Shirin Hajjin 2026 Ya Kankama, NAHCON Ta Fadi Miliyoyin da Alhazai Za Su Tanada
- NAHCON ta gudanar da taro da shugabannin jin daɗin alhazai don nazari da shirin aikin Hajjin 2026 bayan kammala na bana
- Hukumar ta yabawa gwamnati bisa kokarinta a aikin Hajjin 2025 musamman hana biyan BTA da kati, da biyan kudin jirgi da Naira
- Yayin da Najeriya ta samu kujeru 95,000, NAHCON ta ayyana ₦8.5m matsayin kudin da maniyyata za su ajiyewa na Hajjin badi
- Hajiya Salma Kwatta, ta shaidawa Legit Hausa cewa ta biya kasa da N400,00 a lokacin da za ta je aikin Hajji a shekarar 2006
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Hukumar NAHCON ta shirya taron tattaunawa kan aikin Hajjin 2026 tare da shugabanni da sakatarorin hukumomin jin daɗin alhazai na jihohin Najeriya.
Taron wanda aka gudanar ranar 7 ga Agusta, 2025, ya mayar da hankali ne wajen nazarin yadda aikin Hajjin 2025 ya gudana da kuma fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2026.

Source: Twitter
Wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, daraktar sashen watsa labarai na NAHCON ta fitar a shafin hukumar na X ta bayyana abubuwan da suka gudana a taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON ta fadi alheran gwamnati a 2025
A jawabinsa na bude taron, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya nuna godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake baiwa alhazan Najeriya da kuma hukumar.
Ya bayyana yadda gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin a yarda da biyan kudin jiragen Hajji da Naira, lamarin da ya kare alhazan daga matsin canjin kudin waje.
Farfesa Usman ya kuma yaba da matakin gwamnati na dakatar da tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bullo da shi na tilasta biyan kudin BTA da kati kadai, wanda ka iya jefa alhazai da dama cikin mawuyacin hali.
Ya bukaci mahalarta taron da su fito karara su bayyana abubuwan da suka yi nasara a hajjin bana, da kalubalen da suka fuskanta da kuma gyare-gyaren da ya kamata a yi nan gaba.
₦8.5m ne kudin ajiya na Hajjin 2026
Kwamishinan tsare-tsare da bincike, Farfesa Abubakar Yagawal ne ya jagoranci tattaunawa kan jadawalin Hajjin 2026, yayin da kwamishinan ayyuka, Prince Anofiu Elegushi ya jagoranci bangaren batutuwan aikin hajji.
Prince Elegushi ya bude tattaunawa kan yiwuwar ci gaba da aiki da kamfanonin jiragen sama hudu da suka yi jigilar maniyyata a Hajjin 2025, domin Najeriya ta samu damar tanadin guraben jigilar alhazai tun da wuri.
Bayan tattaunawa, shugaban NAHCON ya ce an amince maniyyata su fara ajiye ₦8.5m domin aikin Hajjin 2026, wanda zai iya sauyawa bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Source: Twitter
Saudiyya ta warewa Najeriya kujeru 95,000
Haka zalika, Farfesa Usman ya sanar da cewa Saudiyya ta ci gaba da bai wa Najeriya kujeru 95,000, kamar yadda aka saba kuma za a warewa jihohi kujeru a 2026 kamar yadda aka yi a 2025.
Shugaban kungiyar sakatarorin hukumar alhazai ta jihohi kuma sakatare na Nasarawa, Alhaji Idris Almakura, ya gode wa NAHCON bisa shirya wannan muhimmin taro da ya bai wa jihohi damar bayyana matsayinsu.
Ya bukaci NAHCON da ta kara karfafa hulɗa da hukumomin jihohi ta hanyar inganta sadarwa da bayar da bayanai cikin lokaci, tare da gaggauta warware sauran abubuwan da suka rage daga aikin Hajjin 2025.
"Hajji na son gagarar talaka" - Hajiya Salma
A zantawar Legit Hausa da Hajiya Salma Isiya da ke garin Kwatta, jihar Katsina, ta nuna damuwa kan yadda duk shekara ake samun karuwar kudin zuwa aikin Hajji.
Hajiya Salma Kwatta ta ce yanzu aikin Hajji na son ya gagari talaka, musamman yanzu da ake fama da matsin tattali a kasar nan.
"Lallai na ga wannan rahoto, a raina na ce yanzu dai aikin Hajji ya fi karfin talaka, masu kudin ma sai wanda ya daure ne zai je.
"Mu a lokacin da muka je aikin Hajji a 2006, 350,000 da doriya muka biya, amma bai kai 370,000 ba gaskiya, a haka a lokacin ana ganin ya yi kudi.
"Amma yanzu ana maganar kusan miliyan tara, ai ka ga bambancin na da yawa. Sai dai, abin da ba ka sani ba shi ne, idan kana da kudin, ba ka jin kyashin zuwa.
"Ni dai ka ga na yi kusan shekaru 19 da zuwa, amma har gobe ina rokon Allah ya sake kira na na koma, don duk wanda ya je dakin ma'aiki, to zai so ya sake komawa."
Jiragen da suka yi jigilar alhazai a 2025
Tun da fari, mun ruwaito cewa kamfanonin jiragen sama na Air Peace, Fly-Nas, Max Air da UMZA ne fadar shugaban kasa ta zaba suka yi jigilar alhazai a 2025.
An zakulo kamfanonin hudu daga cikin 11 da aka tantance bayan an kafa kwamitin tantancewa mai mambobi 32 daga hukumomi daban-daban.
Hukumar NAHCOM ta sanar da cewa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Hajji tsakanin Najeriya da Saudiyya a Jiddah kuma an ba ta kujerun Hajji 95,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



