Dangote Zai Saka Matatarsa a Kasuwa domin Jama'a Su Mallaki Hannun Jari
- Alhaji Aliko Dangote ya ce nan ba da jimawa ba zai sa matatarsa ta man fetur a kasuwa domin 'yan Najeriya su mallaki hannun jari
- Ya bayyana cewa matatar tana samar da tan 2,500 na iskar gas a rana domin bunkasa amfani da makamashi wajen girki a gidaje
- Dangote ya karyata zargin neman mamaye harkar man fetur, yana mai cewa ya fi so ya zuba jari a Najeriya ba a wasu kasashen waje ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa nan gaba kadan zai bai wa 'yan Najeriya damar mallakar hannun jari a matatarsa da ke Lekki, jihar Legas.
Aliko Dangote ya bayyana hakan ne yayin taron da hukumar NMDPRA ta shirya tare da hadin gwiwar wani kamfani a Abuja.

Source: UGC
Punch ta wallafa cewa Dangote ya ce shirye yake ya hada gwiwa da gwamnatoci, 'yan kasuwa masu zaman kansu da cibiyoyi domin ciyar da harkar man fetur gaba a nahiyar Afirka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote zai sayar da hannun jarin matatarsa
Alhaji Dangote ya bayyana cewa matatar da ya kafa a Lekki za ta shiga kasuwa nan ba da jimawa ba domin bai wa kowa damar mallakar hannun jari a cikinta.
Rahoton Economic Confidential ya nuna cewa ya ce:
“Muna shirin jawo jama’a cikin wannan gagarumin aiki. Wannan zai ba su damar sanya hannun jari a cikin matatar da take da kimar Dala biliyan 20.”
Dangote ya bayyana cewa ba wai don Najeriya kadai aka yi matatar ba, har da kasashen Afirka baki daya, yana mai cewa lokaci ya yi da Afirka za ta sarrafa man da take hakowa.
Dangote ya mayar da hankali kan iskar gas
Aliko Dangote ya ce suna sarrafa tan 2,500 na iskar gas a rana domin samar da makamashin girki mai tsafta a gidajen Najeriya.
Ya ce:
“Muna son ganin karin gidaje suna amfani da iskar gas wajen girki. Wannan zai amfani kasa, ya inganta lafiyar jama’a.”
Ya kara da cewa wannan wani bangare ne na ci gaban tattalin arzikin cikin gida da kuma rage dogaro da makamashi da ke cutar da muhalli.

Source: UGC
Dangote ya karyata zargin mamaye kasuwa
Dangote ya ce akwai masu zargin cewa yana neman mamaye kasuwar man fetur, amma ya bayyana cewa shi ya fi so ya zuba jari a cikin kasa fiye da fita waje.
Ya ce:
“Wasu masu arziki su na kai dukiyarsu kasashen waje, su bar kasar nan haka, amma mu mun zabi mu tsaya a gida mu taimaka wajen gina Najeriya.”
Ya gargadi gwamnati da kada ta bari shigo da kayayyaki marasa inganci ya rusa masana’antun gida kamar yadda ya faru a wasu fannoni
'Yan kasuwa suna wasan farashi da Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwa sun rage farashin man fetur, sun dawo da kudin lita kasa da yadda Dangote ke sayarwa.

Kara karanta wannan
Dattijon Arewa ya hararo babban rikici a Najeriya idan aka yi magudi a zaben 2027
Hakan na zuwa ne yayin da gasa ke kara zafi tsakanin Dangote da 'yan kasuwa wajen rige rigen sayar da kaya.
'Yan kasuwar sun yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi watsi da bukatar Aliko Dangote ta hana shigo da mai daga waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

