Bayan Saukar Ruwan Sama, Ambaliya Ta Cinye Gidaje da Gonaki a Jihohin Arewa 3
- Mamakon ruwan sama ya jawo rushewar gidaje da cinye gonaki a jihohin Bauchi, Filato da Neja wanda ya tilastawa mutane yin kaura
- A Filato, sama da gidaje 50 da makarantu da majami’a sun rushe yayin da guguwar ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun wuta
- A Bauchi da Neja, ambaliya ta cinye gonaki da dama, inda hukumar SEMA ta sanar da shirin fara kai tallafi ga wadanda abin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka a jihohin Filato, Bauchi da Neja a ranar Lahadi ya jefa mutane cikin cikin mawuyacin hali.
An rahoto cewa mamakon ruwan saman da ya jawo ambaliyar ruwa ya haddasa rushewar gidaje, lalata gonaki a wadannan jihohi uku.

Asali: Getty Images
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutane da dama a jihohin sun rasa muhallansu yayin da suka kuma rasa hanyar daukar dawainiyar rayuwarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da ambaliya ta shafa a Arewa
1. Filato
A yankin Menkaat da ke cikin gundumar Shimankar, karamar hukumar Shendam, jihar Filato, ambaliya ta rusa gine-gine 50, ciki har da gidaje, makarantu da wuraren ibada.
Shaidu sun bayyana cewa guguwar da ta biyo bayan ruwan sama da sassafe, ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun lantarki kuma ta kwashe rufin gidaje, wanda ya sa mutane suka rasa matsugunnansu.
Mazawaje Daniel Danjuma, kansilan gundumar Shimankar, ya tabbatar da irin barnar da aka yi, ya bayyana cewa ambaliyar ta cinye gonakin shinkafa.
“Gidaje da dama sun rushe, kuma gonakin ma sun lalace. Mutane sun yi asarar da ba za a misalta ba,” inji Danjuma.
Wani mazaunin yankin, Lawrence Longwalk, ya roki gwamnatin jihar da ta kawo dauki cikin gaggawa, yana mai cewa ambaliyar ta rushe makarantu biyu da wata majami’a.
2. Bauchi
A jihar Bauchi kuwa, guguwar da ta auku a karamar hukumar Dass ta lalata gidajen mutane fiye da 40, tare da cinye gonaki da dama, a cewar rahoton BBC Hausa.
Adamu Nayola, darakta a hukumar SEMA ta jihar Bauchi, ya ce ba a samu asarar rayuka ba, amma mata da yara da yawa na bukatar agajin jin kai cikin gaggawa.
Ya dora laifin ambaliyar akan wata madatsar ruwa da aka gina ba bisa ƙa'ida ba, wadda ya ce ta rushe bayan gaza rike ruwan sama mai yawa da ya zuba cikinta.
“Hukumar SEMA ta fara tantance barnar da ambaliyar ta yi kuma za ta fara raba kayan agaji nan ba da jimawa ba,” inji Nayola.

Asali: Original
3. Neja
A jihar Neja, ruwan sama da safiyar Lahadi ya haddasa ambaliya a kauyuka da dama a yankin Kafin Koro na karamar hukumar Paikoro, da kuma kauyuka 18 a Lapai.
Wasu daga cikin kauyukan da abin ya shafa sun hada da Dere, Eshi, Apataku, Tsakanabi, Kuchi Kakanda, da Muye, inda gonaki suka nutse cikin ruwa.
A wata sanarwa, Jonathan Vatsa, mai bai wa gwamna shawara kan hulda da jama’a da yada labarai, ya bukaci al’ummomin da ke bakin koguna su sauya matsuguni.
“Mun san cewa akwai ciwo a ce mutane su bar garuruwansu, amma dole ne kowa ya kaura daga yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya har sai ruwan sama ya lafa,” inji Vatsa.
NiMet ta bayyana cewa kananan hukumomi 15 daga cikin 25 na jihar Neja na cikin hadarin ambaliya a kakar daminar bana.
Ana fargabar ambaliya a jihohi 3
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohin Taraba, Adamawa da kuma Bauchi.
A cewar hukumar hasashen yanayin, mamakon ruwan sama da za a shafe kwanaki uku ana yi daga Litinin zuwa Laraba ne zai haddasa wannan ambaliya.
Ba iya jihohin Arewa abin ya shafa ba, NiMet ta ce jihohin Oyo, Ogun, Edo, Delta da Bayelsa da ke a Kudancin kasar za su iya fuskantar ambaliyar ruwan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng