"Ba Mu Buƙatar Kuɗi," Kasurgumin Ɗan Bindiga, Sani Black Ya Zo da Sabon Salo a Zamfara
- Hatsabibin ɗan bindiga a Zamfara, Sani Black ya nemi haraji daga mutanen kauyuka huɗu a yankin ƙaramar hukumar Zurmi
- Ɗan bindigar ya bukaci mazauna waɗannan kauyuka su ba shi zinari mai nauyin kilo 150 domin ba su kariya da kaucewa hare-harensa
- Rahoto ya nuna cewa Sani Black ya nemi zinari ne saboda ya fahimci mutanen yankin suna haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar Zamfara ya bukaci zinari mai nauyin kilogiram 150 daga garuruwa huɗu a matsayin kudin kariya (haraji).
Ɗan ta'addan, wanda aka fi sani da Sani Black ya buƙaci waɗannan garuruwa su nemo masa zinari ne domin kaucewa hare-hare da samun zaman lafiya a yankinsu.

Source: Original
Sani Black ya nemi harajin zinare a Zamfara

Kara karanta wannan
Mutanen gari da 'yan sanda sun yi arangama da 'yan sanda a Abuja, an samu asarar rai
Ƙauyukan da Sani Black ya nemi harajin zinaren sun haɗa da Dada, Gidan Shaho, Marmaro da Rimni, duka a yankin ƙaramar hukumar Zurmi na jihar Zamfara, inji Premium Times.
Wannan bukatar ta zinari ta sha bamban da yadda 'yan ta'adda ke bukatar kuɗin fansa ko dabbobi a da.
Ana ganin dai hakan yana nuna wani sabon salo da 'yan ta'addan suka ɓullo da shi domin samun kuɗi don ci gaba da ayyukansu na ta'addanci a yankin.
Yanzu haka, al'ummomi waɗannan garuruwa da abin ya shafa na cikin damuwa da matsin lamba na tara zinari mai darajar kudi madu yawa.
Meyasa ƴan bindiga suka nemi zinari?
Wasu majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa bukatar na da nasaba da zargin cewa mutanen yankin na harkar hakar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.
Wani matashi daga yankin ya shaida wa manema labarai bisa sharadin ɓoye sunansa saboda yanayin tsaro, cewa:
“Mai yiwuwa ne yana tunanin suna da zinari da yawa tunda da dama daga cikinsu suna harkar haƙar ma'adanai."
Haka nan kuma, wani mazaunin yankin ya ce:
“’Yan bindigar nan sun san cewa ba mu da kuɗi ko dabbobi da za mu ba su yanzu, don haka suka nemi zinare, wanda suka san ya fi sauƙin samu a yankin.”

Kara karanta wannan
Gwara Haka: Jagororin 'yan bindiga sun gwavza fada a Zamfara, an samu asarar rayuka

Source: Twitter
Wane hali mutanen garuruwan 4 ke ciki?
Rahoton Daily Post ya nuna cewa sama da shekaru 10 da suka shuɗe, yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na fama da matsanancin rashin tsaro sakamakon hare-hare da sace mutane da ƴan bindiga ke yi.
A wasu yankuna na jihar Zamfara, wasu ƙungiyoyin ƴan ta’adda sun kwace wuraren hakar ma’adanai domin satar zinari kai tsaye.
An ruwaito cewa mutanen kauyukan da abin ya shafa sun fara tattaunawa domin ganin ko za su iya tara zinariyar da ɗan bindigar ya buƙata ko za su nemi rangwame.
Wani ɗan Katsina da ya nemi sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa su kansu ƴan bindiga sun rubuto wasiƙa suna neman a haɗa masu Naira miliyan 150.
Ya ce hakan ya zama ruwan dare a duka yankunan da ƴan bindiga ke kaiwa hare-hare duk da ana yaɗawa cewa an yi sulhu da su.
Ya ce:
"Yanzu haka an turo mana takarda, wannan abin ya zama ruwan dare, muna kira ga gwamnati ta ɗauki mataki saboda kare rayuka na ɗaya daga cikin nauyin da ya rataya a kanta.
"Mu dai mun miƙa lamarinmu ga Allah don ba mu san yadda za mu tar kuɗin da suka nema ba, Allah Ya kawo mana zama lafiya, Ya shiryar da shugabannin mu."
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa Sojojin haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma sun dakile harin 'yan ta’adda a Neja da ke Arewa ta Tsakiya.
Mai magana da yawun rundunar Operation Fansan Yamma, Kyaftin David Adewusi, ya ce sojoji sun fafata da 'yan ta'adda kuma sun tura da dama lahira.
Adewusi ya ce wannan harin ya dakile 'yan ta’addan daga cimma burin su na farmakar mutane da sace dabbobi a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
