Fulani Makiyaya Sun Kai Sabon Hari Benue, Sun Kashe Ɗan Sanda da Wasu Mutane 8
- Ana fargabar Fulani makiyaya sun kai hari a kan kauyukan Okwutanobe, Okpokpolo, Olegagbani da Ikpele da ke jihar Benue
- Shugaban karamar hukumar Agatu, Melvin Ejeh, ya ce makiyayan sun kashe mutane tara ciki har da wani jami'in dan sanda
- Melvin Ejeh ya yi zargin cewa makiyayan sun kai hare-haren ne matsayin ramuwar gayya biyo bayan sace masu shanu da aka yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Ana fargabar Fulani makiyaya sun kai sabon hari karamar hukumar Agatu ta jihar Benue, inda suka kashe mutane tara, ciki har da dan sanda.
An rahoto cewa makiyayan sun mamaye kauyukan Okwutanobe, Okpokpolo, Olegagbani da Ikpele, kuma sun ci gaba da farmakarsu a kai - a kai.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun farmaki kauyukan Benue
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Channels TV cewa maharan sun rika kai hari a kauyukan tun daga karshen makon jiya har zuwa ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya ce:
“Harin ya fara ne ranar Juma’a a kauyen Okwutanobe inda aka kashe mutane biyu. A ranar Asabar kuma sun kai hari kauyen Okpokpolo, inda suka kashe mutum daya.
“Ranar Litinin, makiyayan dauke da miyagun bindigogi sun kutsa kauyen Olegagbani, suka kashe mutum daya.
"Yau (Talata) kuma sun kai hari kauyen Ikpele, suka kashe jami’in dan sanda daya da wasu mutane hudu. Yanzu haka jama’a na tserewa daga gidajensu.”
Abin da ya sa makiyaya suka kai hari
Shugaban karamar hukumar Agatu, Melvin Ejeh, ya tabbatar da wannan hari na kwanaki uku da suka gabata.
Jaridar Punch ta rahoto Melvin Ejeh yana cewa:
“Tabbas an kashe mutane hudu a kauyukan Okwutanobe, Okpokpolo da Olegugbani, sannan a yau an kashe mutum biyar a kauyen Ikpele, ciki har da dan sanda daya.”
Ya kara da cewa:
“Muna Allah-wadai da wadannan hare-hare, kuma ina ganin harin na ramuwar gayya ne saboda zargin satar shanu da aka yi wa wasu Fulani a garuruwan Agatu.
“Muna rokon su da su ba gwamnati lokaci don gudanar da bincike maimakon daukar doka a hannunsu."

Source: Original
Abin da ke kawo tsaiko ga jami'an tsaro
Shugaban karamar hukumar ya yabawa jami’an tsaro bisa yadda suka mayar da martani da gaggawa, amma ya ce matsalar hanyoyi na hana su gudanar da aiki yadda ya kamata.
Melvin Ejeh ya ce:
“Ana sane da cewa hanyoyin Agatu ba su da kyau. Ko da jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa, yana daukarsu sama da awa hudu kafin su isa. A lokacin kuwa makiyayan sun kammala cin karensu ba babbaka sun tsere.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan Benue, Udeme Edet, bai tabbatar da harin ba a lokacin da ake hada wannan rahoto. Duk da haka, ya yi alkawarin zai yiwa manema labarai bayani idan ya samu cikakken rahoto.
Halin da mutane ke ciki a jihar Benue
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana damuwa kan matsalolin tsaro da ke kara tsananta a jihar Benue.
Ya ce wasu miyagu na ƙoƙarin korar jama'a daga garuruwansu domin su mamaye su, inda ya roƙi gwamnatin tarayya ta kai masu dauki.
Gwamnan Benue ya gargadi 'yan siyasa da ke amfani da rikicin, ya kuma ce duk wanda ya yi laifi dan ta’adda ne kuma za a tona asirinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


