Sarkin Musulmi Ya Cire Tsoro a gaban Shugabannin Duniya kan Abin da Ake Yi a Gaza
- Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi magana kan abin da ke faruwa a Gaza wanda yake jawo asarar rayuka
- Sultan ya bukaci shugabannin duniya su kawo karshen kisan kiyashi a Gaza tare da yafewa kasashe talakawa bashi
- Ya yi wannan kira ne a taron kwana guda na 'Religion for Peace; a Istanbul, inda aka tattauna kan bashi da tasirin fasahar zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Istanbul, Turkey - Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya nuna damuwarsa kan abubuwan da ke faruwa a Gaza.
Sarkin Musulmi ya bukaci a kawo karshen rikicin Gaza da ke kashe mata da yara ƙanana da jawo asarar rayuka.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi ya bukaci kawo karshen kisa a Gaza
Sarkin ya yi wannan jawabi ne a taron kwana guda da aka gudanar a garin Istanbul, tsohuwar Constantinople, a kasar Turkey, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Abin da DSS suka yi wa ɗan TikTok da ake zargin ya ce Tinubu ya mutu sanadin guba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron wanda ake yi duk bayan shekaru biyar, na baya ya gudana ne a Lindau, Jamus, inda mutane daga kasashe 60 suka halarta.
An samu mahalarta daga addinai daban-daban kamar Hindu, Baha’i, Katolika, Anglican, Yahudawa da Musulmi, da kuma cocin Orthodox Coptic.
A cewar sanarwar, Kogunan Sokoto, Dr Danladi Bako, daya daga cikin tawagar Sarkin Musulmi, Patriarch na Constantinople, Bartholomew I sun yi jawabi kan hadin kan addinai.
Ya ce wajibi ne a dawo da darajojin da ke cikin kowanne addini domin samun zaman lafiya da daidaito a duniya baki daya.
An yi zama biyu inda aka tattauna kan nauyin bashi da kuma darajar addini da tasirin fasahar zamani ga al’adunmu da addinai, The Nation ta ruwaito.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi ya roki alfarmar yafe bashi
A yayin zaman, Sarkin Musulmi ya bayyana yadda bashin ke hana ci gaban kasashe masu tasowa da kara talauci da rashin daidaito.

Kara karanta wannan
'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'
Ya bada shawarar a gaggauta yafewa kasashe masu karamin karfi bashi domin rage bambancin arziki da kuma kawar da tsarin danniya na baya.
An samu muhawara daga kwararru, kungiyoyin addini, mata masu rajin kare hakki, masana da sarakuna a zama guda biyu na taron.
A karshe, an cimma matsaya guda tara da Sakataren Tattalin Arziki, Dr Francis Kuria ya karanta, ciki har da dakatar da rikicin Gaza.
'Religion for Peace World Council' kungiya ce da ke hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya, hedikwatarta na cikin ginin MDD a New York.
Za a gudanar da taron gaba daya na gaba na wannan Majalisa a birnin Abu Dhabi a shekarar 2030 mai zuwa idan Allah ya kaimu.
Sarkin Musulmi ya wakilci Najeriya a taron Musulmai
Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya halarci taron shugabannin Musulmi na duniya a Oxford, inda ya bukaci inganta zaman lafiya.
Taron na kwana biyu ya zo ne a matsayin bikin cika shekara 40 da kafuwar cibiyar nazarin addinin Musulunci ta Oxford a kasar Birtaniya.
An tabbatar taron ya samu halartar manyan shugabanni ciki har da Sarki Charles III, tsohon shugaban Turkiyya Abdullah Gul da yarima Turki Al Faisal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng