Talaka Bawan Allah: ADC Ta Fusata da Tinubu Zai Kashe N712bn a Gyaran Filin Jirgin Legas

Talaka Bawan Allah: ADC Ta Fusata da Tinubu Zai Kashe N712bn a Gyaran Filin Jirgin Legas

  • Jam’iyyar ADC ta bayyana shirin kashe N712bn wajen gyaran filin jirgin Legas a matsayin almubazzaranci da rashin tausayi
  • Bolaji Abdullahi da ke magana da yawun ADC ya ce babu tabbacin cewa majalisar dokoki ta amince da kashe makudan kuɗin
  • Kakakin ADC ya ce a baya, an kashe irin kuɗin da ake shirin narkawa a gyaran wani sashe na filin jirgi a gina sababbi guda huɗu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Jam’iyyar adawa ta ADC ta soki shirin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na sake gyaran filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

A makon da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da kashe Naira biliyan 712 domin aikin.

Kara karanta wannan

Yadda aka samu kusan Naira tiriliyan 1 da za a gyara filin jirgin saman Legas

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
ADC ta caccaki Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa za a kashe kuɗin wajen samar da na'urar CCTV da sauran abubuwa a filin jirgin saman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun jam’iyyar ADC ta ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa har yanzu ba a bayyana ko an samu amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa kafin fara wannan aiki mai tsada ba.

Jam'iyyar ADC ta soki gwammatin Bola Tinubu

Daily Post ta wallafa cewa ADC ta ce aikin ya yi tsada fiye da kima, inda ta kira shi da alamar ɓarnatar kuɗin talakawa.

Jam’iyyar ta ce wannan lamari na ƙara tabbatar da yadda gwamnatin APC ta rabu ƴan kasa a cikin yunwa da ƙunci.

Jam'iyyar ADC ta fusata
ADC ta ce gyara sashen tashar jirgin a kan N712bn almubazzaranci ne Hoto: ADC Coalition 2027
Source: Twitter

ADC ta ce:

"Abin mamaki ne yadda za a kashe Naira biliyan 712 wajen gyaran filin jirgi, alhali wasu cibiyoyin ilimi da lafiyar jama’a na cikin mawuyacin hali. Yaya hakan zai yi ma’ana a ƙasar da jama'arta ke cikin yunwa kuma miliyoyin mutane sun faɗa cikin talauci saboda manufofin da gwamnati ta samar?"

Kara karanta wannan

Amnesty Int'l ta dura kan Tinubu da gwamnati ta ƙi tsoma baki shekaru 6 da 'sace' Dadiyata

ADC ta fusata da shirin gyaran filin jirgin

Jam’iyyar ADC ta ce adadin kuɗin da za a kashe, wanda ya kai dala miliyan 500, ya yi daidai da kuɗin da aka yi amfani da shi wajen gyara filayen jiragen sama guda huɗu.

An yi gyaran filin jiragen a Abuja, Legas, Kano da Fatakwal a shekarar 2014 da kuɗin da aka aro daga China, kuma har yanzu ana biyan bashin.

Jam’iyyar ADC ta ce tana mamakin ko filin jirgin Legas da aka gyara a kwanan ne za a sake gyarawa da wannan kudi mai yawa, ko kuwa wani sabo ne da ba a bayyana wa jama’a ba.

Kiran ADC ga tsohon Gwamnan Kaduna

A baya, kun ji jam’iyyar haɗakar adawa ta ADC reshen jihar Kaduna ta buƙaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, da ya sauya sheka, ya bar SDP.

Tsohon mataimakin shugaban APC, shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman da ya koma ADC ne ya yi kiran a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025.

Lukman ya ce lokaci ya yi da duk masu kishin ƙasar nan su haɗa ƙarfi da ƙarfi domin ganin bayan mulkin jam’iyyar APC bayan zaben 2027 mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng