Hako Fetur a Arewa: Kamfanin NNPCL Ya Tono Rijiyoyin Mai 4 a Kolmani
- NNPCL ya tabbatar da kudirinta na hakar mai da iskar gas a yankin Arewa tare da gina sababbin cibiyoyi a jihar Kogi
- Wani rahoto ya nuna cewa an yi nasarar tono rijiyoyi hudu a yankin Kolmani da ke tsakanin Gombe da Bauchi
- Shirin zai samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki a jihohin Bauchi, Gombe da yankin Arewa maso Gabas
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, ya sake jaddada kudirinsa na ci gaba da hakar albarkatun mai da iskar gas a yankin Arewa.
Kamfanin ya bayyana hakan ne yayin wani taron hadin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma da aka gudanar a Kaduna ranar Laraba, 30 ga watan Yuli, 2025.

Source: Facebook
Ma'aikatar yada labarai ta kasa ta wallafa a X cewa NNPCL zai cigaba da aikin hako mai da aka fara a Kolmani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani darakta a kamfanin NNPCL, Yusuf Usman ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa a gaban mahalarta taron da gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya.
Ya ce kamfanin na aiki da cikakken tsari da dabaru domin tabbatar da dorewar ayyukan hakar man.
NNPCL ya hako rijiyoyi 4 a Kolmani
A cewar Yusuf Usman, zuwa yanzu kamfanin NNPCL ya kammala hako rijiyoyi hudu a yankin Kolmani da ke jihohin Gombe da Bauchi.
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce ana ci gaba da duba fasahar da ta dace domin shiga matakin gaba na aikin hako man.
Ya kara da cewa wannan yunkuri ya samo asali tun a zamanin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya kaddamar da hakar a Kolmani.

Source: Twitter
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin ci gaba da aikin domin bunkasa yankin Arewa maso Gabas.
Ana sa ran aikin zai haifar da damammakin aikin yi ga matasa da sauran mazauna jihohin Bauchi da Gombe da kewaye, tare da inganta tattalin arzikin yankin da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan
'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'
Ana gina cibiyoyin iskar gas 5 a Arewa
Yusuf Usman ya bayyana cewa a halin yanzu ana gina cibiyoyin iskar gas na CNG da LNG guda biyar a jihar Kogi domin kara samar da gas a yankin Arewa.
Ya ce hakan na cikin shirin Shugaba Bola Tinubu na bunkasa amfani da iskar gas bayan cire tallafin man fetur.
Ya kara da cewa aikin zai taimaka wajen rage dogaro da fetur da kuma sauƙaƙa sufuri da masana’antu, musamman a Arewa.
Mai magana da yawun Ministan yada labarai, Rabiu Ibrahim, ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar ci gaba da duk wasu ayyuka da za su bunkasa yankunan Najeriya.
Za a samar da jirgin kasa a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa ta fara shirin samar da jiragen kasa a Arewa.
Ministan sufuri na kasa, Sa'idu Ahmed Alkali ne ya bayyana haka yayin taron da aka gudanar a jihar Kaduna.
Sa'idu Alkali ya bayyana cewa jihohin Kano da Kaduna sun fara cin gajiyar shiri a karon farko kafin a fadada shi a sauran yankuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
