An Kama Boka Mai ba 'Yan Ta'adda Maganin Bindiga da Kayan Tsafi

An Kama Boka Mai ba 'Yan Ta'adda Maganin Bindiga da Kayan Tsafi

  • Rundunar ‘yan sandan Akwa Ibom ta cafke wani mai yin asiri, Cletus Bassey, bisa zargin bai wa ‘yan fashi magungunan kariya daga harbi
  • An kama shi ne a maboyarsa da ke kauyen Nung Oku, karamar hukumar Uruan, tare da samun bindiga kirar gida tattare da shi
  • Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Timfon John ta ce a yanzu haka bincike na ci gaba don gano sauran abokan harkallar matsafin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Akwa Ibom - Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta samu nasarar kama wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da yin asiri ga ‘yan fashi da makami.

An cafke mutumin mai suna Cletus Effiong Bassey ne bayan samun sahihan bayanan sirri daga al’umma.

An kama boka mai ba da maganain bindiga a Akwa Ibom
An kama boka mai ba da maganain bindiga a Akwa Ibom. Hoto: Legit
Source: Original

Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar, DSP Timfon John, ta tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin ne a daren 29 ga Yuli, 2025, a bukkarsa da ke karamar hukumar Uruan.

Kara karanta wannan

Masu sayar wa ƴan ta'adda bindigogi sun gama guje guje, sun shiga hannu a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DSP Timfon John ta ce mutumin na bai wa ‘yan fashi magungunan kariya daga harbi da sauran nau’o’in tsafi.

'Yan sanda sun kama boka a Akwa Ibom

Daily Post ta wallafa cewa DSP Timfon John ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi amfani da bayanan sirri wajen gano maboyar wanda ake zargi.

Bayan kama shi, rundunar ta gudanar da bincike a gidansa inda suka gano bindiga kirar gida, abin da ya kara tabbatar da zargin hulɗarsa da laifuffukan da suka shafi makamai.

A cewar ta, rundunar ta dauki wannan kame a matsayin ci gaba wajen yaki da ta’addanci da sauran manyan laifuka a jihar.

Ayyukan da ake zargi bokan yana yi

Binciken farko ya nuna cewa Bassey ya dade yana yin asiri ga kungiyoyin ‘yan fashi, musamman samar da maganin harbi.

A cewar jami’an tsaro, tsafin da ya ke yi wa ‘yan fashi yana sa su yi tsammanin ba za a iya harbe su ba, lamarin da ke karfafa musu gwiwar kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta a garin Raan, an rasa rayukan ƴan bindiga 30

Haka kuma, akwai zargin cewa yana hada wasu nau’o’in tsafi ya ke ba mutane, wanda hakan na taimakawa wajen yada barna.

Sufeton 'yan sandan Najeriya, IG Kayode
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IG Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan sanda za su cigaba da bincike

DSP Timfon John ta ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano sauran wadanda ke hada kai da Bassey.

Rundunar ta sha alwashin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa duk masu aikata laifi sun fuskanci fushin hukunci.

'Yan bindiga sun titsiye Sarki a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi wa wani Sarki, Alhaji Babangida Kogo tambayoyi a Zamafara.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kama Sarkin ne a lokacin da ya ke kokarin tafiya zuwa wani waje bayan an yi musu luguden wuta.

Ana zargin yaran Ado Aliero ne suka kama shi domin masa tambayoyi a kan ko yana da hannu wajen tona musu asiri a kan yadda suke ta'addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng