Tinubu Ya Shiga Ganawa da Ministoci da Manyan Ƙusoshin Gwamnati a Aso Rock Villa
- Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta ƙasa a Abuja, inda ya fara da rantsar da sabon mamban hukumar NASC
- Hon. Nnanna Uzor Kalu ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Alhamis, bayan majalisar dattawa ta tabbatar da nadinsa a Mayun 2025
- An ruwaito cewa ministoci da manyan jami’an gwamnatin tarayya sun halarci taron FEC din, inda suka tattauna muhimman batutuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu na nuni da cewa Shugaba Tinubu na jagorantar taron FEC din ne a dakin taro na majalisar.

Source: Facebook
Tinubu ya rantsar da mamba a NASC
Jaridar Punch ta rahoto Tinubu ya rantsar da Hon. Nnanna Uzor Kalu, a matsayin mamba na hukumar kula da ayyukan majalisar ƙasa (NASC).

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Dakarun Sojoji sun hallaka ƴan bindiga sama da 3,000 a jihohin Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalu ya yi rantsuwar kama aiki da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Alhamis, jim kaɗan kafin fara taron majalisar FEC.
Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Hon. Uzor Kalu a ranar 20 ga Mayu, bayan amincewa da rahoton kwamitin kafa hukumomi da harkokin ma’aikata.
An amince da nadin bayan an warware wani ƙorafi da aka gabatar a baya kan nadin nasa, kuma an wanke shi daga zargin da ke tattare da ƙorafin.
Ya shiga cikin sababbin kwamishinonin NASC da aka rantsar a fadar shugaban ƙasa a ranar 5 ga Mayu, 2025, kuma zai yi aiki na tsawon shekaru biyar, tare da yiwuwar sabunta nadin.
Abubuwan da aka yi kafin taron FEC
Kalu, ƙanin tsohon gwamnan Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya taba zama ɗan majalisar wakilai na tsawon wa’adi biyu, inda ya wakilci mazabar Aba ta Arewa/Aba ta Kudu.
Majalisar FEC ta kuma yi jimamin rasuwar tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Navy Captain Caleb Olubolade (mai ritaya), wanda ya rasu a ranar 11 ga Mayu, 2025 yana da shekara 70 a duniya.
’Yan majalisar sun kuma yi shiru na minti ɗaya domin girmamawa ga Olubolade, wanda shi ne gwamnan soja na farko a jihar Bayelsa.

Source: Facebook
Ministoci da kusoshin gwamnati sun hallara
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sauran da suka halarci taron akwai mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu; shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Didi Walson-Jack; da babban sakataren ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Emmason Imabong.
Sauran mambobin majalisar da suka halarta sun haɗa da ministan kuɗi da tattalin arziki, Wale Edun; ministan tsare-tsaren kasafin kuɗi da tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu; da ministan yada labarai, Mohammed Idris, da sauran ministoci.
Mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sada zumunta, Olusegun Dada ya wallafa bidiyon zaman majalisar a shafinsa na X. Kalli bidiyon a kasa:
'Abin da zai hana Tinubu cin zaben 2027'
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ali Modu Sheriff ya ce abubuwa biyu ne kawai za su iya hana Shugaba Bola Tinubu zarcewa a 2027.
Fitaccen dan siyasar ya ce Shugaba Tinubu ba zai ci zaben 2027 ba ne kawai idan ya janye daga takara ko kuma ba a yi zaben ba gaba daya.
Sanata Modu Sheriff wanda ya bayyana cewa shi ne ya kawo Kashim Shettima siyasa ya kuma ce hadakar ADC ba za ta hana Tinubu nasara a 2027 ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

