Ana Wata ga Wata: Malaman Asibiti 25,000 Sun Tsunduma Yajin Aiki a Fadin Najeriya
- Malaman asibiti 25,000 a karkashin NANNM sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, wanda ya fara daga safiyar Laraba
- Yajin aikin zai shafi dukkanin asibitocin gwamnatin tarayya 74, da na jihohi 36, FCT da kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan
- NANNM na bukatar aiwatar da tsarin albashi, karin kayan aiki, daukar ma’aikata, da kuma dakatar da rage kudin alawus ga malaman jinya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Harkokin lafiya za su fara fuskantar cikas a asibitocin gwamnati da ke a fadin Najeriya tun daga yau, Laraba, 30 ga Yuli, 2025.
Hakan za ta faru ne bayan malaman asibiti 25,000 da ke karkashin kungiyar NANNM, bangaren cibiyoyin lafiyar gwamnatin tarayya, suka fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai.

Source: Getty Images
Malaman jinya sun shiga yajin aiki a asibiti
Wannan yajin aikin ya fara ne da misalin karfe 12:00 na safiyar Laraba, bayan karewar wa’adin kwanaki 15 da NANNM ta bai wa gwamnatin tarayya a baya, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar NANNM, Morakinyo Rilwan, ya shaida wa manema labarai cewa za a daina duk wata hidimar jinya a asibitocin gwamnatin tarayya yayin yajin aikin.
Ya bayyana cewa wa’adin kwanaki 15 da aka ba gwamnati ya kare ne a daren Talata, 29 ga Yuli, 2025, yayin da yajin aikin ya fara da safiyar Laraba, 30 ga Yuli, 2025.
Wannan mataki ya shafi asibitoci 74 na gwamnatin tarayya ciki har da manyan asibitocin koyarwa, cibiyoyin lafiya na tarayya da asibitoci na musamman kamar na kashi, kwakwalwa da ido.
Haka kuma, dukkan asibitocin gwamnati na jihohi 36, babban birnin tarayya (Abuja), da kananan hukumomi 774 za su fuskanci tasirin yajin aikin.
Sai dai, asibitocin na masu zaman kansu ba su cikin wannan yajin aiki, kasancewar mafi yawan malaman asibiti da ke aiki a wajen ba su da yawan gaske a kasar.
Dalilan malaman jinyar na shiga yajin aiki
Trust Radio ya rahoto Rilwan ya bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon wasu jerin korafe-korafen da suka dade suna yi amma ba a saurare su ba.
Cikin bukatun da kungiyar ke nema har da wallafa tsarin aikin malaman asibiti da majalisar ilimi ta kasa (NCE) ta amince da shi tun 2016 a Minna, jihar Neja.
Sauran bukatun sun hada da cikakkiyar aiwatar da hukuncin kotun ma’aikata ta kasa da aka yanke tun 27 ga Janairu, 2012 da kuma duba yadda ake biyan kudaden alawus-alawus na malaman asibiti da ungozoma.
Kungiyar na kuma bukatar daukar karin ma’aikatan jinya da kuma samar da kayan aiki na zamani a cibiyoyin lafiya a fadin kasar.

Source: Twitter
Karin bukatun da suka gabatarwa gwamnati
Sauran bukatu masu muhimmanci da kungiyar ta ce suna cikin silar shiga yajin aikin sun hada da kafa sashen kula da harkokin malaman jinya a ma’aikatar lafiya ta tarayya.
Haka kuma, suna neman a ba malaman asibiti damar jagorantar cibiyoyin lafiya na gwamnati da kuma samun wakilci nagari a kwamitocin kula da asibitoci.
NANNM na kuma bukatar a daidaita yadda ake tura sababbin malaman jiya da ke aikin koyo da kuma amincewa malaman jinya da ungozoma su rike matsayin masu ba da shawara.
A karshe, kungiyar ta bukaci a janye sabuwar sanarwar da aka fitar kwanan nan wacce ke rage kudaden alawus da suka shafi ma’aikatan lafiya, musamman malaman jinya.

Kara karanta wannan
'Ba mu janye ba,' malaman jinya sun 'kunyata' ministan lafiya kan batun yajin aiki
"Ban ga laifin su ba" - Malama Safiyya
Wata ma'aikaciyar jinya da muka zanta da ita a jiha Kaduna, Malama Safiyya (wanda ba asalin sunanta ba ne) ta ce ba ta ga laifin malaman jinyar da suka shiga yajin aiki ba.
Malama Safiyya ta ce:
"Gaskiya yana da kyau da suka tafi yajin aiki saboda malaman jinya muhimman ma'aikatan lafiya ne, ya kamata a ce an biya bukatunsu sosai.
"An yi magana, an ba gwamnati wa'adi, duk dai ba a daidaita ba, idan aka tafi yajin aikin ina ga zai taimaka, sai gwamnati ta gane amfanin malaman jinyar.
"Ko da a ce ba a biya bukatunsu gaba daya ba, amma zai zama an duba muhimmai daga ciki an biya masu."
Malama Safiyya ta kuma ce bai kamata gwamnati ta yi watsi da bukatun malaman jinyar ba, la'akari da cewa babu wani fanni da gwamnatin ta biya ma bukatunsa.
Ta kawo misali da matsalar tsaro da kullum gwamnati ke cewa ta na mayar da hankali a kansa, inda ta ce har yanzu Arewa maso Yamma na fuskantar matsalar tsaro.
Game da likitoci ko malaman jinya da ke tsallakewa suna neman aiki a kasashen waje, Malama Safiyya ta ce:
"Ba za ka iya tsayawa ka gina kasa ba idan kasa ba za ta gina ka ba. Idan an ba ka tallafi ka yi karatu, ka gode, amma ya kamata a duba yanayin aiki shi ma.
"Ya kamata a rika duba yanayin aikin su ma'aikatan lafiyar, domin sau tari kana aikin ne amma shi aikin ne yake so ya kwantar da kai kasa, ai ka ga ba dadi."
Likitoci sun tafi yajin aiki a Ondo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, likitoci a Ondo sun fara yajin aikin gargadi domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ke wulakanta harkar lafiya.
Ƙungiyar NAGGDDPP ce ta jagoranci yajin aikin, inda likitocin suka bayyana damuwarsu kan ƙarancin ma’aikata, rashin albashi da alawus, da kuma kuɗin karin matsayi.
Amma gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta soma biyan bashin da ke kanta, tare da nuna aniyar ɗaukar ƙarin likitoci da ke da niyyar yin aiki a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

