Tsofaffin Sojojin Najeriya Sun Fara Zanga Zanga, Sun Mamaye Ofishin Ministan Kuɗi

Tsofaffin Sojojin Najeriya Sun Fara Zanga Zanga, Sun Mamaye Ofishin Ministan Kuɗi

  • Tsofaffin sojoji sun mamaye hedikwatar ma’aikatar kudi a Abuja domin neman hakkokinsu da suka hada da alawus da inshora
  • Wadannan tsoaffin sun ce an dakatar da albashinsu, an zabtare giratutinsu, kuma an hana su inshora tun bayan ajiye aikinsu
  • Shugabanninsu sun ce ba za su bar wajen ba sai an biya bukatunsu gaba daya, yayin da rundunar sojoji ta ki yin martani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wasu tsofaffin sojoji da suka bar aiki a kashin kansu sun rufe kofar shiga hedikwatar ma’aikatar kudi ta kasa a ranar Litinin a wani mataki na zanga zanga.

Zanga-zangar, wacce aka fara da misalin karfe 10:15 na safe, ta jawo zuwan jami’an tsaro da dama daga rundunar soji, ‘yan sanda da DSS domin hana rikici da karya dokoki.

Kara karanta wannan

Babu dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata yayin wani hari a Zamfara

Tsofaffin sojoji da suka ajiye aiki sun mamaye ofishin ministan Kudi a Abuja
Yadda sojojin da suka ajiye aiki suka mamaye hedikwatar ma'aikatar kudi a Abuja. Hoto: @DejiAdesogan/X
Source: UGC

Tsofaffin sojoji sun rufe ma'aikatar kudi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsofaffin jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda da ta soji sun yi zanga-zanga a Abuja fiye da sau uku cikin watanni bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kwanakin da suka gabata, wasu tsofaffin ‘yan sanda suka mamaye hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Abuja domin nuna rashin jin dadinsu kan tsarin fansho na CPS.

A yau din, daya daga cikin shugabannin masu zanga-zangar, Staff Sergeant Simon Ipwu, ya ce sun mamaye ma'aikatar kudi ne kan rashin biyan su kudin alawus din SDA da inshorar lafiya.

Sauran korafe-korafensu sun hada da zabtare musu kudin giratuti da kuma hanasu albashin watanni hudu bayan sun ajiye aiki.

Dalilin zanga zangar tsofaffin sojoji

SS Simon Ipwu ya yi alkawarin cewa ba za su bar kofar ma’aikatar kudin ba har sai an cika bukatunsu baki daya, a cewar rahoton Vanguard.

A cewar tsohon sojan:

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina, an dakile hare hare 2

“Muna nan mun kasa mun tsare saboda neman hakkokinmu da aka rike. Mun rubuta neman barin aiki saboda irin rikon sakainar kashin da ake yi mana. Akwai makirci sosai a lamarin.
“Sun nuna mana a fili ba su ji dadin ajiye aikinmu ba, wannan ya sa suka dakatar da albashinmu na watanni hudu. Bayan haka kuma suka ce za mu samu giratuti amma har yanzu ba su biya ba.
“Mun aika wasiku zuwa wurare daban-daban ciki har da rundunar soji, ma’aikatar tsaro, kudi, DSS, ‘yan sanda da sauran hukumomi. Mun jira tsawon mako biyu, amma har yanzu ba su mayar mana da martani ba."
Tsofaffin sojoji na zargin an rike masu albashin wata 4, an hana su alawus da giratuti da kuma inshora
Tsofaffin sojoji sun tare kofar shiga hedikwatar kudi da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: @DejiAdesogan
Source: Twitter

Rundunar sojoji ba ta ce komai ba

Tsohon sojan ya kara da cewa:

“A yanzu haka, ba a biya mu kudin alawus na tsaro ba, watau SDA, an kuma rage kudin giratuti dinmu, an hana mu albashin watanni hudu da suka wuce, kuma ba a biya kudin inshorar mu ba.”

An yi kokarin tuntubar mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Laftanal Kanal Appolonia Anele, ta wayar salula amma ba ta dauka ba.

Haka kuma, ba ta mayar da martani ba kan sakon da aka tura mata har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Yaƙi da ƴan ta'adda: Gwamnatin tarayya za ta ɗauki matasa 13000 aikin sojan ƙasa

Ma'aikata sun rufe ofishin ministan kudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma'aikatan hukumar nukiliya sun rufe ofishin ministan kudi saboda rashin biyan alawus da bashin albashin wata biyu.

Ma'aikatan sun zargi ministan kudi, Wale Edun da hana su hakkokinsu duk da roƙo da suka yi, inda suka bayyana cewa sun gaji da yin haƙuri.

Sun ce gwamnati na karɓar duk kuɗin da hukumar ke samu maimakon barin wani kaso, lamarin da ya hana su samun albashin watannin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com