Yaƙi da Yan Ta'adda: Gwamnatin Tarayya Za Ta Ɗauki Matasa 13000 Aikin Sojan Ƙasa

Yaƙi da Yan Ta'adda: Gwamnatin Tarayya Za Ta Ɗauki Matasa 13000 Aikin Sojan Ƙasa

  • Hedikwatar sojin kasa ta ce za a dauki sababbin sojoji 13,000 kafin karshen 2025 amma babu isassun kuɗaɗen kula da su
  • Laftanar-Janar Olufemi Oluyede ya bayyana matsalolin da rundunar sojin kasa ke fuskanta musamman rashin matsuguni da kayan aiki
  • Majalisar dattawa ta bayyana cewa akwai buƙatar a cire sojoji daga tsarin kasafin bai daya domin samar masu da isassun kuɗaɗe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar sojin kasa ta Najeriya ta bayyana cewa za a dauki sababbin sojoji 13,000 kafin ƙarshen shekarar 2025 domin ƙara ƙarfin rundunar.

Sai dai shugaban rundunar, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, na fargabar cewa ba za a iya kula da sababbin jami'an yadda ya kamata ba saboda ƙarancin kuɗaɗe.

Rundunar sojin kasa ta ce za a dauki sababbin sojoji 13,000 aiki kafin karshen 2025
Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya ziyarci barikin sojin Zamfara. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojojin kasa na korafin karancin kudi

Olufemi Oluyede ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da kwamitin majalisar dattawa kan harkokin soja, ya kai masa ziyarar aiki a ranar Alhamis, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban rundunar ya roƙi gwamnati ta ƙara wa sojin kasa kuɗin gudanarwa, yana mai cewa rundunar na da tarin buƙatu da ke bukatar isasshen kudi.

Ya yi nuni da cewa samar da walwala da kayan aiki na zamani su ne manyan abubuwan da za su kara wa sojoji kaimi wajen yaki da ta'addanci a kasar nan.

An rahoto cewa shugaban kwamitin, Sanata Abdulaziz Yar’Adua, ya jaddada bukatar inganta ayyukan tsaro a ƙasar nan saboda yawaitar matsalolin tsaro da ake fuskanta.

"Za a dauki sababbin sojoji 13,000" - Hafsu

A jawabinsa yayin ziyarar, Laftanar-Janar Oluyede ya bayyana damuwa kan tsarin kasafin kuɗin da ake ba rundunar soji, wanda ya ce baya isa wajen biyan bukatun rundunar.

Ya ce:

"A bana kaɗai, muna sa ran samun sababbin sojoji 13,000 amma babu isassun kuɗi da za su samar musu da matsuguni.
"Har yanzu akwai sojojinmu da ba su da inda za su zauna, kuma lamarin kullum gaba yake yi ba wai baya ba."

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta ɓarke a haɗakar su Atiku, jigon ADC ya naɗa kansa shugabanci

Olufemi Oluyede ya bukaci a samar da wata sabuwar hanya ta ware kuɗi kai tsaye ga rundunar sojin Najeriya ba tare da ta shiga tsarin kasafin ba, domin samar da muhimman kayan aiki da walwalar sojoji.

Rundunar sojin kasa ta ce tana fuskantar karanci kudade da kayan aikin yakar 'yan bindiga
Shugaban rundunar sojin kasa (CoAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Majalisar dattawa ta daukarwa sojoji alkawari

Ya ƙara da cewa:

"Damuwar mu ba ta tsaya a kan cikin gida ba, me zai faru idan wata kasa ta kawo mana hari? Don haka muna bukatar ku duba yiwuwar ware kuɗaɗe na musamman don samar da matsuguni da kayan aiki ga sojojinmu."

Shugaban kwamitin, Sanata Yar’Adua, ya bayyana cewa sun fahimci ƙaranci kuɗi da rundunar ke fuskanta, tare da alƙawarin ci gaba da matsa lamba don a ƙara mata kasafi.

Yar’Adua ya ce:

"Ya kamata a cire rundunar soji daga tsarin kasafin bai daya domin ta samu isasshen kuɗin gudanar da ayyukanta."

Ya bayyana cewa kwamitinsu ya raba kansa zuwa rukunai biyu domin duba sansanonin soji a jihohin Borno, Katsina, Sokoto, Kebbi da Legas.

Motar sojoji ta fada babban rami a Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, soja daya ya mutu yayin da wasu biyu suka jikkata bayan motarsu ta yi mummunan hatsari a jihar Yobe

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, an tura miyagu barzahu

Sojojin da ke aiki a karkashin Operation Hadin Kai sun gamu da haɗarin ne yayin da suke tafiya a kan hanyar Jos/Damaturu domin wani aiki

An ce motar sojojin ta faɗa wani babban rami bayan direban ya rasa ikon sarrafa sitiyarinta, lamarin da ya jawo asarar rai da jikkatar sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com