An Gwabza Fada tsakanin 'Yan Sanda da 'Yan Ta'adda a Katsina, An Rasa Rayuka
- Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta dakile yunkurin sace mutane a Katsina har sau biyu, inda aka ceto mutane 28 ba tare da sun ji rauni ba
- A harin farko da aka kai daren ranar Lahadi, ‘yan sanda sun kubutar da wasu mutane 14 da aka sace a Sabuwa tare da kwato shanu biyu
- A hari na biyu a safiyar Talata, ‘yan sanda sun sake fatattakar ‘yan bindiga bayan samun kiran gaggawa daga wani mai kishin kasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta ce ta dakile yunkurin sace mutane a karamar hukumar Sabuwa har sau biyu tare da ceto mutane 28.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa harin farko ya faru ne da misalin karfe 9:24 na safiyar Talata.

Kara karanta wannan
Ruwa da iska mai ƙarfi sun kifar da jirgi bayan ya ɗauko fasinjoji a jihar Jigawa

Source: Twitter
'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga a Sabuwa
DSP Sadiq ya ce wani mai kishin kasa ne ya kira rundunar a waya, yana sanar da su cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar Sabuwa–Kaya, kuma har sun sace mutane 14, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Bayan samun rahoton, DPO na Sabuwa ya hanzarta tura jami’ai zuwa wurin, inda suka gwabza da ‘yan bindigar. Sakamakon ruwan harsasai da 'yan bindiga suka sha ya sa suka tsere."
- DSP Abubakar Sadiq.
Hakazalika, 'yan sanda sun ceto dukkan mutane 14 da aka sace ba tare da wani ya ji rauni ba, sai dai DSP Sadiq ya ce ‘yan bindigar sun kashe wani matashi dan garin Funtua mai suna Abba.
DSP Sadiq ya ce wannan na daga cikin kokarin rundunar wajen ci gaba da yaki da masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a fadin jihar Katsina.
'Yan bindiga sun kashe mutum 2 a Sabuwa
Sanarwar DSP Sadiq ta kuma bayyana cewa wasu gungun 'yan bindigar sun kai wani hari da misalin karfe 11:27 na daren ranar Lahadi, 28 ga Yuli a Sabuwa.
Ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa na cewa ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai sun kai hari kauyen Zagaizagi da ke Sabuwa inda suka sace mutane a kauyen.
"DPO na Sabuwa ya sake jagorantar jami’ai inda suka sha kan ‘yan bindigar, suka yi musayar wuta, wanda ya haifar da nasarar ceto mutum 14 da aka sace. An kuma kwato shanun sata biyu a yayin artabun."
- DSP Abubakar Sadiq.
Sai dai, kakakin rundunar 'yan sanda a Katsina ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutane biyu yayin wannan harin.

Source: Twitter
'Yan sanda sun sha alwashin ba da tsaro
DSP Sadiq ya ce har yanzu rundunar na ci gaba da kokarin gano inda ‘yan bindigar suka yi sansani domin kamo su ko kakkabe su, inji rahoton Punch.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bello Shehu, ya jinjinawa jarumtar jami’ansa tare da bukatar jama’a su ci gaba da ba rundunar hadin kai domin rage barazanar ta’addanci a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa rundunar 'yan sanda ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Sojojin Najeriya sun fafata da 'yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Operation Hadin Kai sun kama wani da ake zargi ɗan ta’adda ne da ya shigo Najeriya daga kasar Nijar.
A hare-haren da sojojin suka gudanar a jihohi daban daban, dakarun sun yi nasarar kashe 'yan bindiga da dama tare da kama wasu.
Dakarun sojojin sun kuma kama masu safarar makamai, masu satar mai, sannan suka bankado maboyar IPOB a jihar Delta tare da kama mutane bakwai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

