Bikin Gargajiya: Gwamnoni 4 Za Su ba Ma'aikata Hutu na Musamman a Agustan 2025

Bikin Gargajiya: Gwamnoni 4 Za Su ba Ma'aikata Hutu na Musamman a Agustan 2025

  • Oyo, da jihohin Kudu uku za su ayyana hutu na musamman ranar 20 ga Agusta domin bikin al’adar gargajiyar Yarbawa ta Isese
  • Gwamnatocin jihohin sun amince da hutu bayan matsin lamba daga masu bautar gargajiya da sarakuna domin girmama al’adun Yarbawa
  • Jihohin Ondo da Ekiti ne kawai a Kudu maso Yamma da har yanzu ba su dauki 20 ga Agusta a matsayin hutu na bikin Isese ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo – Idan ba a samu wani sauyi ba, to ana sa ran gwamnonin jihohi hudu; Oyo, Lagos, Ogun da Osun za su ayyana hutu na musamman don bikin ranar Isese.

Ranar Isese na gudana ne a duk shekara a ranar 20 ga watan Agusta domin girmama addini da al’adun gargajiyar Yarbawa.

Kara karanta wannan

2027: Dino Melaye da wasu na hannun daman Atiku 2 da suka fice daga PDP zuwa ADC

Ana gudanar da bikin Ranar Isese a watan Agusta, musamman ranar 20 ga watan.
Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma sun gana da manema labarai a Legas. Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

Masu bautar gargajiya sukan gudanar da addu’o’i, raye-raye da kuma hadaya domin karrama gumakansu a irin wannan rana, a cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A shekarar 2025, 20 ga watan Agusta za ta fado ne a ranar Laraba, kuma shi ne hutu daya tilo da za a yi a watan a sassan kasar.

Jihohin da za su ayyana hutu don ranar Isese

A wannan rahoton, Legit Hausa ta jero jihohin da za su ayyana hutu don ranar Isese kamar yadda suka yi a shekarun baya:

1. Jihar Oyo

A shekarar 2022, masu bautar gargajiya a Oyo suka sake gabatar da bukatar neman a ayyana hutu don bikin Isese.

Kodayake gwamnati ba ta ayyana hutu a wancan shekarar ba, amma daga bisani Gwamna Seyi Makinde ya amince da 20 ga Agusta a matsayin ranar hutun Isese daga shekarar 2023.

2. Jihar Legas

Kamar Oyo, jihar Lagos ta fara ayyana hutu don bikin Isese a shekarar 2023 bayan majalisar sarakunan gargajiya ta jihar ta rubuta wa majalisar dokoki wasika kan neman hakan.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

3. Jihar Ogun

A watan Yulin 2023, majalisar dokokin jihar Ogun ta amince da kudurin da ya ayyana 20 ga Agusta a matsayin ranar al’adar Isese da kuma hutu a jihar.

Manyan dalilan kudurin sun haɗa da farfado da al’adu da bunkasa yawon shakatawa a jihar ta Ogun.

Jihohi 4 za su ayyana ranar hutu a watan Agusta don bikin gargajiya na Isese.
Ranar Isese wani biki ne na musamman da ake gudanarwa a wasu jihohin Yarbawan Najeriya. Hoto: @ifayemi
Source: Twitter

4. Jihar Osun

Gwamnatin jihar Osun ta dade tana ayyana hutu domin ranar Isese tun shekarar 2013, lokacin Gwamna Rauf Aregbesola, inji rahoton The Guardian.

Ranar hutu ce ta musamman ga masu bautar gargajiya inda bankuna da ofisoshin gwamnati ke rufewa don girmama hutun.

A cewar rahoton Legit.ng, jihohin Ondo da Ekiti ne kadai daga cikin jihohin yankin Kudu maso Yamma shida da har yanzu ba su ayyana 20 ga Agusta a matsayin ranar hutu ba.

An daure shugabar al'adun gargajiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun majistare da ke zama a Ilorin, ta yanke hukuncin tsare Madam Efunsetan Abebi Aniwura Olorisha a gidan yari.

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sha ruwan sama da tsawa a Yobe, Katsina da jihohi 27 a ranar Alhamis

Madam Abebi, wacce aka fi kira da Iya Osun, ta kasance babbar mamba a ƙungiyar masu addinin gargajiya na Isese da ke jihar Kwara.

Bayanan da Legit.ng ta samu sun nuna cewa, an hana bayar da belin matar, wacce ita ce shugabar masu addinin gargajiya na Isese.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com