Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Kwamitin Binciken Zargin Kwamishina da Belin Dilan ƙwaya
- Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton bincike kan zargin Alhaji Ibrahim Namadi, kwamishinan sufuri, da taimakawa dillalin ƙwaya
- Hukumar yaƙi da shan miyagun kwayoyi ta NDLEA na shari'a da Sulaiman Danwawu da ake zargin kasurgurmin dilan ƙwaya ne
- Wannan ya jawo gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin da zai bibiyi lamarin domin zargin kwamkshinansa da belin Danwawu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa don tantance zargin da ake yi wa kwamishinan harkokin sufuri na jihar, Ibrahim Namadi.
Ana zargin Alhaji Ibrahim da taimakawa wajen samun beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a sanarwar da Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamiti ya miƙa rahoto ga gwamnatin Kano
Shugaban kwamitin kuma mai ba gwamna shawara kan shari’a da harkokin kundin tsarin mulki, Barrister Aminu Hussain ne ya miƙa rahoton.
Ya shaida wa Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, cewa kwamitin ya gudanar da cikakken bincike bisa gaskiya da kwararan hujjoji.
Ya ce:
“Mun gana da kwamishinan da ake zargi, wanda shi ma ya rubuta bayaninsa. Baya ga haka, mun tattauna da wasu muhimman mutane da ke da alaƙa da lamarin, ciki har da Abubakar Umar Sharada, mai ba da shawara ta musamman kan faɗaɗa siyasa, da kuma Musa Ado Tsamiya, mai ba da shawara kan magudanan ruwa."
Yadda kwamitin gwamnatin Kano ya yi aikinsa
Ya ƙara da cewa kwamitin ya tuntubi hukumomin tsaro da na shari’a da suka haɗa da Hukumar DSS, NDLEA da kuma ƙungiyar lauyoyi ta NBA, domin tabbatar da sahihancin binciken.

Kara karanta wannan
Dilan ƙwaya: Bayanai sun bulloƙo kan kwamishinan Kano, ana zargin ya karbi $30,000

Source: Facebook
Ya ce:
“Mun nazarci takardun da kotu ta tabbatar da ingancinsu tare da nazarin doka. Mun gudanar da wannan aiki da kwarewa, bin ƙa’ida da gaskiya."
Barrister Hussain ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kin tsoma baki a aikin kwamitin, yana mai cewa hakan ya nuna shugabanci nagari da mutunta doka.
Ya ce:
“Muna gode wa Mai Girma Gwamna bisa barin kwamitin ya yi aikinsa cikin ‘yanci da kwanciyar hankali.
Ya ce:
"Wannan ya ba mu damar gudanar da bincike ba tare da wani tsoro ko son zuciya ba."
Da yake karɓar rahoton a madadin gwamnatin jihar, Alhaji Farouk Ibrahim ya nuna godiya ga kwamitin bisa jajircewa da kwarewa.
Ya kuma yaba da yadda kwamitin ya tsaya tsayin daka duk da matsin lamba daga jama’a.
Kano: Ana zargin kwamishina da cin hanci
A baya, mun wallafa cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana sababbin bayanai a kan kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi.
Ta ce ya karɓi cin hanci na $30,000 daga hannun sanannen dillalin miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu, domin taimaka masa samun beli.
Majiyoyi daga cikin DSS sun ce an biya Namadi kudin ne kafin ya amince da zama mai karɓar belin Danwawu, wanda aka dade ana nema ruwa a jallo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

