'Ba Mu Janye ba,' Malaman Jinya Sun 'Kunyata' Ministan Lafiya kan Batun Yajin Aiki

'Ba Mu Janye ba,' Malaman Jinya Sun 'Kunyata' Ministan Lafiya kan Batun Yajin Aiki

  • Ƙungiyar NANNM ta bayyana cewa ba ta janye yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da ta shiga ba duk da ganawa da Ministan lafiya
  • NANNM na neman karin alawus, ɗaukar sababbin ma’aikata, kafa bangaren malaman jinya a ma’aikatar lafiya ta tarayya da dai sauransu
  • An ce yajin aikin ya jefa marasa lafiya cikin ƙunci a asibitoci da dama, inda aka rufe wasu dakuna gaba ɗaya saboda ƙarancin ma’aikata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Ƙungiyar malaman jinya da ungozoma ta kasa reshen asibitocin tarayya (NANNM-FHI) ta karyata rahotannin da ke cewa ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta shiga.

Legit Hausa ta ruwaito cewa malaman jinyar sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai ne a ranar Laraba, 30 ga Yulin 2025.

Malaman jinya sun ce har yanzu ba su janye yajin aikin da suka shiga ba duk da ganawarsu da ministan lafiya.
Har yanzu malaman jinya a Najeriya na ci gaba da yajin aikin gargadi na kwana 7. Hoto: Getty Images, @muhammadpate/X
Source: UGC

Malaman jinya ba su janye yajin aikin ba

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: 'Yadda gwamnatin tarayya ta hana a kashe Bello Turji a Zamfara'

Da yake zantawa da jaridar Punch a ranar Juma’a, jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na NANNM-FHI, Omomo Tibiebi, ya bayyana cewa ba su janye yajin aikin ba duk da ganawar da suka yi da ministan lafiya a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta shiga yajin aikin ne domin matsawa gwamnati lamba ta biya mata buƙatunta, wadanda suka haɗa da ƙarin kuɗin alawus na aiki, daidaito a kudin kayan sanyawa na aiki.

Sauran bukatun sun hada da ƙirƙirar tsarin albashi na musamman ga malaman jinya, ƙarin kuɗin aikin jinya, ɗaukar sababbin ma’aikatan jinya da kuma buƙatar a kafa sashen harkar jinya a ma’aikatar lafiya ta tarayya.

Tibiebi ya ce:

“Ba a dakatar da yajin aikin ba. A safiyar yau ne shugabannin NANNM suka gana da ministan lafiya, Farfesa Muhammad Pate, kuma shi ne ya sanar da manema labarai cewa an dakatar da yajin.
“To amma ai shi ba shi ne ya kira yajin aikin ba a farko, don haka ba shi da ikon dakatar da shi. Yajin aiki dai yana nan yana gudana.”

Malaman jinya za su fitar da matsaya gobe

Ya ƙara da cewa za a gudanar da taron majalisar zartarwa ta ƙasa na ƙungiyar a gobe Asabar domin tantance alkawuran da gwamnatin tarayya ta yi da kuma fitar da mataki na gaba.

Kara karanta wannan

Malaman jinya sun cimma matsaya kan janye yajin aiki a fadin Najeriya

“Za a yi taron majalisar zartarwa na ƙasa gobe Asabar, sannan za a yanke shawarar ko abubuwan da gwamnatin tarayya ta bayar sun isa a dakatar da yajin aikin,” inji Tibiebi.

A halin yanzu, asibitoci a faɗin ƙasar na fama da tasirin yajin aikin, inda marasa lafiya ke fuskantar tsaiko a wajen samun kulawa ta lafiya.

An sallami marasa lafiya da dama saboda ƙarancin ma’aikatan jinya, an rufe wasu dakunan asibiti gaba ɗaya yayin da wasu dakunan ke aiki da ƙarancin ma’aikata.

Malaman jinya sun ce za su duba yiwuwar janye yajin aikin ne a taron da shugabanninsu za su yi ranar Asabar.
Malaman jinya na duba marasa lafiya a wani asibiti da ke jihar Zamfara. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan lafiya ya kawo batun janye yajin

BBC Hausa ce ta rahoto cewa ministan lafiya a Najeriya, Farfesa Ali Pate ya ce ma'aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar NANNM sun janye yajin aikin da suka fara yi.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Juma'a, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin aikin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin tarayya bayan wata ganawa a yau ɗin.

Sai dai tun ma ba a je ko ina ba, ƙungiyar NANNM ta fito ta musanta kalaman na ministan. Yanzu dai za a jira matakin da malaman jinyar za su dauka gobe Asabar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fito da shirin tallafawa mutane miliyan 8 a fadin Najeriya

"Ban ga laifin su ba" - Malama Safiyya

Wata ma'aikaciyar jinya da muka zanta da ita a jiha Kaduna, Malama Safiyya (wanda ba asalin sunanta ba ne) ta ce ba ta ga laifin malaman jinyar da suka shiga yajin aiki ba.

Malama Safiyya ta ce:

"Gaskiya yana da kyau da suka tafi yajin aiki saboda malaman jinya muhimman ma'aikatan lafiya ne, ya kamata a ce an biya bukatunsu sosai.
"An yi magana, an ba gwamnati wa'adi, duk dai ba a daidaita ba, idan aka tafi yajin aikin ina ga zai taimaka, sai gwamnati ta gane amfanin malaman jinyar.
"Ko da a ce ba a biya bukatunsu gaba daya ba, amma zai zama an duba muhimmai daga ciki an biya masu."

Malama Safiyya ta kuma ce bai kamata gwamnati ta yi watsi da bukatun malaman jinyar ba, la'akari da cewa babu wani fanni da gwamnatin ta biya ma bukatunsa.

Ta kawo misali da matsalar tsaro da kullum gwamnati ke cewa ta na mayar da hankali a kansa, inda ta ce har yanzu Arewa maso Yamma na fuskantar matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Maryam Bukar: 'Yar Arewa ta zamo jakadiya ta farko a majalisar dinkin duniya

Game da likitoci ko malaman jinya da ke tsallakewa suna neman aiki a kasashen waje, Malama Safiyya ta ce:

"Ba za ka iya tsayawa ka gina kasa ba idan kasa ba za ta gina ka ba. Idan an ba ka tallafi ka yi karatu, ka gode, amma ya kamata a duba yanayin aiki shi ma.
"Ya kamata a rika duba yanayin aikin su ma'aikatan lafiyar, domin sau tari kana aikin ne amma shi aikin ne yake so ya kwantar da kai kasa, ai ka ga ba dadi."

Ma'aikatan jami'a sun shiga yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’ar jihar Legas.

An umarci malamai da ma’aikata da su janye daga aiki a LASU, LASUCOM-Ikeja da sashen Epe daga ranar Alhamis, 31 ga watan Yulin 2025.

Kungiyoyin na so a biya masu bukatunsu, da suka hada da karin albashi, daidaita albashi da na sauran makarantu da kuma aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com