Abin Mamaki: Farida Sultana da Wasu Mata 'Yan Arewa 2 Sun Shiga Shirin BBNaija
Abuja – Gasar Big Brother Naija (BBNaija) ta shiga zangonta na 10 a 2025 cikin sabon salo mai zafi, inda aka fara da mata 15 kacal a daren ƙaddamarwa na Asabar.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Daga cikin mata 15 da za su fafata a wannan gasar ta bana, akwai guda uku da suka fito daga jihohin Arewa; Kaduna, Benue sda kuma Adama - abin da ba a saba gani ba.

Source: Twitter
An fara shirin BBNaija zango na 10
Channels TV ta rahoto cewa matan 15 da suka fito daga kabilu da jihohi daban-daban sun shiga gidan 'Biggie' domin kafa tarihi tare da kawo sabon salo da nishadi cikin shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An buɗe zangon bana da raye-rayen mawaki Fido (da waƙar “Joy Is Coming”), alamar cewar wannan kakar za ta kasance cike da dariya, rudani da kuma sabon nishadi.
Ebuka Obi-Uchendu, wanda aka fi sani da 'gwanin ado', ya shiga gidan da kaya biyu masu jan hankali: Daya irin na Osuofia da wasu manyan kaya da ke tuna wa da Sarki Sunny Ade.
BBNaija S-10: Mata 15 sun shiga gidan Biggie
A yayin da aka shirya shigar maza ranar Lahadi, 27 ga Yuli, hankula sun karkata kan matan da za su fafata a shirin, wadanda suka shiga gidan Biggie a ranar Asabar.
Daga Zita zuwa Isabella, daga Joanna zuwa Big Soso, kowacce ta shiga gidan da kuzari, kyau da salo, alamar tana shirye don yin abin da zai sa ta lashe gasar.
Wannan zangon na musamman ne, domin shi ne zangon bikin cika shekara 10 da kafuwar gasar BBNaija, wanda aka sanya masa kyautar N150m ga zakaran shirin.
Sabon gida, sababbin dokoki, da sabuwar rayuwa; abin da ke jiran wadannan zafafan mata. Lokaci kuma ya yi da masu kallo za su ba idanuwansu abinci.
Mata 3 'yan Arewa da suka shiga shirin BBNaija
A gasar BBNaija ta bana, akwai mata uku da suka shiga, wadanda sun fito ne daga jihohin Arewacin kasar; Kaduna, Benue da kuma Adamawa - abin da ba a saba gani ba.
Legit Hausa ta yi bayani game da 'yan wasan:

Source: Twitter
1. Big Soso (Sonia Amako), 28 – Kaduna
Sonia Amako, wadda za a rika kiranta da Big Soso a shirin, ta kasance kwararriyar mai dafa abinci kuma lauya da ta yi karatu a Burtaniya.
Gidan talabijin na DSTV ya rahoto Big Soso ta bayyana cewa ta shiga shirin BBNaija ne domin:
"Ina son na zama gadar da ta hade Arewa da sauran sassan Najeriya ta hanyar nuna karfin hali, jajurcewa da kyawun da akasan yankinmu yana da shi.
"Ina so 'yan mata da ke tasowa su dauki darasi a kaina, cewa za su iya yin aiki tukuru domin cika mafarkansu, su gina kasuwanci, su taimakawa al'umma, kuma su kare al'adunsu."

Source: Twitter
2. Joanna (Josephine Iwoh), 21 – Benue
Josephine Iwoh, wacce za a rika kira da Joanna a gasar, ta kasance sarauniya a gasar kyawawa da ta koma harkar kasuwanci. Joanna ba ta jin tsoron bayyana ra’ayina.
Joanna ta bayyana cewa ta shiga shirin BBNaija zango na 10 domin:
"Na saba taka rawa a shirye-shiryen jama'a, amma shiga ta wannan shirin zai ba ni damar nunawa duniya irin baiwar da Allah ya ba ni.
"A cikin wannan gidan, mutane za su san wacece Josephine, za su gane rawar kan Josephine, za su fahimci karfin zuciya da jarumtar Josephine, kuma za su san kyawawan dabi'u na da ma akasin hakan.
"Na shiga shirin don na gwada kaina, na koya daga mutanen da suka fito daga wurare daban daban, in kuma koyi juriya daga gwaje-gwajen da zan gamu da su a gidan."

Source: Twitter
3. Sultana (Farida Sultana Ibrahim), 25 – Adamawa
Farida Sultana Auduson Ibrahim, wacce za a rika kira da Sultana a shirin, ta kasance kyakkyawa, mai cike da kuzari, baiwa da kuma hangen nesa.
BBNaija Daily ya rahoto Farida Sultana Auduson Ibrahim ta bayyana cewa ta shiga shirin BBNaija na bana ne domin:
"Ni mai son shiga bakon abu ne, kullum ina so na gwada karfin kwakwalwa da tunani na, in kuma gwada mizanin sauyin da ruhi da jikina za su iya dauka.
A shirye nake na tunkari sabon kalubale, kuma ina da yakin cewa kalubalen zai koya mani darasin da zan gina rayuwata da shi.
"Ina kuma son na hadu da mutanen da suka fito daga bigiren rayuwa daban-daban, mu san labarin juna, mu koyi dabi'un juna, mu kuma nunawa duniya karfi da izzar Arewacin Najeriya."
Sauran mata a wasan BBNaija
Bayan bayani game da 'yan mata uku da suka fito daga Arewa, akwai kuma jerin sauran matan da suka shiga shirin BBNaija zango na 10:
4. Zita (Elizabeth Oloruntola), 24 – Lagos
5. Gigi Jasmine (Nicole Simon–Ogan), 31 – Akwa Ibom
6. Ivatar (Ifeyinwa Okafor), 37 – Anambra
7. Sabrina Idukpaye, 32 – Edo
8. Mide (Ayomide Iwasokun), 23 – Ondo
9. Dede (Precious Ashiogwu), 23 – Delta
10. Doris Okorie, 33 – Imo
11. Isabella (Esther Georgewill), 29 – Rivers
12. Imisi (Opeyemi Ayanwale), 23 – Oyo
13. Ibifubara Davies, 28 – Lagos
14. Tracy (Uchenna Ekwe), 27 – Anambra
15. Thelma Lawson, 26 – Rivers
'Shirin BBNaija wakilin shaidan ne' - MURIC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar hare hakkin musulmai ta MURIC ta bayyana goyon bayanta ga kawo karshen shirin BBNaija.
A lokuta da dama kungiyar ta sha bayyana rashin amincewarta da shirin mai nuna abubuwan da basu dace da tarbiyya ba, har ma ta kira BBNaija da 'wakilin shaidan.'
MURIC ta koka da yadda wani gwamna ya kwashi kudaden jama'a da gida ya ba wanda ya lashe wasan BBNaija, ba tare da la'akari da tasirin hakan ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




