Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Ministan Buhari, Audu Ogbeh Ya Rasu
- Tsohon ministan noma na tarayyar Najeriya, Audu Ogbeh, ya rasu a yau Asabar yana da shekara 78 a duniya
 - Iyalan Ogbeh sun bayyana cewa ya rasu cikin lumana, kuma ya bar kyakkyawan tarihi na gaskiya da hidima ga kasa
 - An ce za a sanar da cikakkun shirye-shiryen jana’iza daga baya, tare da neman mutane su kiyaye sirrin marigayin
 
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Tsohon ministan noma da cigaban karkara na Najeriya, Cif Audu Innocent Ogbeh, ya rasu a yau Asabar, 8 ga Agusta, 2025 yana da shekara 78.
Iyalan mamacin sun fitar da sanarwa a yau, inda suka bayyana cewa marigayin ya rasu cikin lumana bayan shafe shekaru yana hidima ga kasarsa.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa sun yi godiya ga abokai, ‘yan uwa da jama’a baki daya bisa addu’o’i da ta’aziyya, tare da neman a basu damar yin jimami cikin kwanciyar hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Audu Ogbeh ya yi aiki da Buhari
An haifi Audu Innocent Ogbeh a ranar 28 ga Yuli 1947, ya kasance manomi, marubucin wasan kwaikwayo, kuma dan siyasa.
Ya yi aiki a matsayin ministan noma daga 2015 zuwa 2019 a gwamnatin marigayi shugaba Muhammadu Buhari.
Wasu mukaman da Audu Ogbeh ya rike
Ogbeh ya fara siyasa a 1979 lokacin da aka zabe shi a majalisar dokokin jihar Benue a matsayin mataimakin shugaban majalisa.
Daga baya ya zama ministan sadarwa a shekarar 1982 a zamanin shugaba Shehu Shagari, inda ya yi aiki har zuwa 1983.
Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Audu Ogbeh ya rike shugabancin kungiyar dattawan Arewa ta ACF
Ayyukansa sun shafi bangarori daban-daban, inda ya yi fice wajen bunkasa harkokin noma a kasa.
Yadda Ogbeh ya rike jam'iyyar PDP
A shekarar 2001 aka nada Audu Ogbeh shugaban jam’iyyar PDP, wanda ya rike shugabancin har zuwa 2005.

Kara karanta wannan
A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London
Ko da yake murabus dinsa ya zo da ce-ce-ku-ce, ya ce ya bar mukamin ne don gujewa rikici a jam’iyyar da kuma komawa harkar noma.
A lokacin shugabancinsa, PDP ta samu karfin siyasa sosai, duk da cewa akwai kalubale da dama da ya fuskanta.

Source: Facebook
Rawar da Ogbeh ya taka a harkar noma
A matsayinsa na ministan noma, Ogbeh ya gabatar da manufofi da dama don bunkasa amfanin gona, tallafawa manoma da kara samar da abinci a cikin gida.
Ya kasance mai kishin aikin gona tun kafin ya shiga siyasa, inda gonakinsa suka zama cibiyar koyarwa ga matasa.
Mutuwarsa ta bar gibi babba a bangaren noma da siyasa, musamman a Arewa da Najeriya baki daya.
Gwamna Abba ya yi jimamin rasa hadiminsa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi ta'aziyyar rasuwar hadiminsa, Sadiq Gentle.
Rahotanni sun nuna cewa Sadiq ya rasu ne bayan wasu 'yan daba sun kai masa hari, sun sassara shi da makami.
Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin rai sosai tare da tabbatar da cewa za a dauki matakin kama wadanda suka masa lahani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
    