Wani Rikicin Ya Barke a Filato, an Rasa Rai bayan Kona Tarin Gidaje

Wani Rikicin Ya Barke a Filato, an Rasa Rai bayan Kona Tarin Gidaje

  • Wata mata ta rasa rayuwarta a rikicin da ya faru tsakanin makiyaya da mazauna garuruwan Rwan da Kopmon a Bokkos
  • An kona gidaje da dama yayin da dakarun sojoji da jami’an tsaro suka kai dauki domin daidaita lamarin
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumomi na ci gaba da bincike da sa ido don hana rikicin ya kara bazuwa a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Wata mata ta rasa rayuwarta kuma an kona gidaje da dama sakamakon rikicin da ya ɓarke a jihar Filato.

Rahoto ya nuna cewa rikicin ya barke ne tsakanin wasu makiyaya da mazauna garuruwan Rwan da Kopmon da ke gundumar Mushere a ƙaramar hukumar Bokkos, jihar Filato.

An rasa rai yayin da aka gwabza fada a Filato
An rasa rai yayin da aka gwabza fada a Filato. Hoto: Legit
Source: Original

Legit ta tattaro bayanai kan barnar da aka yi a lokacin rikicin ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Bayan saukar ruwan sama, ambaliya ta cinye gidaje da gonaki a jihohin Arewa 3

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Agusta, 2025 kuma shugaban matasan yankin ne ya sanar da hukumomi da misalin karfe 8:10 na safe.

Har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin rikicin ba, amma an ce tashin hankali ne ya rikide zuwa rikicin da ya jawo asarar rai da kuma lalata dukiyoyi.

Sojoji sun shiga tsakani don daidaita al'amura

Yayin da hukumomi suka samu rahoton faruwar lamarin, rundunar sojoji tare da wasu jami’an hadin guiwa sun garzaya zuwa yankin domin kwantar da tarzoma.

Wata majiya daga cikin jami’an tsaron ta shaida cewa an shawo kan lamarin, amma suna ci gaba da sa ido a yankin domin hana sake barkewar wani sabon rikici.

An bayyana cewa jami’an tsaron na gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a kisan matar da kuma lalata dukiyar jama’a.

Rikicin jihar Filato na ci gaba da barazana

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun harbe 'dan limamin Abuja, ya mutu har lahira

Filato na daga cikin jihohin da ke fama da rikice-rikicen kabilanci da addini a Najeriya, musamman tsakanin makiyaya da manoma ko mazauna ƙauyuka.

A ‘yan watannin nan, an samu karin yawaitar hare-hare da asarar rayuka a sassan jihar, lamarin da ke jefa al’ummomi cikin fargaba da tsoro.

Gwamnatin jihar Filato ta sha alwashin magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin al’ummomi.

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang. Hoto: Plateau State Government
Source: Twitter

Kiran zaman lafiya da hadin kai a Filato

Yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike da sa ido, an yi kira ga dukkan ɓangarori da su zauna lafiya tare da gujewa daukar doka a hannunsu.

An kuma bukaci gwamnati da ta kara sa kaimi wajen warware rigingimun ƙabilanci da rikice-rikicen da suka dade suna ci wa jihar tuwo a kwarya.

A halin yanzu, ana sa ran gwamnati da hukumomin tsaro za su ƙara kaimi wajen tabbatar da adalci da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin Bokkos da kewaye.

'Yan daba sun kai wa matashi hari a Kano

Kara karanta wannan

Babu dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata yayin wani hari a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan daba sun kai hari ga wani matashi mai suna Sadiq Gentle cikin dare.

Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya samu raunuka da dama kuma a yanzu haka yana kwance a asibiti.

Bayan kwantar da shi, mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ziyarci asibitin Murtala domin duba halin da matashin ke ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng