'Ba Ku da Imani,' Ministan Buhari Ya Tsine wa Gwamnonin Arewa saboda Tinubu
- Solomon Dalung ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun ci amanar al’umma, sun yaudari talakawa sannan sun zura masu 'karya
- Tsohon ministan ya nuna mamakin ikirarin gwamnonin cewa Bola Tinubu ya cika dukkannin alkawuran da ya dauka ga yankin Arewa
- Dalung ya ce amma tun da gwamnonin na ganin Tinubu ya sauke nauyin da ke kansa, Allah Ya mayar da su halin da jama'a ke ciki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Solomon Dalung, tsohon ministan wasanni a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya yi kaca-kaca da gwamnonin jihohin Arewa da sauran ‘yan siyasa daga yankin.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnonin Arewa suka bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika dukkannin alkawuran da ya dauka dangane da ci gaban yankin Arewa.

Kara karanta wannan
"Ƴan Arewa ba su yi nadama ba," Minista ya faɗi abin da ke faruwa a gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na ADC Media Centre, Dalung ya yi zazzafar suka inda ya kira gwamnonin “marasa imani, marasa tsoron Allah kuma azzalumai.”
“Wane alkawari Tinubu ya cika?” - Dalung
A wani bidiyo daban da aka wallafa a shafin Facebook na Solomon Dalung Foundation, tsohon ministan ya bayyana mamakinsa kan yadda gwamnonin Arewa ke ikirarin cewa komai na tafiya lafiya a yankin.
A cewarsa:
“Kuna cewa duk alkawarin da Tinubu ya dauka ga Arewa ya cika su. Bari in tambaye ku: wane alkawari kuka kulla da Tinubu? Kuma wanne daga cikin alkawuran ya cika?”
“Alkawarinku da Tinubu kenan – cewa ya azabtar da al’ummar Arewa da yunwa, da talauci, da wahala? To, wannan alkawari ya cika.”
“Alkawarinku da Tinubu shi ne yadda aka kama mutane 48, aka karɓi kudin fansa har N2,000,000 daga kowannensu, daga baya kuma aka yi musu yankan rago?”
Dalung ya yiwa gwamnonin Arewa mugun fata
Dalung ya fusata bisa yadda ake ci gaba da kashe-kashe da sace-sace a sassa daban-daban na Arewa, musamman a Zamfara da Bokkos.
Ya ce:
“Yanzu haka ana kwashe mutane a Zamfara – yara, manya, maza da mata – duk suna hannun ‘yan bindiga. A Bokkos an kashe sama da mutane 25, sannan ana kona gidajen jama’a kullum.”

Source: Facebook
Dalung ya kuma zargi gwamnonin da karɓar kuɗi daga hannun Tinubu ba tare da wani aiki a bayyane ba, yana mai cewa:
“Allah ya tsine maku. Irin wannan shugabanci – Allah ya kawar da dukkanin bala’in da al’ummarmu ke fama da shi, ya koma kanku. Ubangiji Allah, tun da kuna cewa alkawarin ya cika, ka sanya wannan bala’i ya dawo kanku: a sace yaranku, a kai daji.”
“Ubangiji Allah, Ka ɗauki fansa a kansu saboda wannan ƙarya da suka yi wa talakawa.”
Dalung ya yi wa Tinubu wankin babban bargo

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ɗauki zafi kan zargin yiwa ƙusa a ADC tayin kujerun ministoci
A baya, kun ji cewa tsohon Ministan Matasa da Wasanni a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da azabtar da talakawa.
A cewarsa, Tinubu ne kadai shugaban Najeriya da ya bayyana a fili cewa ba ya son talakawa, yana kuma nuna hakan ta ayyukansa na cutar da masu karamin karfi da barin jama'a da yunwa.
Dalung ya ce kalaman Shugaba Tinubu na cewa yana kokarin ceto kasa daga durkushewa ba su da tushe, ganin yadda shi da iyalansa ke rayuwa cikin jin dadi amma jama'a na wahala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
