Kashi 90 cikin 100 na shinkafan da ake ci, a kasar nan ake nomawa - Ministan Noma

Kashi 90 cikin 100 na shinkafan da ake ci, a kasar nan ake nomawa - Ministan Noma

Ministan aikin noma da raya karkara, Audu Ogbeh ya bayyana farin cikinsa kan yadda Najeriya ke noma kashi 90 cikin 100 na shinkafar da ake ci kulli yaumin a kasar, ya fadi hakan nan ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, 2019.

Audu Ogbeh ya laburta hakan ne a taron bincike da shirye-shirye da aka gudanar a kwalejin Ilimin binciken aikin noma dake Zaria, jihar Kaduna.

Kashi 90 cikin 100 na shinkafan da ake ci, a kasar nan ake nomawa - Ministan Noma

Kashi 90 cikin 100 na shinkafan da ake ci, a kasar nan ake nomawa - Ministan Noma
Source: Twitter

Taken wannan taro shine: "Inganta fitar da amfanin gona kasashen waje a Najeriya: Rawar ganin da masu ruwa da tsaki zasu taka."

Mista Ogbeh wanda ya samu wakilcin Karima Babangida, diraktar fitar da amfanin gonan ma'aikatar, ta bayyana yadda gwamnatin shugaban Buhari ke mayar da hankali kan yadda yan Najeriya zasu rika noma abincinsu da kansu sabanin shigo da su daga kasashen ketare.

KU KARANTA: Dattawan Borno: Ba mu goyon bayan Ali Ndume

Jawabinsa yace: "Misali daya da zan baku shine a yanzu aka mun shaida shine noman shinkafa, Najeriya ta kasance kasa mafi shigo da shinkafa daga kasar Thailand a duniya."

Amma a yau, mun samu canji wanda ya kai kashi 90 cikin 100 na shinkafan da muke ci a Najeriya a kasar nan ake nomashi, ya kamata mu yabawa manomanmu."

"Najeriya na da ikon ciyar da kanta, kana ta zama babba a fitar da amfanin gona wasu kasashen nahiyar Afrika, Turai, Amurka da Asiya , musamman kasar Sin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel