Katsina: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa ga Mutum 2 kan Kisan Tsohon Kwamishina

Katsina: Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa ga Mutum 2 kan Kisan Tsohon Kwamishina

  • Kotu a Katsina ta yanke hukuncin kisa ga mai gadi da mai dafa abinci bisa kashe tsohon kwamishina, Rabe Nasir
  • Rahoton ya ce wadannan mutane sun kashe marigayi Rabe ta hanyar sa masa guba bayan yunkurin sata ya ci tura
  • An yanke wa wani tsohon mai gadi ɗaurin shekaru 5, yayin da wata mace ta samu ‘yanci saboda rashin hujjoji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Babbar kotun jihar Katsina ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyu bisa laifin kashe tsohon kwamishinan kimiyya da fasaha, Rabe Nasir, a 2021.

Mai shari’a Ibrahim Mashi na kotu mai lamba 9 ya samu Shamsu Lawal da Tasi’u Rabi’u da laifin kashe Nasir ta hanyar sa masa guba.

Kotu ta yi hukuncin kan wadanda suka hallaka tsohon kwamishina a Katsina
An yanke hukuncin kisa kan wadanda suka hallaka tsohon kwamishina. Hoto: @jackietude.
Source: Twitter

Ana zargin mutane 2 da kisan tsohon kwamishina

Shamsu Lawal shi ne tsohon mai gadi a gidan Nasir, yayin da Tasi’u Rabi’u shi ne mai dafa masa abinci kafin rasuwarsa, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mahaifin yarinyar da malamin Musulunci ya kashe ya roki gwamnan Kwara alfarma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa mutanen biyu sun yanke shawarar kashe Nasir bayan yunkurin sata daga gidansa ya ci tura.

Binciken hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da asibiti ya tabbatar da cewa an samu sinadarin guba a cikin jikin marigayin.

Kotu ta yanke hukuncin cewa harin ya kasance da nufin kisa, kuma an shirya komai cikin tsari da hadin kai.

Kotu ta kuma yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ga wani tsohon mai gadi, Sani Sa’adu, saboda boye gaskiyar kisan.

Abin da lauyan wadanda ake zargi ya bukata

Lauyan masu laifi, Ahmad Murtala Kankia, ya roƙi kotu da ta sassauta hukunci saboda waɗanda ake tuhuma na da iyali da masu dogaro da su.

Wata mata mai suna Gift Bako ta samu ‘yanci bayan kotu ta gaza samun isassun hujjoji da za su danganta ta da laifin.

Rabe Nasir ya rike mukamin kwamishinan kimiyya da fasaha a zamanin Gwamna Aminu Masari kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Bayan zargin shirya yi wa Tinubu juyin mulki, ana so hukuma ta dauki mataki

Za a hallaka wasu da ake zargi da kashe tsohon kwamishina
An yanke hukuncin kisa kan wasu da zargin hallaka tsohon kwamishina a Katsina. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da dangin mamacin ke cewa

Har ila yau, ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa a shekarar 2003.

Mutuwarsa ta tayar da jijiyoyin wuya a jihar Katsina tare da kira ga gwamnati da ta ƙarfafa tsaro.

Al’umma da dangin mamacin sun bayyana farin cikinsu da hukuncin da kotu ta yanke, suna cewa adalci ya samu.

Hukumar yan sanda ta bayyana cewa wannan hukunci zai zama izina ga wasu da ke shirin aikata laifuffuka makamanta haka, Premium Times ta tabbatar.

Gwamnatin jihar ta ce zata cigaba da haɗin gwiwa da kotuna domin hukunta masu laifi da tabbatar da zaman lafiya.

Legit Hausa ta tattauna da lauya, Ahmad Murtala

Lauyan da ke kare wadanda ake zargi, Ahmad Murtala Kankiaya bayyanawa wakilin Legit Hausa matakin da suka dauka bayan yanke hukuncin.

Ya ce:

"Tun bayan yanke hukuncin na saka a raina matakin da zan dauka amma ka san dole sai sanin su wadansa ake zargi kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Za a rataye shi': Kotu ta yanke wa malamin Musulunci hukuncin kisa a jihar Kwara

"An yi sa'a kuwa suma ba su gamsu da hukuncin ba inda muka yanke shawarar daukaka kara kan matakin da kotun ta ɗauka."

Ya ce suna neman karin bayani kan hukuncin daga kotu domin daukar matakin da ya dace na daukaka kara.

Tsohon kwamishina ya riga mu gidan gaskiya

Kun ji cewa babban jigo kuma tsohon kwamishina a jihar Anambra, Cif Maja Umeh ya riga mu gidan gaskiya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Umeh ya kamu da ciwon bugun jini a 2022 amma ya samu sauƙi a kwanakin baya har ya halarci zaɓen fidda gwani na APGA a Anambra.

An ce Umeh ya rasu yana da shekara 64, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ke Awka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.