Akwai Matsala: Adamawa da Jihohi 7 Za Su Fuskanci Ambaliya daga Litinin zuwa Laraba

Akwai Matsala: Adamawa da Jihohi 7 Za Su Fuskanci Ambaliya daga Litinin zuwa Laraba

  • Hukumar NiMet ta fitar da sabon hasashen yanayi na kwanaki uku tare da gargadin yiyuwar ambaliya a Adamawa da wasu jihohi
  • Daga ranar Litinin zuwa Laraba, za a samu mamakon ruwan sama a sassa da dama na Arewa da Kudancin kasar nan, a cewar NiMet
  • NiMet ta ja kunnen jama’a da su guji tuki yayin da ake ruwan sama mai karfi tare da bibiyar hasashen yanayi domin kare kai da dukiyoyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamar yadda ta saba, hukumar NiMet ta fitar da rahoton hasashen yanayi na Najeriya, wanda ya shafi ranakun Litinin zuwa Laraba.

A sabon rahoton, NiMet ya ce za a samu ruwan sama a sassa daban-daban na kasar tare da yiwuwar ambaliya a wasu yankuna.

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai yawa daga Litinin zuwa Laraba wanda zai iya jawo ambaliya
Wani gari ya gamu da ambaliyar ruwa, jami'ai na kokarin ceto wadanda suka makale. Hoto: Sani Hamza/Staff
Asali: Original

Hasashen yanayi na kwanaki uku da NiMet ta fitar na kunshe ne a cikin sanarwar da ta rabawa manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Hankula sun tashi da yara 8 suka mutu a hadari bayan nutsewa a kogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi na ranar Litinin

NiMet ta ce za a samu hadari da ruwan sama da safe a yankunan babban birnin tarayya, da jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Jigawa, Kano da Katsina, Benue, Neja, Kogi da Nasarawa.

Rahoton hukumar ya ce:

“Daga bisani da yamma ko daren ranar ta Litinin, za a sake samun hadari tare da ruwan sama a Arewa maso yamma da Kudu da kuma sassan Nasarawa, Kwara, Kogi, Filato, Neja da Benue.
“Akwai yiyuwar ambaliya a wasu yankunan Adamawa, Taraba da Bauchi."

A kudancin kasar, ana hasashen ruwan sama zai sauka a wasu sassan Ebonyi, Enugu, Imo, Anambra, Abia, Ogun, Edo, Delta, Legas, Ribas, Cross River, Akwa Ibom da Bayelsa da safe.

A cewar NiMet, za a ci gaba da samun ruwan sama har zuwa dare a sassan Abia, Imo, Ebonyi, Anambra, Osun, Ogun, Oyo, Ondo, Ekiti, Edo, Delta, Bayelsa, Ribas, Legas, Cross River da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Ruwan sama da iska mai karfi zai jawo ambaliya a Taraba da jihohi 7 ranar Lahadi

Hukumar ta kara da cewa akwai yiyuwar ambaliya a yankunan Oyo, Ogun, Edo da Delta a wannan ranar.

Hasashen yanayi na ranar Talata

A ranar Talata, NiMet ta hango hadari da ruwan sama da safe a Arewacin kasar musamman a yankunan Taraba, Katsina, Kebbi, Sokoto, Kaduna da Zamfara.

A Arewa ta tsakiya ma, ana sa ran ruwan sama a birnin tarayya Abuja da kuma jihohin Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Filato da Benue.

A Kudu, an hango hadari tare da yiwuwar ruwan sama a Ebonyi, Imo, Abia, Enugu, Anambra, Ondo, Ekiti, Ogun, Osun, Oyo, Legas, Edo, Delta, Ribas, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom.

Hukumar NiMet ta ce za a sha ruwan sama na kwanaki 3 a jere a wasu jihohin Najeriya
Mamakon ruwan sama na sauka yayin da iska mai karfi ke kada rassan itatuwa. Hoto: Sani Hamza/Staff
Asali: Original

Hasashen yanayi na ranar Laraba

Jaridar Punch ta rahoto cewa a ranar Laraba, hukumar ta hango hadari da ruwan sama da safe a wasu sassan Abuja, Taraba, Nasarawa, Neja da Kaduna

NiMet ta kuma hango hadari da ruwan sama da yamma a yankunan Abuja, Borno, Bauchi, Taraba, Kaduna, Gombe, Yobe, Jigawa, Kano, Adamawa, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Filato da Benue.

Kara karanta wannan

Hako fetur a Arewa: Kamfanin NNPCL ya tono rijiyoyin mai 4 a Kolmani

Sanarwar ta ce:

“A Kudancin kasar, za a samu hadari da ruwan sama a Ebonyi, Abia, Imo, Enugu, Anambra, Legas, Edo, Ribas, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta da Cross River da safe."

Ta ce daga bisani za a samu ruwan sama a dukkanin yankin Kudu, tare da yiyuwar ambaliya a wasu sassan Bayelsa.

NiMet ta gargadi 'yan Najeriya

NiMet ta gargadi jama’a da su guji tuki yayin ruwa mai karfi, yayin da ta nemi mazauna yankunan da ake zargin za a samu ambaliya su gaggauta kaura.

“Ku tabbata kun kashe duk wasu na'urorin wutar lantarki, ku nisanci manyan itatuwa don gujewa faduwar rassan itace ko shi kansa iccen.
“Kamfanonin jiragen sama su rika neman rahotannin yanayi daga NiMet domin tsara tafiye-tafiyensu yadda ya kamata."

- Hukumar NiMet.

Hukumar ta shawarci jama’a da su rika bibiyar shafinta na intanet www.nimet.gov.ng don samun sababbin bayanai kan yanayi.

Ambaliya ta rusa gidaje a jihar Borno

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ruwan sama mai karfi ya haddasa ambaliya a Maiduguri, inda mazauna wuraren da abin ya shafa suka fara hijira.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da afkuwar ambaliya a Bulumkutu da Gomari, har ta kai an tura jami’ai don ceto mutane kuma a hana sata.

Wannan ambaliya ta biyo bayan ruwan sama na tsawon sa’o’i uku, wanda ya jawo rushewar gine-gine takwas, a cewar rundunar 'yan sandan jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com