Ogun ya shiga damuwa yayin da yake zargin ana yi masa bita da kulli domin ruguza shi
  • Gbenga Daniel, ya zargi Gwamna Dapo Abiodun da amfani da sabuwar doka wajen yi masa barazanar rushe gidaje da gine-ginensa
  • Daniel ya ce gwamnati ta ba shi kwana uku ya kwashe kadarorin da suka hada da Asoludero da otali dinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Ana zargin gwamnan Ogun da amfani da sabuwar doka domin cin zarafin wasu yan siyasa.

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel ya yi zargin abin da ya kira “cin zarafi na siyasa” daga Gwamna Dapo Abiodun.

Ana zargin gwamna da rushe kadarorin yan siyasa
Tsohon gwamna ya zargi Dapo Abiodun da rushe masa kadarori. Hoto: Prince Dapo Abiodun.
Source: Facebook

Tsohon gwamna ya koka da rushe masa kadarori

Hakan na cikin wata sanarwa daga Shugaban Ofishin yada labaransa, Steve Oliyide ya fitar a Sagamu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya samo mafita ga PDP kan mutanen da suka yi mata zagon kasa a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daniel ya zargi Gwamna Abiodun da fakewa da sabuwar doka domin rushe kadarorinsa a Sagamu.

Ya roki manyan ‘yan Najeriya, kungiyoyin farar hula da lauyoyi su shiga su soki abin da ya kira “mummunan amfani da iko” daga gwamnatin jihar Ogun.

Oliyide ya bayyana cewa a daren Juma’a gwamnati ta umarci Daniel ya bar gidansa na Asoludero, da kuma otal otal da yake da su.

Takardar ta ce an gina wadannan kadarori “ba tare da samun lasisin gine-gine ba” kuma “ba tare da isasshen sarari na kariya ba,” bisa bayanin ma’aikatar tsare-tsaren birane.

Umarnin, mai kwanan wata 8 ga Agusta 2025, ya umurci Daniel ya kwashe kayansa cikin sa’o’i 72, idan ba haka ba a rusa su gaba daya.

Tsohon gwamna ya zargi kokarin rushe masa kadarori
Tsohon gwamnan Ogun na zargin Dapo Abiodun da neman rushe masa gidaje. Hoto: Legit.
Source: Original

Ana zargin gwamna da bita da kullin siyasa

Daniel ya ce wannan mataki ya nuna bita da kullin siyasar da wuce gona da iri, ba tare da bin doka ba, The Guardian ta ruwato.

Kara karanta wannan

'Dan shekara 32 ya yi barazanar kashe gwamna, ya jefa kansa a babbar matsala

Sanarwar ta ce umarnin ya saba tsarin da ya tanadi tazara tsakanin sanarwar barazana, umarnin barin wuri, da hukunci, idan akwai.

Ya ce:

“A nan, gwamnati ta bayar da takardar ‘Contravention’ da ‘Notice to Quit’ lokaci guda tare da barazanar rushewa nan da nan."

Daniel ya kara da cewa wannan mataki na nuni da cewa akwai siyasa, tare da amfani da sabuwar doka a baya don kai wa abokan hamayya hari.

Ya ce zargin rashin lasisin gini abin dariya ne, tunda kadarorin sun wanzu tsawon shekaru da dama ba tare da matsala ba.

Daniel ya sha alwashin cewa ba zai yi shiru ba, kuma zai yi amfani da duk hanyoyin shari’a don tabbatar da an hukunta Gwamna Abiodun bisa “cin zarafi.”

Gwamnan Ogun ya maka Sarki a kotu

Kun ji cewa Gwamnatin Ogun ta gurfanar da Sarkin Obafemi, Oba Taofeek Owolabi a kotu bisa zargin kwace da sayar da fili ba bisa ka’ida ba.

An ce Sarkin ya sayar wa wani mutumi wata gona a kan ₦75m, amma ya ki ba masu gonar kuɗinsu, sai ma ya tura masu 'yan daba.

Duk da gayyatar majalisar dokokin jihar da majalisar sarakunan gargajiya, Oba ya ƙi mika wuya, lamarin da ya kai ga gurfanar da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.