Rarara Ya Magantu kan Yiwuwar Cigaba da Waƙa da Amarya, Aisha Humairah bayan Aure
- Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara ya ce yana da ikon yanke hukuncin ko amaryarsa Aisha Humairah za ta ci gaba da waka
- Mawakin ya bayyana cewa sun saba aikin waka tun kafin aure, don haka babu matsala idan suka ci gaba da aiki tare da take cikin gidansa
- Rarara ya ce wannan magana ce tsakaninsu, ba sai sun bayyana wa duniya ba, kuma ya bar masu sauraro su yi hukuncinsu da kansu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Mawakin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya yi magana kan cigaba da aiki da amaryarsa.
Rarara ya bayyana cewa shi ya ke da hakki kan duk abin da ya ga dama game da cigaba da aiki da ita ko sabanin haka.

Source: Facebook
Rarara ya magantu kan aiki da Aisha Humairah
Mawakin ya bayyana haka a cikin wata hira da DCL Hausa ta aka wallafa a Facebook a safiyar yau Asabar 2 ga watan Agustan 2025.
A cikin bidiyon, Rarara ya ce wannan ba abin damuwa ba ne tun da daman sun saba aiki tun kafin su yi aure.
Rarara ya ce yana da damar ya ce su ci gaba da aiki ko kuma ya umarce ta ta zauna a gida tun da matarsa ce.
Ya ce:
"Ah to wannan kuma ai matata ce idan na ga dama na ce ta yi idan ban ga dama ba na hana ta, tun da wannan sana'a ta ce.
"Kuma ita ma a ciki na same ta, a ciki muka hadu, ka ga dukanmu mun gamsu da wannan sana'a ce ita muke yi."

Source: Facebook
Rarara ya fadi matsayarsa kan waka da amaryarsa
Rarara ya ce hakan ba wani abun damuwa ba ne kuma sirri ne tsakaninsa da mai dakinsa ba dole sai ya bayyanawa duniya ba.
Ya ce ya ragewa mai kallo ko sauraro ya yi amfani da abin da ya gani daga yanzu ya yanke wa kasa hukunci.
Ya kara cewa:
"To ka ga wannan wani abu ne tsakaninmu ba sai mun bayyana ba sai dai kawai mai sauraro ya yi amfani da abin da ya gani.
"Idan na ga dama in ce Aisha kizo kullum mu yi, waka daman muke yi da babu aure bare yanzu da ita matata ce ai don ta bini wurin aiki ba wani abu ba ne.
"Amma dai wannan wani abu ne wanda ni zan iya yanke hukunci ko ince mu yi ko kuma ki zauna a gida ko ki bini."
Rarara, Humairah sun magantu bayan aure
A baya, mun kawo muku cewa an daura auren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara da fitacciyar jaruma, Aisha Humaira a Maiduguri ba tare da sanar da jama’a ba.
Rarara da amaryarsa sun bayyana farin cikinsu, inda suka bukaci a yi musu addu’a tare da fatan alheri ga duk wanda suka taba yi wa kuskure.
Sanata Barau Jibrin ya halarci daurin auren, kuma ya bayyana cewa aure ne na soyayya tare da yin fatan zaman lafiya mai dorewa ga ma'auratan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

