'An Yaudare Su,' Wasu Tsofaffin 'Yan Majalisar Arewa na Adawa da Tazarcen Tinubu
- Tsofafin 'yan majalisar tarayya daga Arewa sun rabu biyu kan goyon bayan tazarcen Shuba Bola Tinubu a 2027 bayan taron kungiyar NCF
- A taron NCF, Femi Gbajabiamila ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ya fi dacewa ya ci gaba da shugabancin Najeriya bayan 2027
- Sai dai, wasu tsofaffin 'yan majalisar Arewa sun nesanta kansu da taron NCF, inda suka ce su Gbajabiamila ba sa wakiltar ra'ayin Arewa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsoffin 'yan majalisar tarayya daga Arewacin Najeriya sun rabu gida biyu dangane da kudirin shugaban kasa Bola Tinubu na sake tsayawa takara a 2027
An samu rarrabuwar kawunan ne bayan wata sanarwar goyon baya da kungiyar Northern Caucus Forum (NCF) ta ‘yan majalisar tarayya ta tara ta fitar.

Source: Twitter
A sanarwa da suka fitar bayan zaman tattaunawa, NCF ta bayyana Tinubu a matsayin jagoran kasa wanda ke da kudurin ci gaban kowane yanki a Najeriya, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar NCF ta amince da tazarcen Tinubu
Legit Hausa ta rahoto cewa zaman tattaunawar wani bangare ne na yunkurin tuntubar al’umma da NC ke yi a fadin kasa domin tallafa wa kudirin shugaban kasa Tinubu na neman wa’adi na biyu a 2027.
A wajen taron, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa kuma tsohon shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya nemi hadin kan tsofaffin 'yan majalisar.
Gbajabiamila ya bukaci NCF ta mara wa gwamnatin Tinubu baya da kuma kudirinsa na tazarce, yana mai cewa Tinubu ne zabin da ya fi dacewa don jagorantar Najeriya a 2027.
Kungiyar ta NCF ta amince da wannan bukata, inda mambobinta suka nuna goyon bayan su ga shugaban kasa ya fito daga Kudu da kuma tazarcen Tinubu.
Wasu tsofaffin 'yan majalisar sun bijirewa NCF
Sai dai wata kungiya ta daban da ta kunshi wasu tsoffin 'yan majalisa daga Arewa ta nesanta kanta daga matsayar NCF, tana mai cewa taron farfaganda ce kuma bai nuna ainihin ra’ayin mutanen Arewa ba.
A wata sanarwa, wannan kungiya ta masu sukar NCF ta ce taron kungiyar siyasa ce kawai da aka tsara don baje kolin wani ra'ayi da bai da sahihancin wakiltar dukkanin tsoffin 'yan majalisa daga Arewa.
Sanarwar, wadda Zakari Mohammed, Aminu Shagari, Tom Zakari da Mohammed Musa Soba suka sanya wa hannu, ta ce an yaudari kungiyar NCF a goyawa Tinubu baya.

Source: Twitter
"NCF ba ta wakiltar Arewa" - Zakari, Aminu
Jaridar Punch ta rahoto su Zakari suna cewa:
“Wannan kungiya ba ta wakiltar dukkanin tsoffin ‘yan majalisa daga Arewa, kuma matsayar da suka dauka ba ya nuna ko wakiltar halin da al’ummar Arewa ke ciki a halin yanzu.
“NCF tamkar wata kungiyar siyasa ce kawai, kuma ya kamata su bayyana kansu a matsayin magoya bayan Femi Gbajabiamila kai tsaye, maimakon fakewa da sunan taron tattaunawa.
“Kowa yana gani, a karkashin wannan gwamnatin, talauci ya tsananta matuka, inda iyalai da dama ke cikin mawuyacin hali na tattalin arziki, ga matsalar tsaro a Arewa.”
Daga karshe, kungiyar ta yi watsi da duk wani ikirarin shugabanci daga NCF ta fitar, tana mai cewa kungiyar na kare muradunta ne kawai, ba wai don amfanin al'umma ba.
Kungiyar Arewa ta goyi bayan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta ce babu wani dalili da zai hana Arewa goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Kungiyar ATT ta ce Arewa za ta goyi bayan Shugaba Tinubu, duba da ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a fannin tsaro da ababen more rayuwa a yankin.
Jagoran kungiyar, Muhammad Alhaji Yakubu, ya ce mayar da hankalin da Tinubu ke yi wajen ci gaban yankin Arewa ya haifar da sakamako mai kyau.
Asali: Legit.ng


