Aminu Ado Bayero da Kwankwaso Sun Haɗu a Wurin Taro, Sun Tattauna a Abuja
- An gudanar da taron kaddamar da littafin tarihin Cif Gabriel Igbinedion a dakin taro na cibiyar Yar’Adua da ke birnin Abuja
- Rabiu Musa Kwankwaso ya halarci taron tare da sauran manyan ’yan siyasa da sarakunan gargajiya kamar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
- Masarautar Kano ta tabbatar da halartar Sarkin kuma ta wallafa hotunansa da Sanata Kwankwaso suna magana yayin taron
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - A yau Alhamis 31 ga watan Yulin 2025 aka gudanar babban taro a birnin Abuja inda manya suka halarta.
An gudanar da taron kaddamar da littafin tarihin rayuwar Cif Gabriel Osawaru Igbinedion a dakin taro na cibiyar Yar’Adua da ke Abuja.

Source: Twitter
Sanata Kwankwaso ya halarci taron a Abuja
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yana daga cikin wadanda suka samu halartar taron kamar yadda ya sanar a shafin X.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa
Taron ya samu halartar manyan yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya da sauran mutane a Najeriya.
Daga cikin manyan da suka halarta akwai tsohon gwamnan Kwara kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.
A cikin rubutunsa, Sanata Kwankwaso ya ce:
"A yau, na ji daɗin halartar bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar Cif Gabriel Osawaru Igbinedion mai taken “The Chronicles of a Legend”, tare da wasu manyan mutane a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja.
"Ina taya Cif Igbinedion murna bisa kaddamar da wannan littafi da ke ɗauke da tarihin rayuwarsa wadda aka girmama kuma aka yi ta cikin kwarewa da nasara."
Aminu Ado ya hadu da Kwankwaso a taro
Har ila yau, sarakunan gargajiya manyan kasa da dama sun sheda wannan taro da aka gudanar a yau Alhamis.
Daga cikinsu akwai Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero wanda ya hadu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
An gano wasu hotuna da ke nuna mutanen biyu na tattaunawa yayin taron da aka yi.

Source: Facebook
Shafin Masarautar Kano da ke yada abubuwan da suka shafi Aminu Ado Bayero ta tabbatar da haka inda ta yaɗa hotunansu a taron.
Masarautar Kano ta wallafa a shafin X da cewa:
"Daga babban birnin tarayya Abuja,
"Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya halarci taron kaddamar da littafin rayuwar Cif Gabriel Osawaru Igbinedion mai suna (THE CHRONICLES OF A LEGEND) a safiyar yau Alhamis 31 ga watan Yulin shekarar 2025,
"Ran sarki ya dade."
Kwankwaso, Abba, Sanusi II sun hadu a taro
A baya, mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Kwankwaso ya halarci taron masu ruwa da tsaki kan gyaran kundin tsarin mulki.
Taron wanda ya gudana a gidan gwamnatin Kano, ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II domin kawo ci gaba a yankin.
Gwamnatin Kano ta ce an shirya taron domin jihar ta ɗauki matsaya gabanin taron jin ra'ayoyin jama'a na Majalisar Dattawa ta shirya a fadin kasar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
