Kebbi: Gwamna Ya Ƙirƙiro Sabuwar Masarauta, Ya Naɗa Sababbin Hakimai 2
- Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya raba masarautar Maiyama zuwa gida biyu tare da naɗa sababbin hakimai biyu
- Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Garba Dutsinmari ya ce an cire masarautar hakimin Sarandosa daga Maiyama
- A wata sanarwa da kwamishinan ya fitar, ya ce Gwamna ya amince da naɗin Dr. Faruk Maiyama a matsayin Sarkin Gabas Sarandosa kuma hakimi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamnatin Jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta amince da ƙirƙirar sabuwar masarautar Sarandosa a ƙaramar hukumar Maiyama
Gwamnatin Kebbi ta ce wannan dai wani ɓangare ne na sabon tsarin da ta ɗauko da nufin daidaita harkokin mulki da sarauta a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Garba Dutsinmari, ya sanya wa hannu.
Kwamishinan ya rabawa manema labarai wannan sanarwa a Birnin Kebbi ranar Laraba, 6 ga watan Agusta, 2025.
Gwamnan Kebbi ya ƙirƙiro sabuwar masarauta
A cewar sanarwar, Gwamna Nasir Idris ya amince da ciro masarautar Sarandosa daga ƙaramar hukumar Maiyama, wadda ke ƙarƙashin Sarkin Kudun Maiyama
Kwamishinan ya ƙara da cewa garin Sarandosa ne zai kasance fadar sabuwar masarautar da aka ƙirƙira a yankin Maiyama.
Yankin masarautar Sarandosa zai ƙunshi garuruwa guda biyar kamar haka: Gubba, Sarandosa, Acikaratu Ubandawaki, Acikaratun Dodo da kuma Tsalibi.
Dalilin raba yankin hakimin Maiyama gida 2
Garba Dutsinmari ya bayyana cewa ƙirƙirar masarautar ya zama dole ne sakamakon ci gaban yankin da kuma buƙatar inganta gudanarwar mulki da sarauta.
Ya ce duba da yadda yankin ke ci gaba, akwao buƙatar kawo sauyi ta hanyar raba alhakin shugabanci domin samun sauƙi na gudanarwa.
Gwamna Idris ya naɗa sababbin hakimai 2
Gwamnatin jihar Kebbi ta nada Dr. Faruk Maiyama a matsayin hakimin farko na sabuwar masarautar Sarandosa, tare da ba shi sarautar gargajiya ta Sarkin Gabas na Sarandosa.
Haka kuma, an sake naɗa Haliru Maiyama a matsayin sabon Hakimin Maiyama da aka sake fasalinta wa a yanzu, inda zai ci gaba da riƙe sarautar Sarkin Kudun Maiyama.

Source: Facebook
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa yankin masarautar Maiyama a yanzu za ta ƙunshi ƙauyuka guda bakwai, wato Dangaladıman Maiyama, Yarıman Maiyama, Giwatazo, Kurya, Rafintofa, Zara Birni, da kuma Idiga.
An naɗa sababbin hakimai 5 a jihar Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya naɗa sababbin hakimai shida da aka ƙirƙira a jihar.
Sakataren masarautar Katsina, Alhaji Belli Ifo ne ya bayyana waɗanda aƙa naɗa a matsayin hakimai a wata sanarwa da ya fitar ramar Asabar da ta shuɗe, 2 ga watan Agusta, 2025.
Ɗan mai girma gwamnan Katsina, Muhammad Dikko Umaru Raɗɗa da tsohon minista, Hadi Sirika na cikin waɗanda aka naɗa a matsayin sababbin hakimai a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

