Gwamnatin Kaduna za ta biya Malaman lafiya da ke aikin COVID-19 alawus

Gwamnatin Kaduna za ta biya Malaman lafiya da ke aikin COVID-19 alawus

- Za a biya kudi ga iyalan malaman asibitin da su ka mutu wajen jinyar COVID-19 a Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna za ta dauki nauyin ma’aikatan lafiyan da su ka harbu da COVID-19

Kwamishinar lafiya ta jihar Kaduna, Dr. Amina M. Baloni ta sanar da irin jerin alawus din da gwamnati ta shigo da su domin ma’aikatan lafiya da ke yaki da cutar Coronavirus a jihar.

Amina M. Baloni ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta amince da alawus da kuma kudin inshora ga malaman lafiyan da su ka mutu a asibiti a sanadiyyar kula da masu COVID-19.

Gwamnatin Kaduna ta kasa ma’aikatan lafiya da ke aikin jinyar masu cutar COVID-19 zuwa gida uku; za a rika biyan wadanda su ka fi samun alaka da masu wannan cutar N15, 000 kullum.

Ma’aikatan da ke samun matsakaicin alaka da masu jinya za su karbi N10, 000 duk rana. Sauran ma’aikatan da hadarin da su ke shiga bai kai na sauran rukunanba ba za su samu N5, 000.

Haka kuma gwamnati ta ware kudi masu tsoka ga iyalin wadanda su ka rasu wajen kula da masu cutar COVID-19. Gwamnati za ta biya iyalan wadannan ma’aikatan lafiya Naira miliyan 5.

KU KARANTA: Abin da zai sa a sassauta dokar kulle a Jihar Kaduna - El-Rufai

Duk ma’aikacin da ya samu wata tawaya ko nakasa wajen jinyar Coronavirus zai samu Naira miliyan biyu da rabi daga hannun gwamnatin Kaduna kamar yadda kwamishinar ta bayyana.

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta kuma amince a biya N100, 000 na tsawon kwanaki goma domin kula da duk wani malamin asibiti da ya harbu da cutar Coronavirus wajen jinyar marasa lafiya.

Bayan haka gwamnatin Nasir El-Rufai ta amince da bada alawus na 10% daga albashin malaman lafiyan da ke aiki a duk wasu dakunan shan magani da asibitocin gwamnatin da ke Kaduna.

Baloni ta bayyana cewa kamfanin Leadway Assurance ne zai dauki nauyin biyan wadannan kudi. A karshe gwamnan ya sake godewa malaman da su ka kula da shi a lokacin da ya ke jinya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel