Bello Yabo: 'Tun da Buhari Ya Mutu, Tinubu Ya Ƙwato Kuɗin da Aka Sace a Mulkinsa'
- Sheikh Bello Yabo ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya karbo dukiyar al’umma da aka wawure a lokacin mulkin Muhammdu Buhari
- Ya ce tunda Buhari ya mutu, bai kamata shugaban kasa ya ci gaba da jin kunyar karɓar dukiyar jama'a daga barayin gwamnati ba
- Bello Yabo ya kuma gargadi Tinubu da ya shirya zuwan tashi shi ma, domin wanda zai gaje shi zai karbi dukiyar jama'a da ya sata ya boye
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Bello Yabo, ya ja hankalin Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da karbo kudaden jama'a daga barayin gwamnati.
Sheikh Bello Yabo ya bukaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar ya kwato kudin da aka sace a lokacin mulki marigayi Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
Malamin ya aika wannan sako ga shugaban kasar ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Shugaban gwamnoni 19 ya fadi ya fadi abin da 'yan Arewa za su yi kan tazarcen Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakon Bello Yabo ga Shugaba Bola Tinubu
A cikin bidiyon, Bello ya ce lokaci ya yi da Tinubu zai karbo kudaden da aka sace, tun da Buhari ya mutu, yana mai cewa yanzu sai shugaban ya daina jin kunyar kowa.
Sheikh Yabo ya ce ko da a ce kowa bai yarda cewa Buhari ya mutu ba, to shi Tinubu zai gaskata hakan, don gabansa ne aka sanya tsohon shugaban kasar a kabari.
"Sannan Tinubu, in kunyar Buhari ce ta sa ka kyale su, to Buhari ya mutu. In kowa bai tabbatar da mutuwar Buhari ba, kai ka tabbatar da mutuwarsa.
"To kuma dukiyar nan tamu da suka sata ita ce dai suka fito da ita yanzu za su yake ka, ka yi wa kanka kiyamul laili, ka tabbatar ka taushe su ka amso mana dukiyarmu."
- Sheikh Bello Yabo.
Bello Yabo ya magantu kan yafewa Buhari
Fitaccen malamin addinin, dan asalin jihar Sokoto, ya kuma gargadi Shugaba Tinubu a kan satar kudin jama'a.

Kara karanta wannan
'Abubuwa 2 za su hana Tinubu lashe zabe a 2027,' Modu Sheriff ya ba da satar amsa
A jawabin malamin, babu inda ya kawo hujjar cewa an yi sata a gwamnatin da ta gabata ko kuwa ana yin hakan a mulkin Bola Tinubu.
Malamin ya ce:
"Kai ma wacce ka sata wanda zai gaje ka ya taushe ka ya amso mana abin mu."
Kalaman malamin dai sun karkata ne game da ce-ce-ku-ce da aka rika yi game da yafewa marigayi Muhammadu Buhari.
Sheikh Bello Yabo ya ce ta yaya wasu malamai za su yi amfani da hadisi cewa ko ba ka yafe ba Allah zai tafe masa.
Mun ruwaito cewa malamin ya ce abin takaici ne kana ganin wadanda suka kwashe muku dukiya suna facaka amma ace a yafe musu.

Source: UGC
Martanin jama'a ga kalaman Bello Yabo
'Yan Najeriya sun yi martani game da bidiyon Sheikh Bello Yabo:
Hamdala-store Abban Ridwan
"Malam Bello Yabo ko kana so ko ba ka so mun yafewa Buhari. Kuma In-sha Allahu muna mai fatan shiga Aljanna."
Nafiu Bala Muhammad
"Ba mu yafe ba wallahi. A dawo da dukiyar talaka shi ne kawai."
Muhyissunnah Assalafiy
"Ina ganin da Dr Idris Rahmatullahi na raye shigen irin huɗubar nan zai yi"
Dahiru Abubakar:
"Allah ya sakawa malam da mafificin alkairi, gaskiya daya ce wallahi. Malam tun kafin ka hau munbari a wannan matsaya muke, ba mu yafe ba, kuma ba zamu ta6a yafewa ba."
Mustapha Muhammad:
"Allah yakara sutura. Wasu Malaman suna boye gaskiya don son zuciyarsu kawai, Allah ya karo mana irinku malam."
Haruna Malam Salihijo Marke:
"Satar biro ita ta jawo satar bindinga. Mu dama tun farko ba mu yafe ba kuma ba za mu taba yafewa ba."
Kali bidiyon a nan kasa:
Bello Yabo ya je wajen wa'azi dauke da bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Bello Yabo ya janyo cece-kuce sosai bayan bullar wani bidiyo da aka ga malamin yana wa’azi rike da bindiga.
Sheikh Bello Yabo ya ce idan yana rike da bindiga, ba wani bata gari da zai firgita shi; a cewarsa a shirye yake ya kare kansa a kowane lokaci.
Yayin da wasu ke goyon bayan matakin malamin na kare kai tare da bayyana bindigarsa a fili, wasu na ganin hakan na iya tayar da zaune tsaye a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
