Tashin Hankali: Gini Ya Rufta kan Uwa da Ƴaƴanta 5 a Katsina bayan Mamakon Ruwa
- Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun mutu sakamakon gini da ya rufta kansu suna tsakiyar bacci a garin Dankama da ke jihar Katsina
- An ce bangon gidan ya rufta kan mutane 10 a cikin gidan da misalin ƙarfe 2:00 na dare, bayan saukar mamakon ruwan sama
- Wannan na zuwa ne yayin da gidaje fiye da 50 da makarantu da wuraren ibada suka rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a Filato
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina – Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun mutu sakamakon ruftawar gini a Dankama da ke karamar hukumar Kaita, jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku da misalin ƙarfe 2:00 na dare a gidan wani mutum mai suna Muhammad Sani Garba.

Source: Twitter
Uwa da 'ya'ya 5 sun mutu a Katsina
Mutanen da abin ya rutsa da su sun rasu ne suna tsakiyar barci, bayan bangon gidan ya fado a kansu sakamakon mamakon ruwan sama, inji rahoton Leadership.
An garzaya da wasu mutane huɗu daga cikin 'yan gidan da suka tsira daga iftila'in zuwa asibiti don samun kulawar gaggawa.
Da yake magana da manema labarai, mai gidan, Muhammad Sani, ya ce yana waje ne lokacin da lamarin ya faru.
A cewarsa:
“Wannan iftila'in ya afkawa mutane 10 ne, amma mutum shi ne kawai suka mutu. Yanzu haka huɗu na asibiti suna jinya.”
Mahaifin yaran ya kadu da iftila'in
An rahoto cewa waɗanda suka rasu sun haɗa da Mariya Sani mai shekaru 45 (uwar), Mujahid Sani mai shekara 20, Zahariya Sani mai shekara 18, Hauwa Sani mai shekara 15, Amira Sani da Nura Sani mai shekara 5.
Wannan mummunan lamari ya tayar da hankula a cikin danginsu da al’ummar gari, inda mutane ke tururuwa zuwa gidan da abin ya faru domin yi musu ta’aziyya.
Duk da wannan babban rashi, Muhammad Sani ya bayyana godiyarsa ga Allah tare da yi wa matarsa da ’ya’yansa addu’a.
Jaridar Daily Trust ta rahoto magidancin ya ce:
“Ina kallon wannan a matsayin ƙaddara daga Allah. Ina rokon Allah ya jikansu, ya sa sun huta.”
Da take tabbatar da faruwar lamarin, shugabar SEMA a jihar Katsina, Hajiya Binta Dangani, ta ce ma’aikatan hukumar sun isa wurin da lamarin ya faru domin duba halin da ake ciki.

Source: Original
Gidaje 50 sun rushe a Filato
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan fiye da gidaje 50, makarantu da wuraren ibada sun rushe sakamakon ruwan sama mai karfi a yankin Menkaat na gundumar Shimankar, karamar hukumar Shendam, jihar Filato.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ruwan saman ya haifar da lalacewar turakun wutar lantarki kan wasu gidaje, wanda ya jawo mummunan hadari, kamar yadda muka ruwaito.
Mazawaje Daniel Danjuma, kansila mai wakiltar gundumar Shimankar, ya shaida cewa gonaki da dama, musamman na shinkafa, sun lalace sakamakon ambaliyar.
Ruwan da ya wuce kima zai sauka a Arewa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama da ya wuce kima zai sauka a jihohin Sokoto, Zamfara da wasu 8 a watan Agusta, 2025.
NiMet ta ce akwai yiwuwar jihohin Kudu maso Yamma su fuskanci fari a Agusta yayin da ruwa zai yi karanci a jihohin Arewa ta Tsakiya.
Hukumar ta shawarci jama’a da hukumomi da su shirya don tunkarar ambaliya, cututtuka da sauran abubuwan da ruwan Agusta zai zo da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


