Wata Sabuwa: Rasuwar Sanata Ibrahim Musa a Asibitin Abuja Ta Bar Baya da Ƙura
- Ana yaɗa jita-jitar cewa Sanata Ibrahim Musa Kontagora ya rasu ne sakamakon rashin cika $15,000 da za a masa aiki a wani asibitin Abuja
- Rahotannin sun yi ikirarin cewa asibitin sun nemi a biya $30,000 amma rabi kaɗai iyalansa suka biya wanda ya jawo jinkiri har ya rasu
- Hukumar gudanarwar asibitin ta bayyana cewa wannan rahotanni ba gaskiya ba ne domin har ragowar canji aka mayar wa iyalan sanatan bayan ya rasu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Asibitin Nizamiye da ke Abuja ya nuna rashin jin daɗinsa kan rahotannin batanci da ake yadawa kan yadda aka kwantar da Sanata Ibrahim Musa Kontagora har ya rasu.
Wasu rahotanni da ake yaɗawa bayan rasuwar tsohon sanatan sun nuna cewa asibitin ya ƙi kula da lafiyar mairigayin saboda iyalansa sun gaza biyan kudin aiki $30,000.

Kara karanta wannan
Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

Source: Facebook
A wata tattaunawa ta musamman da jaridar Vanguard a daren Juma’a, mai magana da yawun asibitin, Mohammed Abubakar, ya ƙaryata wannan rahoto.
Abin da ya faru a asibitin da Sanatan ya yi jinya
Ya ce saɓanin abin da ake yadawa, dangin marigayin sun biya kuɗin maganinsa gaba ɗaya, kuma ba a binsu bashin ko Naira ɗaya.
Ya kuma kara da cewa asibitin ya mayar wa iyalan marigayi Sanata Ibrahim Musa kuɗin da suka ajiye domin kula da shi bayan rasuwarsa.
Abubakar ya tabbatar da cewa ana biyan kuɗin aiki a asibitin da Naira, sabanin rahotannin da ake yaɗawa cewa ana karɓar kuɗi ne da Dalar Amurka.
Ya bayyana cewa dangin marigayin sun damu ƙwarai da wannan rahoto, kuma sun kira asibitin domin su nesanta kansu daga wannan zargi.
Yadda Sanata Ibrahim ya kwanta ya rasu
“Wannan bawan Allah (marigayi sanata) ya zo daga wani asibiti kusan kwanaki 10 da suka gabata, kuma da isowarsa nan take aka yi masa tiyata.
“Ya zauna a sashen kulawa ta musamman (ICU), har ma sai da muka mayar wa iyalansa da ragowar kuɗinsu. Don haka ba mu san daga ina wadannan rahotannin batanci ke fitowa ba.
"Su kansu ƴan uwan sanatan ba su ji daɗin irin wannan labari ba saboda ba gaskiya ba ne, sun ce ba daga gare su labarin ya fito ba.
"Sai dai duba da sanata ɗan siyasa ne, watakila wani ɗan siyasa ne ya yi hakan, amma ba gaskiya ba ne, mun yi iya ƙoƙarinmu, kowa ya san waraka tana hannun Allah ne, ba hannun likita ba."
- Mohammed Abubakar.

Source: Facebook
Abubakar ya ƙara da cewa asibitin ya yi duk mai yiwuwa wajen ceton rayuwar sanatan, kuma an kammala dukkan matakai na magani yadda ya dace.
Tsohon minista, Audu Ogbeh ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan harkokin noma a Najeriya, Audu Ogbeh, ya riga mu gidan gaskiya a yau Asabar yana da shekara 78.
Sanarwar da iyalansa suka fitar ta bayyana cewa marigayin ya rasu cikin lumana bayan shafe shekaru yana hidima ga kasa.
Audu Ogbeh ya yi aiki a matsayin ministan noma daga 2015 zuwa 2019 a gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
