Dilan Ƙwaya: Bayanai Sun Bulloƙo kan Kwamishinan Kano, Ana Zargin Ya Karbi $30,000

Dilan Ƙwaya: Bayanai Sun Bulloƙo kan Kwamishinan Kano, Ana Zargin Ya Karbi $30,000

  • Rahoton Hukumar DSS ya sake bankado wasu bayanai game da Kwamishinan sufuri na Kano, Ibrahim Namadi
  • An bayyana cewa Kwamishinan ya karɓi $30,000 daga Sulaiman Danwawu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi
  • Gwamna Abba Yusuf ya fusata da wannan batu tare da kafa kwamiti, duk da cewa Namadi yana da dangantaka da Rabiu Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana zargin kwamishinan sufuri na jihar Kano, Ibrahim Namadi da karɓar $30,000 don belin Sulaiman Danwawu.

Rahoton Hukumar DSS ya ce Kwamishina ya karbi cin hanci daga sanannen ɗan safarar miyagun ƙwayoyi domin yin belinsa.

An sake samun bayanai kan Kwamishina a Kano
Rahoton DSS ya fito bayanai kan Kwamishina a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Rahoton DSS kan Kwamishinan sufurin Kano

Daily Nigerian ta ce Ibrahim Namadi yanzu yana cikin majalisar zartarwa ta Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi a hedikwatar DSS da ke Abuja sun shaida cewa hukumar ta gudanar da bincike a asirce kuma ta ba da shawarar a kori kwamishinan.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Kotu ta nuna iko bayan hana gwamna zaɓe da naɗa Sarki a jiharsa

A cewar rahoton, an biya kwamishinan $30,000 kafin ya amince da zama mai karbar belin shahararren dillalin miyagun ƙwayoyi.

Bayan fushin jama'a kan lamarin, gwamnan ya kafa kwamitin bincike da zai binciki batun belin tare da mika rahoto cikin mako guda.

Gwamna Abba Kabir ya ba ‘yan sanda haɗin kai wajen cafke Danwawu kuma ya matsa lamba kan NDLEA kada su saki wanda ake zargi.

“Gwamna Abba Yusuf yana kallon abin da kwamishinan ya yi a matsayin kalubale kai tsaye ga yaki da shan miyagun ƙwayoyi.
“Watanni da suka gabata, kwamitin tsaro na jihar wanda gwamnan ke jagoranta ya yanke shawarar cewa cafke Danwawu ne mafita.
“Don haka gwamnan ya amince a gudanar da aiki na ɓoye domin cafke Danwawu, wanda CP Bakori ya kammala cikin nasara.”

- Cewar wata majiya

Ana zargin Kwamishinan na da alaƙa da Kwankwaso a Kano
Abba Kabir ya kafa kwamiti domin bincike kan Kwamishina. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Meyasa gwamna bai iya korar kwamishinan ba?

Wasu majiyoyi sun gano cewa tun farko gwamna Abba Yusuf yana shirin korar kwamishinan, amma ya dakatar da shirin bayan tuntubar Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Bayan zargin shirya yi wa Tinubu juyin mulki, ana so hukuma ta dauki mataki

Majiyar ta ce:

“Kwamishinan yana da dogon tarihi na badakala, amma gwamna ba ya son ya saba wa Kwankwaso."

Dangantaka tsakanin gwamna da kwamishinan na kawo tsaiko, domin fiye da takardu 30 daga ma’aikatar suna ofis dinsa ba tare da duba su ba.

Namadi ya musanta zarginsa da ake yi

Da aka tuntube shi domin martani, Ibrahim Namadi ya musanta zargin yana mai cewa:

“Ban san da wannan zargi ba, ba gaskiya ba ne.”

Amma ƴan mintuna bayan kiran Namadi, kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya yi magana yana zargin cin zarafin abokin aikinsa.

A wani yunkuri na razana ɗan jarida, ya ce:

“Wane irin aikin jarida kuke yi…? Me ya sa ku ka kasa barin wannan batu ya mutu?”

NDLEA ta kama Danwawu da zargin safarar kwayoyi

Mun ba ku labarin cewa Hukumar NDLEA ta shigar da kara kan wani matashi Sulaiman Danwawu a gaban kotun tarayya a Kano kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Bayan Muhuyi ya sauka, Gwamna Abba ya naɗa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano

An kama shi matashin da miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol, Rohypnol da Pregabalin, dukkaninsu na kamanceceniya da hodar iblis.

NDLEA ta kuma bayyana cewa ana yiwa Sulaiman Danwuwu tuhume-tuhume takwas, a kan safarar kwayoyi masu hadari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.