Belin Dilan Ƙwaya: Kwamishinan Abba a Jihar Kano Ya Yi Murabus
- Kwamishinan sufuri na Kano, Ibrahim Namadi, ya miƙa takardar ajiye aiki daga mukaminsa ga gwamnatin jihar
- Wannan na zuwa bayan an gudanar da bincike kan rawar da ya taka a belina dilan ƙwaya, Suleiman Danwawu
- Duk da haka, Ibrahim Namadi ya kafe a kan cewa bai aikata laifin komai ba a kan zargin da aka yi masa wajen belin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya yi murabus daga mukaminsa.
Ya ajiye aiki sa’o’i kadan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin beli da dilan ƙwaya, Sulaiman Aminu Danwawu.

Asali: Facebook
Darakta Janar kan yaɗa labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan sufuri ya yi murabus a Kano
Sanarwar ta ce murabus ɗin Kwamishinan wani muhimmin mataki ne da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen bin gaskiya, bayyana ta da kuma mulki da adalci.
Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan ya yanke shawarar murabus ne duba da nauyin lamarin da kuma kwantar wa da jama’a hankali.

Asali: Facebook
A cewar Kwamishinan:
“A matsayina na jigo a gwamnati da ke fafutukar dakile safara da shan miyagun ƙwayoyi, dole ne in ɗauki wannan mataki, duk da tsaurinsa.”
“Ko da yake ina mai tabbatar da cewa ba ni da laifi, ba zan iya watsi da yadda jama’a ke kallon lamarin ba, da kuma bukatar kare ƙimar gwamnatinmu."
Ibrahim Namadi ya gode wa Gwamnan Kano
Alhaji Namadi ya bayyana godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa jihar hidima.
Ya ƙara da tabbatar da biyayyarsa ga manufofin kyakkyawan shugabanci da rikon amana.
Ya ce:
“A matsayina na ɗan ƙasa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da muka share shekaru muna ƙoƙarin shimfiɗawa a jiharmu. Ina nan daram kan akidar da ta samar da wannan gwamnati.”
A bangarensa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin tare da fatan alheri ga tsohon kwamishinan.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ba wajen tabbatar da adalci, da’a, da yaki da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran munanan dabi’u.
Gwamnan ya kuma ja kunnen sauran masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu taka-tsantsan kan duk wani batu da ya shafi jama’a.
An zargi Kwamishina a Kano da cin hanci
A baya, kun samu labarin cewa Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, yana fuskantar zarge-zarge masu nauyi bayan rahoton DSS.
Rahoton ya yi zargin cewa ya karɓi cin hanci daga hannun wani sanannen dillalin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu a jihar.
A cewar majiyoyi daga hedikwatar DSS da ke Abuja, hukumar ta gudanar da bincike a asirce kan Namadi kuma an gano ya karɓi cin hanci $30,000.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng