Tinubu: Gwamnati Ta Kashe N26.38bn a kan Jiragen Shugaban Ƙasa a cikin Watanni 18
- An samu rahoto a kan yawan kudin da gwamantin Bola Ahmed Tinubu ta kashe a kan jiragen sama a watanni 18 kawai
- A tsakanin 2023 da 2024, gwamnatin tarayya ta kashe sama da Naira biliyan 26 domin tabbatar da jiragen suna lafiya lau
- Gwamnatin tarayya ta rika fitar da wannan kudi a rukuni rukuni, yayin da rundunar sojin sama ta Najeriya ke kula da su
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta kashe kimanin Naira biliyan 26.38 wajen kula da jiragen fasinjojin shugaban ƙasa a cikin watanni 18 na farko na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wani rahoto ya nuna cewa an fitar da kudin ne tsakanin watan Yuli 2023 zuwa Disamba 2024, domin tafiyar da jiragen da kuma kulawa da su.

Asali: Facebook
Punch News ta ruwaito cewa bincike ya nuna cewa daga shekarar 2016 zuwa 2022, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ware N81.80bn domin kula da jiragen shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin da gwamnati ta kashe a zamanin Buhari
The Cable ta bayyana cewa daga cikin wannan adadi, an kashe N62.47bn a kan gudanar da harkokin jiragen da gyaransu, yayin da N17.29bn suka tafi a kan tafiye-tafiyen cikin gida da na waje.
An kuma ware N2.04bn don wasu ƙarin al’amuran da suka shafi tafiyar da jiragen, a yayin da fadar shugaban ƙasa ta ke riƙe jirage 10 tun daga lokacin da Buhari ya hau mulki a watan Mayun 2015.
Wasu masana a bangaren sufurin jiragen sama sun danganta yawan kuɗin da ake kashewa da raunin darajar Naira saboda duk wasu hidimomi da suka shafi jiragen ana biyan su da dala.
Wasu kuma na ganin cewa yawan jiragen da fadar shugaban ƙasa ke sarrafawa na daga cikin dalilan da ke sa yawan kuɗin da ake fitarwa don kula da su ke ƙaruwa.
Yadda aka fitar da kudin a gwamnatin Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa an fitar da kuɗin da aka kashe a gwamantin Tinubu ne kashi-kashi, inda yawan kuɗin da aka fitar ya fi yawa a tsakanin Afrilu zuwa Agusta na shekarar 2024.
A ranar 14 ga Yuli, 2023, gwamnati ta biya N846.03m a matsayin wasu kudi da su ka shafi fitar da jiragen shugaban kasa zuwa kasashen waje.
Kwana biyu bayan haka, an sake fitar da N674.82m, wanda ke nufin a watan kaɗai, jiragen sun lashe sama da N1.5bn.
A ranar 16 ga Agusta, 2023, an sake fitar da N2bn, tare da wasu ƙarin kuɗai da suka haɗa da N387.6m da N713.22m da aka fitar a farkon watan.

Asali: Facebook
A cikin watan Maris na shekarar 2024, an fitar da N1.27bn sau biyu a ranakun 7 da 9 fa watan a bara.
Daga nan sai aka fitar da N5.08bn a ranar 23 ga Afrilu, wannan shi ne mafi yawan adadi da aka fitar a cikin wata guda a wannan lokacin da aka duba.
A ranar 8 da 11 ga Mayu, an fitar da N2.43bn da N1.27bn, sannan aka sake fitar da N1.27bn a ranar 25 ga watan.
Jiragen shugaban ƙasa, wanda rundunar sojin sama ta Najeriya ke kula da su, su ne ke daukar nauyin jigilar shugaban ƙasa, mataimakinsa da kuma manyan jami’an gwamnati zuwa sassan Najeriya da duniya.
APC ta yabi aikin gwamnatin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kano sun sake jaddada mubaya’arsu ga tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Haka kuma sun nanata goyon bayansu ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da yabon aikin da su ka ce gwamnati na shimfida wa a Arewacin Najeriya, musamman Kano.
A cewar mahalarta taron, jam’iyyar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a da jan hankalin magoya baya don tabbatar da nasara ga APC a zaɓuka masu zuwa nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng