Gingima Gingiman Bashi 6 da Bola Tinubu Ya Ci daga Fara Mulkin Najeriya

Gingima Gingiman Bashi 6 da Bola Tinubu Ya Ci daga Fara Mulkin Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa majalisar dattawa ta amince da bashin fiye da Dala biliyan 21 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ci bashi daga Bankin Duniya da Bankin Exim na China da sauran ƙasashen waje
  • Bincike ya tabbatar da cewa bashin da ake bin Najeriya a halin yanzu ya kai Naira tiriliyan 149.39, lamarin da ke nuna tulin shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar Dattawan ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓar bashi fiye da Dala biliyan 21 daga ƙasashen waje, domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da ayyukan ci gaba, kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro da inganta muhalli.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fito da shirin tallafawa mutane miliyan 8 a fadin Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

BBC Hausa ta wallafa jerin basussuka da dama da gwamnatin Tinubu ta karɓa tun daga hawanta mulki a watan Mayun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin basuka shida mafi girma da gwamnatin Tinubu ta amince da karɓowa:

1. Bashin Dala biliyan 21 – Yuli 2025

A ranar 22 ga watan Yuli 2025, Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar karɓar bashin Dala biliyan 21 domin amfani da shi a wajen cike gibin kasafin kudin 2025.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za a yi amfani da kuɗin ne wajen aiwatar da manyan ayyuka na ci gaba.

2. Bashin Dala miliyan 652 – Mayu 2025

Gwamnatin tarayya ta amince da karɓar bashi daga Bankin Exim na China domin gina titi a tashar ruwa ta Lekki, a ranar 6 ga watan Mayu 2025.

Rahotanni daga irinsu Business Day sun nuna cewa aikin da za a yi da Dala miliyan 652 di zai taimaka wajen rage cunkosa a wasu sassan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

3. Bashin Dala biliyan 2.21 – Nuwamba 2024

Majalisar ta goyi bayan buƙatar gwamnatin tarayya ta karɓo bashi Dala biliyan 2.21 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2024 a ranar 21 ga watan Nuwamba 2024.

Wannan shi ne bashi na karshe da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ciwo daga ketare a shekarar 2024.

Shugaba Bola Tinubu a majalisar wakilai
Shugaba Bola Tinubu a majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

4. Bashin Dala biliyan 2.25 – Yuni 2024

A ranar 13 ga watan Yuni 2024, Najeriya ta amince da karɓar bashin dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya domin daidaita tattalin arziƙi da kuma tallafa wa talakawa.

Daily Post ta ce kudin ya kasance wani bangare na kokarin gwamnatin Bola Tinubu na saukaka rayuwar al'umma yayin da aka fuskanci matsin tattali.

5. Bashin Dala miliyan 500 – Mayu 2024

The Sun ta rahoto cewa majalisar Dattawa ta amince da karɓar bashi Dala miliyan 500 domin samar da mitoci na wutar lantarki.

Wannan na daga cikin shirin karɓar bashin Dala biliyan 7.94 daga 2022 zuwa 2024, hakan na nuna an fara karbar kudin ne tun kafin zuwan Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta samar da ayyuka a Kaduna, za a farfado da masaka

6. Bashin $7.4bn, €100m – Disamba 2023

A ranar 30 ga watan Disamba 2023, Majalisar Dattawa ta amince da ciwo bashin dala biliyan 7.4 da Yuro miliyan 100, Pulse ta dauko labarin a lokacin.

Ofishin kula da lamuran bashi na ƙasa ya bayyana cewa, ya zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar 2025, bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39.

Tinubu zai yi manyan ayyuka a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta jaddada cewa za ta yi wasu muhimma ayyuka a Arewa.

Ministan sufuri a kasa, Sanata Sa'idu Ahmed Alkali ne ya bayyana haka yayin wani taro da aka yi a jihar Kaduna.

Sanata Alkali ya bayyana cewa daga cikin ayyukan da gwamnatin ta fara akwai samar da jiragen kasa a Kaduna da Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng