Gwamna Ya Shirya Daukar Sababbin Ma'aikata, Matasa 12000 Za Su Samu Aiki a Adamawa

Gwamna Ya Shirya Daukar Sababbin Ma'aikata, Matasa 12000 Za Su Samu Aiki a Adamawa

  • Gwamnatin Ahmadu Umaru Fintiri za ta dauki matasa 12,000 aiki kafin Disambar 2025 domin yaki da rashin aikin yi a Adamawa
  • A wata ganawa da kungiyar kiristoci mata ta WOWICAN, gwamnan ya jaddada kudirin inganta rayuwar mata da matasa a jihar
  • Duk da kalubalen da jihar ke fuskanta, Fintiri ya ce gwamnati ta kafa tubalin ci gaba a ilimi, lafiya da sauransu ga kowane dan Adamawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa – Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin daukar matasa 12,000 aiki.

A cewar gwamnan, za a debi ma'aikata ne kafin watan Disamba 2025, kuma za su yi aiki na fansho da giratuti domin yaki da rashin aikin yi a jihar.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri zai dauki matasa 12,000 aikin gwamnati a 2025
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri zai dauki sababbin ma'aikata. Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Kungiyar kiristoci mata ta ziyarci Gwamna Fintiri

Kara karanta wannan

Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu

Fintiri ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Talata, jim kadan bayan karbar tawagar kungiyar kiristoci mata ta WOWICAN reshen Adamawa a gidan gwamnati da ke Yola.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wajen ganawar, Gwamna Fintiri ya tabbatar wa matan da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar jama'a, musamman mata da matasa.

“Ina so in tabbatar muku cewa wannan gwamnati karkashin jagoranci na za ta ci gaba da samar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar Adamawa.
“Tun lokacin da na yanke shawarar tsayawa takara a 2019, na bayyana cewa mata da matasa za su kasance a sahun gaba wajen samun tallafinmu, kuma mun cika wannan alkawari.”

- Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Fintiri zai dauki ma'aikata 12,000

A taron, Gwamna Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa:

“Muna da tsare-tsare na hakika na daukar sababbin ma’aikata 12,000 kafin karshen 2025. Wannan ya hada da malamai 5,000, ma’aikatan gwamnati 5,000, da kuma ma’aikatan lafiya 2,000.”

Ya kara da cewa wannan kari ne a kan daukar wasu ma’aikata 5,000 da ake yi a yanzu, wanda ke nufin jimillar sababbin ma'aikatan za su kai 12,000.

Kara karanta wannan

Ana zaman ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin 'yan Arewa da jami'an gwamnatin Tinubu a Kaduna

Fintiri ya kuma bayyana cewa ana shirin kafa Makarantar Fasaha da Kasuwanci a jihar don koyar da matasa dabarun kasuwanci da dogaro da kai.

“Mun samu gagarumin ci gaba tare, amma ba zan huta ba har sai kowane yaro ya samu ilimi mai inganci, kowane matashi yana da abin yi, kuma rayuwar kowanne dan Adamawa na cikin kariya,” inji Gwamna.
Gwamna Ahmadu Fintiri ya sha alwashin samar da ilimi, kiwon lafiya da ayyuka ga matasa da matan Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri. Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Fintiri ya magantu kan kawo cigaba

Wani hadimin Fintiri a bangaren yada labarai ya wallafa a shafinsa na X cewa gwamnan ya amince akwai kalubale a jihar, amma ya ce gwamnatinsa ta ci galaba a kansu ta hanyar abin da ya kira “sirrin Fintiri”, kalmar da ke nuni da saurin sauyi a jihar karkashin shugabancinsa.

Fintiri ya ce:

“Ko da ba mu da mai ko zinari, mun samu nasarar kawo ci gaba ga kowa. Wannan shi ne sihirin shugabanci na hankali.
“Mun mayar da Adamawa daya daga cikin jihohi biyar da suka fi ci gaba a Najeriya.”

Gwamnan ya kuma bukaci shugabannin kungiyar Kiristoci mata da su ci gaba da goyon bayansa da addu'o’i da hadin kai, yana mai jaddada cewa adalci, daidaito da tsaro za su ci gaba da zama ginshikan mulkinsa.

Kara karanta wannan

Noma: Hadimin Buhari ya goyi bayan Tinubu, ya fadi kuskuren da aka samu a zamaninsu

Fintiri ya gargadi ma'aikata kan shiga siyasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana inda akalar gwamnatinsa za ta karkata a shekarar 2025.

A yayin bayyana akalar ne, Ahmadu Fintiri ya gargaɗi jami'an gwamnatinsa da su kiyayi tsunduma kan su a cikin harkokin siyasa.

Gwamna Fintiri ya yi gargaɗin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen korar jami'in gwamnatin da ya samu yana siyasa a 2025, don ya san yana raba hankalinsa ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com