Musulunci Ya Yi Rashi, Shugaba a Izala Ya Rasu a Garin Argungu
- Shugaban Izala na Argungu, Sheikh Umar Kokoshe ya rasu bayan fama da jinya, za a yi jana'izarsa a filin idi da ke garin
 - Wani malamin addinin Musulunci daga Gombe, Malam Saleh Isah mai tafsiri ma ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya
 - Dubban mutane sun nuna alhini da addu’ar rahama a shafukan sada zumunta kan rasuwar wadannan manyan malamai
 
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Al’ummar Musulmi a Najeriya musamman a Arewacin kasar nan na ci gaba da nuna alhini kan rasuwar malamai biyu a jihohin Kebbi da Gombe.
Shugaban kungiyar Izalatu Bid’a wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) reshen karamar hukumar Argungu, Sheikh Umar Abubakar Kokoshe ya rasu bayan fama da jinya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar shugaban kungiyar ne a wani sako da shafin Jibwis Kebbi ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Sabon shugaban APC da gwamnoni sun gana da Sheikh Jingir, malaman Izala da Darika
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, an samu rahoton rasuwar shugaban makarantar Nurul Huda da ke Madaki, Gombe, Malam Saleh Isah, lamarin da ya jayo masa addu'a daga sassa daban-daban.
Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Kokoshe ya rasu
A ranar Laraba ne aka tabbatar da rasuwar Sheikh Umar Abubakar Kokoshe, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma shugaban Izala na Argungu.
Kungiyar Jibwis ta fitar da sanarwa inda ta bayyana cewa za a gudanar da jana’izarsa da safiyar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025 a filin idi da ke Argungu misalin karfe 10:00 na safe.
Malamin ya rasu bayan doguwar jinya da ya yi, kuma mutane da dama sun bayyana kaduwarsu da addu’ar Allah ya gafarta masa da sanya shi cikin jinan Aljannah.
Iyalan Sheikh Giro sun yi ta'aziyya
Biyo bayan rasuwar malamin, iyalan marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu sun nuna alhini kan rashin.
Legit Hausa ta gano haka ne a wani sako da aka wallafa a shafin Facebook na marigayin a yammacin ranar Laraba.

Kara karanta wannan
2027: Yadda aka samu shugabanni 2 ko fiye a ADC da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya
Marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu ya kasance daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci na Najeriya da suka fito daga karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi.
An yi jimamin rasuwar Sheikh Kokoshe
Tun bayan bazuwar labarin rasuwar shugaban kngiyar, kafafen sada zumunta kamar Facebook sun cika da sakonnin ta’aziyya da addu’o’i.
Mutane da ya wa sun roka masa rahama amma addu’ar da tafi yawan bayyana ita ce:
“Allah ya gafarta musa ya sanya sa cikin Aljannar Firdausi, ya baiwa iyalansa da mabiya hakurin jure wannan babban rashi.”
A daya bangaren, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana rasuwar wani babban malami a jihar Gombe, Malam Saleh Isah.
Sheikh Pantami ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Laraba.
Shugaba a Izala ya rasu a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Shua'ibu A. Ahmad ya rasu a jihar Gombe.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun tabbatar da cewa malamin ya yi fama da doguwar jinya kafin ya rasu.
Shehin malamin ya kasance shugaban majalisar malamai a karkashin kungiyar Izala mai hedkwata a Jos a Jekadafari Kudu a Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng